🛑 ZUWA GA MASU FAMA DA SHA'AWA 🌍
💬 Samari da ‘Yan Mata, Zawarawa, har ma da Matan Aure 👌
#sirrinrikemiji
🕌 Ya Allah kabawa wanda ya samu halin karanta wannan rubutu ikon yin sharing zuwa ga sauran groups.
Samari da ‘yan mata suna yawan turawa malamai tambayoyi iri daban-daban akan yadda suke fama da tsananin sha’awa.
Wasu daga ciki sukan ce suna istimna’i wato wasa da al’aura wai don su gujewa aikata zina, bayan zinar suke aikatawa.
Istimna’i (wasa da al’aura) ya haramtu ta kowace irin siga kuma yinsa zai jawo azaba da ukubar ranar alkiyama matuƙar dai mai aikatawa bai tuba ba ya daina.
Fitar da maniyyi ta kowace irin siga haramun ne, sai dai ta hanyar aure kawai.
Akwai bala’o’i masu tarin yawa dangane da masu wasa da al’aura.
Idan ka kasance ko kin kasance kina fama da matsananciyar sha’awa kuma babu halin yin aure, to akwai hanyoyi masu tarin yawa da zaku bi don gujewa fadawa tarkon Shaidan.
Ga wasu daga cikin jerinsu:
Ku guji zama a ɗaki ku kaɗai, ba tare da mutum yana wani aikin da zai ja hankalinsa ba.
Ku guji yawan sanya sha’awar jima’i a cikin ranku.
Ku yi iya ƙoƙarin da zaku yi wajen kawar da kai daga shafukan da suke yada hotuna masu nuna tsiraici.
Yawan yin azumin nafila yana matuƙar taimakawa wajen nesanta mutum daga wannan dabi’a.
Kada ku yi wa kowace irin mace kallon sha’awa, haka kema ki daina yi wa kowane irin namiji kallon sha’awa.
Mutum zai iya rayuwa cikin ƙoshin lafiya ba tare da yana fitar da maniyyi ba har zuwa sanda zai yi aure, muddin dai mutum yana tunawa da azabobin da Allah ya tanada ga waɗanda suka kasa riƙe sha’awarsu.
Sha’awa irin ta samari da ‘yan mata daga Shaidan take, domin tana ɗaya daga cikin manyan tarkunansa da yake halakar da mutane da su.
Amma duk wanda ya ji tsoron tsayuwa da Ubangijinsa ya hana zuciyarsa abin da take so daga sha’awa da istimna’i, lallai Aljanna ita ce makomarsa matsuguninsa da izinin Allah Maɗaukaki.
Rubutawa ba tayi mana wahala ba, muna fatan sharing zuwa groups ba zai yi muku wahala ba 👏
Mun gode 🤝
📞 WhatsApp: +2348037538596 | +2348066627317
0 Comments