RASHIN HAIHUWA

GARKUWAR MA'AURATA DA MAGUNGUNA

RASHIN HAIHUWA GA NAMIJI

_wato abinda Zan Dan tunasar da Kai ko ke itace mu yarda Allah shine Mai bayarwa ba shan magani ba sai dai magani yana Iya taimakawa domin samun sauki.

Akwai Hanya ta rashin haihuwa kamar uku ko zuwa sama.

↻ sihiri

A lokacin da kake Neman aure ka samu Nasara a kan abokin takara sai yayi maka sihiri kan haka.

● gado

● hatsari ko maniyyi ka baya da karfin sinadarin haihuwa.

● shan kwayoyin

● aure aljana

ALAMAR SIHIRI A JIKIN NAMIJI

namiji Ana gane sihiri a jikinsa, yadda ake ganewa shine, zakaji ka da lafiyarka da kuma sha'awa, Amma duk lokacin da ka kusancin matar ka tun daga Karon farko zakaji gabobinka ba karfi, sha'awar ka kuma ta janye, maimakon gabanka ya mike sai kaga yana komawa baya da kuzari.

Abu na Biyu wani irin wannan baya samun Sa, wato shi zai gama wasa da iyalinsa, sai a Karon farko in yazo zai sadu da matarsa sai gabansa ya noke ya kwanta kamar Wanda aka zuba masa ruwa sanyi.

Abu na uku wani sha'awar tasa gaba daya take janyewa wato yaji shi kwata-kwata baya da sha'awar mace, idan yana cikin gidansa, amma kuma idan yana waje sai yaji shi gagau kamar ya fashe, in kuma ya dawo gida yaji shi kamar mace ba kuzari babu sha'awar.

Abu na Hudu kuma Inda zai sadu da matar baya iyawa Amma kuma yana mafarki yana saduwa da mace ko kuma a fili zai ji yana zubar da Mani kamar ya sadu da wata.

Namiji Mai matsala rashin haihuwa to yayi kokarin jarraba wanna maganin insha Allah.

↠ habbatussauda
↠ hubbu rishad
↠ Zuma
Idan ya samu habbatussauda da hubbu rishad to sai ya daka su waje daya ya rinka dibar Rabin karamin cokali yana zubawa a Zuma yana Sha sau Biyu a yini.

Hanya ta Biyu.
Ko kuma yawaita cin karas 🥕 a rayuwa da Zuma.

RASHIN HAIHUWA GA MACE

ALAMA TA NAMIJI DARE KO SIHIRI

DUK soyayyar da mace take yiwa mijinta, to da zaka same ta mijinta zai kusance ta sai ta mammanne cinyoyinta ta yadda mijin ba zai Iya saduwa da itaba.

Wata matar kuma duk soyayyar da take wa mijinta zata nemi ya bude, cinyoyin Nata da karfi don saduwa Amma sai mijin ya kasa.

Akwai macen da idan mijinta yazo saduwa da ita, sai aljani ya shiga majiyarta, wato ma'ana baxa taji wani dadi a tare da shi ba, kuma ba zata Iya amsa masa ba, sannan kuma zata zama kamar Mai matacce jiki, sai yadda mijinta ya jiya ta, sannan kuma ba zai samu nasarar Kai wa ga majiyarta ba.

Wata macen kuma duk lokacin da mijinta yazo saduwa da ita, kwatsam sai taba jini yazo Mata, daga nan miji sai ya kasa kusantar ta, da ya bar shimfidar sai jinin ya daina zuba, haka yake kasancewa ko yaushe, wata matar duk lokacin da mijinta yazo kusantar ta, sai wata tsoka ta bijiro a farjinta, ta tokare mashigar wacce ba zai Iya kusantar ta ba.

Wata matar kuma mijinta zai aure ta tana budurwa, to sai yazo kwanciya da ita sai yaji ta kamar tsohuwa gaba dayanta har sai ya rinka kokwanto a kan haka, Amma a wajen magani wannan tantanin yana dawowa kamar yadda take budurwa.

mace Mai matsala rashin haihuwa to tayi kokarin jarraba wanna maganin insha Allah.

Kamar yadda muka fadi alamar namiji shine na mace.

Duk lokacin da al'adarta ya tsaya, to ta samu kaninfari ta daka shi Tasa kadan a cikin madara ta Sha da yamma.

HANYA TA BIYU

a samu DAL'U'NAKHIL a kwaba shi da Zuma Mai kyau sai a ajiye shi duk lokacin da ya rage Rabin awa a sadu da maigidanki to sai a sashi a farji,

Amma Inda kina fama da namiji dare yana hana haihuwa ko wasu lalura a nemi magani.

      CIWO BAYAN HAIHUWA

sau tari Ana samun mata da zarar sun haihu sai wani ciwo Mai tsanani ya biyo baya.
Wato mararta ta daure kamar zata mutu, to da zarar ta haihu sai a samu habbatussauda a kwaba ta da Zuma a bata ta Sha, insha Allah.

Ko kuma ta samu hulba da Zuma Mai kyau ta tafasa da ruwa ta rinka Sha.

DOMIN SAMUN SAUKIN HAIHUWA

duk macen da take yin nakuda to tayi kokarin samun hulba ta tafasa ta a ruwa ta Sha.

● YIN KIBA GA MASU RAMA ●

Wacce take da jiki ramamme to domin ta farfado, to ga magani kamar haka.

● hulba Babban cokali 4
● himmas  cokali 4
● shammar karami cokali 2
● sim-sim ( man ridi ) karami cokali
● Zuma
● nono ko madara

Da farko idan aka samu hulba, himmas shammar sai a daka su, su yi laushi, sai a samu Zuma Mai kyau a zuba garin maganin karamin cokali daya a ciki tare da zuba karamin cokali na man ridi daya a ciki, sai a juya a rinka Sha safe da yamma. Bayan an Sha sai a samu nono ko madara Mai kyau a Sha.

Hanyar ta Biyu

● hubbu rishad
● nono ko madara
● Zuma
Da farko idan kika nika hubbu rishad sai Ki rinka zuba karamin cokali a cikin madara tare da Zuma kina Sha da safe tun kafin kici wani Abu.

Hanya ta uku

Ko Ki samu himmas tare da inibi busasshe Ki rinka ci tare da shan madara da zuma, musamman da safe.

          HANYAR RAGE KIBA

Wanda tumbi ko teba tayi yawa, to sai ya yawaita cin ganyen na'a-na'a tun kafin yaci abinci,sannan sai ya Sha Kofi daya na ruwan sanyi tare da zuba karamin cokali na khal tufah.

Hanya ta Biyu

A samu Lemu tsamu a tafasa shi a ruwa asa sukari a rinka Sha da safe.

                   DATTI CIKI

idan Ana fama da datti ciki Wanda yake Sa zuciyar mutum ta rikita shi kamar zai yi amai.

To sai a samu hulba a tafasa ta da Zuma a rinka shan ruwan.

Post a Comment

0 Comments