Hanyoyi da Matakai Goma (10) da Mutum Zai bi Domin Daina Istimna'i (Masturbation)


Hanyoyi da Matakai Goma (10) da Mutum Zai bi Domin Daina Istimna'i (Masturbation)

Istimna'i, wato yin wasa da al'umma domin gamsar da sha'awa, yana daga cikin abubuwan da suka yi yawa a cikin al'umma; maza da mata. Kuma yana haifar da matsaloli masu yawa sosai. Yana kama tunanin mutane, ta yadda wani yana so ya bari amma ya kasa, rayuwarsa ta yi ƙunci, lissafinsa ya dabarbarce, ya rasa natsuwa. 
Daga cikin shawarwarin da zan bayar wa wanda ya tsinci kansa a wannan halin, waɗanda nake roƙon Allah Ya sa su yi tasiri:

1. Fahimtar Haramcin Istimna'i a Musulunci: Mafi yawan malamai suna ganin istimna'i haramun, musamman duba da yadda yake haifar da matsala ga lafiya. Hadisi ya tabbata daga Annabi ﷺ, ya ce: لا ضرر ولا ضرار
Ma'anar hadisin a dunƙule: duk wani abu da zai cutar to haramun ne a Musulunci.
Allah yace:  
"وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ. إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ..."
Muminai su ne masu tsare farjinsu, sai dai ga matayensu da kuma abin da hannayenku na dama ya mallaka (ƙwarƙwara).. sa'an nan a ƙarshen ayar Allah Ya ce: duk waɗanda suka nemi wani abu baicin wannan, to lalle waɗannan masu ƙetare haddi ne.
Wannan yana nuni da cewa fitar da sha’awa ta hanyar da ba aure ba, ba ga baiwar da ya mallaka ba, to ba halal ba ne, wanda istimna'i zai shiga cikinsu.

2. Nisantar Abubuwan Da Ke Tayar da Sha'awa: Guje wa kallon batsa (pornography), hotuna ko labarai masu tayar da sha’awa.

3. Tsarkake wayar hannu ko kwamfuta daga abubuwan da za su jawo sha’awa. Duk wasu hotuna ko bidiyo da ke motsa sha'awa, ka cire su gabaɗaya.

4. Shagaltuwa da Ayyuka: ka cika lokacinka da ayyuka masu amfani kamar karatu da sana’a da motsa jiki da ayyukan alheri, wanda za su shagaltar da kai daga tunanin yin istimna'in.

5. Rage zama kai kaɗai a wurin da babu mutane. Yawan zaman kaɗaici yana iya dawowa da mutum tunanin istimna'i.

6. Yin Aure (idan akwai iko): Manzon Allah ﷺ yace:
  "يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ، مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ..." 
Ya ku matasa, wanda zai iya ɗaukar ɗawainiyar aure, to ya yi aure. Aure zai taimaka wa mutum matuƙa.

7. Idan babu halin yin auren, to ya dage da azumi da ibada. Kamar yadda Annabi ﷺ ya ya faɗa a ƙarashen hadisin da ke sama.

8. Ya riƙa halarto da ɓarnar da istimna'i yake yi wa rayuwarsa, kamar yadda masana suke faɗa: yana sanya mantuwa da rashin yarda da kai da rashin jin daɗin rayuwar aure da makamantansu.

9. Ya riƙa halarto da girman Allah a zuciyarsa a duk lokacin da ya ji sha'awar yin istimna'in, ya tuna Allah Yana ganinsa, to wannan jin kunyar Allah zai iya sanya mutum ya kame kansa.

10. Ya Tuntubi Likita: Yana da kyau koda ya bi duka waɗannan matasan, to ya tuntubi likita domin samun magunguna na musamman da za su taimaka masa.
Allah Ya datar da mu, Ya yare mana damuwarmu, ya sanya mu fi ƙarfin zuciyarmu.
© Isa Sadi

Post a Comment

0 Comments