MU GYARAN KANMU DA KANMU CIKIN SAUKI
☏+2348037538596
✎ sirrinrikemiji:
↻ gyaran jiki.
↻ kamshin jiki.
↻ laushi data.
● Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da dwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin sannan a wanke.
● domin gyaran farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi kyau sosai.
● Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai sulbi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya a sati za a ga canji.
● Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke madale a gefen gashin kai.
● Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rida shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka badin da ya bayyana a wasu gafen fata.
● Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rida dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
● Man kwa-kwa na matudar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
● Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
● A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai.Sannan a rida shafawa a kan durajen fuska. Yin hakan na kasha su sosai.
● Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
*MACEN DA TAKE SO FATARTA GA GOGE TAI KYAU TA QYALLI.*
☏+2348037538596
✎ sirrinrikemiji@yahoo.com
✎ sirrinrikemiji@gmail.com
✐ sirinrikemiji.com
sai ta nemi waxannan abubuwa kamar haka:
● Sabulun Gana.
● Sabulun sabo
● Majigi
● Jangana.
● Kurkur
● Lemon tsami.
● Qwai 2.
● Sabulun Detol
● Sabulun Dawa'us Sabunu.
Sai ta haxasu a guri guda ta dake su, sannan ta sami kurkur ta zuba a ciki sannan ta sami lemon tsami da qwan ta kaxa ta haxa a ciki zata ga yanda fatarta za tayi kyau sosai.
*2-MACEN DA TAKE SO FUSKARTA TA GOGE TAIQYALLI*
Sai ta nemi wannan abubuwan:
Ta nemi Kurkur.
Ta nemi dilka.
Ta nemi zuma.
Ta nemi lalle.
Ta nemi qwai.
Ta nemi lemon tsami.
Sai ta haxa su guri guda ta sami ruwa kamar zaki kwalalle amma ya fi lalle ruwa in zaki kwanta barci sai ki goga a fuskar ki, idan kuma duka jikin ki kike so sai ki shafa idan kika tashi daga barci sai ki yi wanka za ki ga yanda jikinki zai goge yai kyau da sheqi.
*3-QAMSHIN JIKI:*
Macen da take so ta riqa yin qamshi mai xaukar hankali sai ta nemi:
Kafi amarya qamshi.
Garin ambar.
Garin miski.
Garin kaninfari.
Kafun-kafun.
Sai ta cakuxasu a cikin baslilin (Vaseline) ta ringa shafawa. Duk inda kika je to gurin zai dinga qamshi ba za'a so ki tashi ba.
*KYAN FUSKA (1):*
Wadda take so fuskarta tayikyau sosai to sai ta nemi waxannan abubuwa:-
Farar albasa.
Garin zogale.
Sabulun salo.
Sabulun Gana.
Dettol.
Sai kuma ta kirvasu a guri xaya ta mulmulesu, sannan ta dinga yin wanka dasu. Za ki ga yadda jikinki zai yi kyau. Kuma zaki yi fari ba mai cutarwa ba.
*KYAN FUSKA (2):*
Macen da take so fuskarta tayi haske, haske mai xaukar hankali duk wanda ya ganta zai ga kamar a kwali aka varota. Sai ki nemi waxannan:-
Jar hoda.
Tumatir.
Lalle.
Ganyen darbejiya.
Gishiri.
Sai ki haxesu guri xaya ki cakuxasu da Bayo kiliya sai ki dinga shafawa in zaki kwanta barci, kuma idan kin tashi sai kisa ruwa mai xumi ki wanke fuskarki zaki yi mamaki.
*5-QAMSHIN JIKI:*
Macen da take so kar aji jikinta yana wari sai dai a ji yana qamshi to sai ta nemi:-
Kanwa Ungurnu.
Alumun.
Lemon tsami.
Turaren Bahur.
Sai ta cakuxasu guri xaya ta riqa gogawa a jikinta.
Zuwa hammatarta. Saboda shi wari ta guri uku yake fitowa a jikin mace. Guraren sune:
Hammata.
Baki.
Farji..
Idan mace zata kula da waxannan gurare to zata kuvuta daga dukkan wari.
Bayan kin gagasu a jiki sai kuma ki je kiyi wanka to jikin ki koda yaushe qamshi za'a ringa ji ba dai aji wari ba.
*LAUSHI DA SANTSIN FATA:*
Macen da take so fatarta tai laushi da taushi da santsi, sai ta nemi:
'Ya'yan auduga.
Man zogale.
Man shanu.
Kurkur.
Sai ta soyasu a guri xaya. In ya huce sai tad aka garin farar wuta sai ta zuba a ciki sannan duk lokacin da zata kwanta sai ta shafa a jiki. Jikin zai yi kyau fata zata yi taushi da laushi da santsi inSha Allahu.
*GYARAN FATA:*
Macen da ke son fatarta tai laushi tuvus-tuvus sai ta nemi:
Sabulun salo.
Man auduga.
Dudu Osun.
Dawa'u Sabun.
Dettol.
Rihatul Hubbi.
Lemon tsami.
Saiki haxesu ki cakuxesu a guri guda ki ringa wanka, fatarki za tai laushi da taushi da santsi.
*QAMSHIN BAKI:*
Wadda take so bakinta ya ringa qamshi ko da yaushe to lalle ne ta riqa kulawa da waxannan abubuwa:
Kula da bakinki bayan kinci abinci da kuma kafin ki ci.
Barin surutu yayin cin abinci.
Saboda duk lokacin da kike surutu a yayin cin abinci to ragowar abincin zai riqa komawa qarqashin ganxarki kuma ba zai tashi fitowa ba sai lokacin da kika haxa harshe da mijinki (Kiss) sannan sai ya riqa fitowa da wari.
Wannan kuwa babbar illa ce. Manzo (SAW) ya ce: "Ku tsaftace bakinku domin rashin tsaftace baki shi yasa matan banu Isra'ila suka dinga yin zina" shawara ga maza da mata a tsaftace baki wajen jima'i yana haddasa qiyayya sosai.
*SHEQIN FUSKA:*
Macen dake fama da qurajen fuska sai ta sami:-
Dawa'u Sabuni.
Lemon tsami.
Haidirojin (Hydrogen).
Farar wuta.
Man darbejiya.
Man zogale.
Sai ki haxe su guri xaya ki riqa dangwale da tsumma kina shafawa kina goge fuska dashi.
Fuskarki za tai kyau sosai. Kuma qyasbi, quraje, tabo duk zasu fita InSha'Allahu zatai sheqi.
*SHEQIN FUSKA DA WALWALI:*
Wadda take so fuskarta tai kyau ta riqa sheqi da walwali kuma tai tas, fatarta ta goge sai ta nemi.
Giye.
Lemon tsami.
Vawon qwai.
Kurkur.
Sai ta kirvesu ta dunqule guri xaya ta riqa wanka dasu, fatarta zatai fest a goge tai kyan gaske.
*LAUSHIN GASHI:*
Wadda take so tayi laushin gashi a koda yaushe sai ta sami waxannan:
Man kwakwa.
Man zogale.
Xan bayala-yala.
Ki haxesu wuri xaya ki riqa shafawa, sannan ki wanke da rowan magarya. Za kiyi mamamki.
*FARI DA QAMSHIN FATA*
Sai ki nemi:-
Coconut.
Bayo.
Alabin.
Bakur.
Ambar.
Ki cakuxesu guri xaya ki qara musu rowan rijiyar kasuwa ki tafasa su in ya huce ki zuba a mazubi mai kyau, in zaki kwanta ki sahfe jiki dashi, fatarki za tai kyau da qamshi da haske. Kuma duk wanda yaji wannan qamshi yaro ko babba zai ji yana qaunar ki matuqa wannan shine ake cewa (xanxani ruxi).
*FARIN IDO:*
Macen da take so idonta yayi fari kamar madara inta kalli miji sai ya ruxe, sai ta nemi:
Kifi sadin guda 3
Citta qwaya 7
Kanin fari guda 21.
Masoro guda 21.
Kimba guda 21.
Sai ki haxesu guri xaya sai ki dafa su bayan kin dafa sai ki soya su ki shanye su bushe sai ki dake su ki riqa zubawa a abinci kinanci. Za kiyi mamamkin yadda idonki zai yi fari tar Insha Allahu Ta'alah.
*YAWA DA TSAWON GASHI:*
Macen da take buqatar gashitna ya qara yawa da kuma tsayo, to sai ta nemi waxannan:-
Ganyen magarya.
Turare mai qamshi.
Kanimfari.
Man zogale.
Sai ki haxesu guri xaya ki riqa shafawa. Za kiyi mamakin yadda gashinki zai yi tsawo da kuma qara yawa Insha Allah.
Dulka.
Sukari.
Lemon tsami.
Man zogale.
Du'a'ull janna.
Ruwa.
Sai a zubasu a cikin ruwa gaba xaya ki xora akan wuta ki riqa basu wuta kaxan-kaxan har sai ya tafasa yayi kumfa sai ki bari ya huce. Ki dinga dangwala kina shafawa a ko ina ajikinki yayin da kika ga kika gama shafe ko ina ajikinki dashi sai ki barshi yayi kamar rabin awa ko awa xaya, har sai ya fara marmasowa da kansa, sai ki murmushe shi sannan kije kiyi wanka Wai! Wai!! Wai!!! Fatarki zata koma kamar tarwaxa wajen santsi. Idan kika juri yin haka zaki koma kamar baturiya ko Balarabiya wajen santsin fata.
Macen da take so mijinta ya dinga jin qamshinta yana tashi lokacin jima'i sai ta nemi:
Miski.
Ambar.
Zam-zam.
Ma'ul – ma'i.
Rihatul-hubbi.
Ganyen magarya.
Sai ki haxasu guri xaya a kwano sannan ki xan tasasu in ya huce sai ki nemi buta mai kyau ki zuba ki qara ruwa duk lokacin da zaki kwanta sai ki je ki yi tsarki das hi kuma ki shafe tsakanin cinyoyinki dashi har zuwa gefen farjinki da cikinsa. Tabbas mijinki zai qara kwaxaituwa izuwa gareki kuma zai so ace koda yaushe kuna tare.
*QAMSHI MAI KWANTAR DA HANKALIN MASOYI:*
Macen da take so ta dinga qamshi mai kwantar da hankali duk wanda ya ji shi ko da faxa yazo sai yaji hankalinsa ya kwanta sai ta haxa waxannan turarukan guri guda:
Jan ambar.
Rihatul hubbi.
S.S.
Internet.
Sai ki cakuxasu guri xaya a sayo miki zuciyar damo sai ki shanyata ta bushe sai ki daketa ki zuba a cikin waxannan turarurrukan, sai ki dinga shafawa bayan kin qara musu turare irin wanda ranki yake so, to duk faxan mutum idan yazo gunki sai yaji zuciyarsa tai sanyi.
*QAMSHI MAI JAN HANKALI:*
Macen da mijinta baya saurararta ko hira da ita sai ta nemi:
Farin miski na ruwa.
Dum (turare).
Turaren Khalid.
Turaren kaliyo.
Turaren qud.
Mujlabul-khairi.
Sai ta juyesu guri guda, sai ta tofa masa tahiya bakin salihina qafa 130, zata ga yadda mijinta zai dawo gareta.
*INDA AKE HAXA FARAR HUMRA MAI KAMA FATA:*
Sai ki nemi:-
Farin sandal.
Hawiy.
Rihatul hubbi.
Garin humra fari.
Dusha.
Turaren 24 hours.
Sai ki haxa su waje guda sai ki qara turare mai sanyin ruwa kalar da kike so wannan humrar in kika sata ba za a so ki tashi ba.
*BAQAR HUMRA:*
Sai a nemi:
Mujlabul khairi a daka shi.
Sifirit.
Babby doll.
Hawiy.
Silva café
Garin Baqar Humra.
Sai ki haxasu waje guda da dakakken garin mujlabul khairi xinki sai ki nemi turare mai sanyin ruwa sai ki zuba gwargwadon yadda kike buqata to in kika shafa wannan za kiyi mamakin yadda zaki samu farin jinni da kwarjini.
*TURARE NA TSUGUNO*
Macen da take so ko ina nata ya ringa qamshi da mijinta ya kusanceta sai yaji tana qamshi sai ta nemi Sandal na itace sai ta nemi turaren 'yan matan Arewa sai ta nemi lemozin da Dusha sai ta sassara wannan itacen na Sandal sai ki zuba a ciki sai ya kwana uku (3), sai ki xaukoshi turaren ki riqa shafeshi a qirjinki zuwa mara. Shi kuma itacen ki riqa hayaqi da shi. Za kiga inda ko ina aka kusance ki zaki burge mijinki.
*SHAWARA GA MA'AURATA (1):*
Kada ki bari cikinki yayi girma teva
0 Comments