*★GYARAN MATANCI SANADIYYAR RASHIN KULAWA★*
☞ islamic medical center
☏+2348037538596
☞ www.sirinrikemiji.blogspot.com
da yawa mata sai su zauna ba wanka ,haka babu wanki , to anan idan muka Duba mu fa mata muna da matsalolin daban-daban wadanda a zahiri sune ma idan kin kasance daya daga ciki zasu iya haifar miki da matsala ta warin matanci.
MISALI☞ : zaki shiga gida ki tarar da mace wai matar aure tun safe tana zauna a gaban wuta tana ta soye-soye ko kuma girke-girke na abincin siyarwa alhalin tana cikin hali na jinin haila ko kuma ta Tara da maigida amma tunda ta taso daga bacci tana nan a zaune a bakin murhu ba wanka, ga wata idan haila take tun kunzugun jiya ga warin gumi ga kaurin hayakin duk ta hadu ta cakude, sannan sai yamma ko dare zata rabu da bakin murhu , sai kuma ta dan dibi ruwa aje Ayi wanka, ba za a tsaya a wanke jiki yadda ya kamata ba, sai kuma a nufi turaka a haka.
Shi ne Zaki ga maigida kullum cikin fada cikin kyamar matarshi har ma idan ba mai zurin hakuri bane ya Saki matar ,kuma ka rasa dalili sakin.
*❊・HANYAR DA ZAKI GYARA・❊*
☆ ruwan dumi
☆ sabulun salwa.
☆ Alimun /turare
Kullum idan kika tashi ki tafasa alimun kafin ki shiga wanka sai ki dinga shiga ciki ki wanke ko ina ki saka sabulun salwa kadan ki wanko ciki sossai sai kuma ki shiga wani ruwan cumin ki sake daurayewa sossai, sai kuma ki fesa dan turare ko miski akan tissue ko pad ki saka kamshi zai koma jikinki yadda ko maigida ya kusance ki ba zai ji warin ba.
Ke da kanki ma za ki gane a yanzu kin canja.
✎ +2348037538596
*°◇°GYARAN FARJI A YAYIN HAIHUWA °◇°*
( shiga turaka Kai tsaye )
Yan uwa mata Ku fahimci wani abu, mu mata kullum muna haihuwa, jikinmu na Kara karuwa, don haka yana da kyau ga kowacce 'ya mace a duk haihuwa da kika yi to ya zama lai-lai ki gyara jikinki kada kice ai ke kin tsufa Bari ki barwa yara, a a ai idan har kina da aure to ya zama lallai ki kula da gyaran jikinki.
*❀RANAR FARKO❀*
Zaki tafasa alimun, bayan kin wanke duk wani jini dake dankarewa mace na haihuwa, to kuma sai ki wanke jikinki da ruwan alimun ki kuma shiga ciki ki zauna tsawon minti goma sannan ki fito, anan a gefe ki samu naman da kika dan dafa ki cinye da dumi sai ki Dora kunun:
✎ Kunun aya
✎ Kunun kanwarki
✎ Kunun gyada
*⁝⁞⁝⁞⁝⁝⁝ GYARAN FARJI A LOKACIN AL'ADA ⁞⁝⁞⁝⁞⁝*
lokacin al'ada lokacin ne da mace zata tsaya ta kula ta ga cewa bata sakin jikinta kamar lokuta da bata al'ada ba, musamman ma budurwa wacce bata taba aure ba, har itama matar auren wacce ta San ciwon kanta, kuma bata son taga miji yayi watsi da ita da wuri ko yana tunanin Karin aure da wurin, to sai ki tsaya ki maida hankali wajen kulawa da jikinki a lokacin al'ada da kuma haihuwa, saboda itace mace a duk lokacin da take cikin al'ada to a wannan lokacin jikinta budewa yake yi, shi yasa idan mace na cikin al'ada idan akwai manya a kusa, sai su rinka hanata daukan abu mai nauyi
Bokiti da kuma tsalle-tsalle ko kazar-kazar saboda wannan lokacin jikinta a bude yake.
Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi.
Don haka idan budurwa tayi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi'a shine sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawan banza tunda bai samata a matsayin wacce bata taba aure ba.
Nan kuwa ba haka bane, yawan tsalle-tsalle ne ya jawo a ya yin al'ada.
Idan kuma matar aure ce to sai kaga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al'ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rikka waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse a a sai ma ya Kara budewa da yayi.
*DON HAKA IDAN HAR KINA CIKIN AL'ADA YA KAMATA*
Ki kula da irin zaman da Zaki yi da tafiya ki kuma kiyaye da daukan abu mai nauyi.
*▼ YADDA ZAKI GYARA ▼*
ya zama dole ki kula da wanke mafi karanci a Rana sau biyu wato safe da yamma.
Sannan wanka da sabulun mai kamshi da kuma ruwan dumi, sai kuma ki shafa mai mai kamshi ki saka turare mai kamshi sannan a koda yaushe ki rinka yawan canja din da ke jikinki saboda shi jini ya danganta, wani yana karni wani babu wani ma wari yake.
✿ ・+2348037538596
☏+2348037538596
☞ www.sirinrikemiji.blogspot.com
0 Comments