CIWON MARA LOKACIN AL'ADA (HAILA 🌺) DA MAGUNGUNANSA.
Daga shafin Bashir Halilu.
Ciwon mara lokacin al’ada wani ciwo ne da mata ke ji a ƙasan cikinsu yayin da mahaifa ke ƙoƙarin fitar da jinin al’ada. Yana iya zama mai ƙarfi ko kuma mai sauƙi sannan wani sa'in yana iya zama mai matsala wani sa'in kuma ba matsala ba ne kuma zai iya dainawa da kansa zuwa wani lokaci.
ABUBUWAN DA KE KAWOWA MATA CIWON MARA LOKACIN AL'ADA.
1. Murɗawar mahaifa domin fitar da jinin al’ada.
2.Yawan sinadarin "prostaglandins", sinadarin da ke taimakawa wajen murɗawar mahaifa, da taimakawa zubar jini da kuma sarrafa zafin jiki, idan wannan sinadari yai yawa a jikin mace yana iya sa wa ta ji zafi yayin fitar jinin al'ada.
3. Cututtuka kamar:
a) "Endometriosis" wata cuta ce da ke sa fata ta fara tsiro acikin mahaifa ko cikin hanji ko mafitsara da dai sauransu. Samuwar wannan ciwo na sa mace zubar jini mai yawa, ciwon mara bayan al'ada, ciwon ciki yayin saduwa da matsalolin haihuwa.
b) Samuwar tsiro a cikin mahaifa wato "Fibroid".
c) Ciwon sanyi na cikin mahaifa wato "Infection"
4. Ciwon damuwa na iya ƙara radadin ciwon zubar jinin al'ada
5.Rashin bacci da tarawa kai gajiya na ƙara tsananin ciwon.
6. Rashin motsa jiki.
HANYOYIN MAGANCE CIWON MARA
1) Citta da Zuma.
A tafasa rabin cokali na garin citta, ɗanya, in busasshiya ce a ɗan rage kaɗan, a cikin ruwa, a tace, a sa zuma cokali ɗaya, a sha sau 2–3 a rana. Za a fara sha kafin a fara al'ada da kuma lokacin al’adar.
Yin wannan haɗi yana rage murɗawar mahaifa da kumburi.
2) Tafarnuwa da Madara.
A samu Tafarnuwa guda biyu zuwa uku (2–3)
Madara kofi ɗaya (1).
A daka tafarnuwa a tafasa da madara, a sha da daddare kafin kwanciya bacci. A fara kwana 2–3 kafin al’ada ta zo.
Tafarnuwa tana kashe kumburi da hana ciwo.
3) Ruwan ganyen na’a-na’a.
A tafasa ganyen na'ana'a a cikin ruwa, a tace, a sha ruwan kamar shayi. A iya haɗawa da zuma
Wannan na sanyaya mahaifa da kawar da radadi.
4) Ruwan kanumfari da lemon tsami.
A tafasa kanumfari a ruwa, a tace, a zuba ruwan lemon tsami da zuma kaɗan, a sha safe da yamma.
Kanunfari na rage zafi, yana maganin kumburi.
5) Ruwan ganyen zogale.
A tafasa ganyen zogale a cikin ruwa, a tace ruwan, a sha sau 2 a rana.
Zogale na ƙarfafa jiki da rage zubar jini da ciwo.
Idan ciwon mara ya cigaba ko an kasa gano kansa to ya kamata a je asibiti ko a nemi maganin gargajiya.
Duk mai bukatar magungunan da muke siyarwa yana iya tuntuɓarmu a wannan lamba 08134434846.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da Magunguna na Musulunci da na gargajiya.
0 Comments