NA
MUHAMMAD MUHAMMAD ABUBAKAR
ALBANI MISAU.
GABATARWA.
Godiya ta tabbata ga Allah (SWA) wanda ya halicci dukkan komai. Babu wani abu mai faruwa, sai tare da nufinsa da ikonsa da kaddarawarsa. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa, har ya zuwa ranar tashin Alkiyama.
Lokaci ya yi da da'awar Islama takai mu gane cewar komai na shari'ah baya halatta sai da iliminsa.
Don haka bai halatta ga wani ya yi nufin aure ba, har sai ya san hukuncin auren.
Amma za ka yi mamakin mai imani da Allah da Manzonsa komai nasa ya zama kara zube, babu sanin hukuncin Islama, ba shi da ilimin sauke farillan kansa, to gaya mun ya ya zai dora wa kansa hakkin waninsa, alhali sallah ma bawa bai karanta ba, wai kuma wannan shine za a ba shi tarbiyyar wata!
Ga shi ya yi aure wai zai yi rayuwar koyi da Manzon Allah (SAW).
Kowa na kokari wajen neman ilimin rayuwar duniya, amma sha'anin rayuwar da ta hada da Allah ana yine da ka, ta ya ya wannan idan ya yi aure zai zama jagora kan hanyar Manzon Allah?!.
Don haka wajibine ga matasa kafin kowa ya doshi yin aure sai ya je ya karanta hukuncin aure da dukkan ilimin da ya shafi auren a cikin addinin musulunci, domin baya halatta ka aikata aiki sai kasan hukuncin addini a kansa, ashe a karkashin haka muke iya fahimtar cewar da yawa daga cikin masu kokarin aure daga samari baya halatta su yi aure a haka.
Ya zo cikin sharhin Ibn Majah "Abubuwa da yawa ba wajibi ne mutum ya yi iliminsu ba, amma ba ya halatta kuma ka aikata abin, idan ka tashi sai ka yi iliminsa".
Misali: Ba wajibi bane kowa yasan ilimin kasuwanci, amma baya halatta ga musulmi ya fara kasuwanci sai ya yi iliminsa, haka ma aure iliminsa ba ya zama wajibi akan kowa, amma duk wanda ya yi nufin aure, baya halatta ya yi sai yasan hukuncinsa a cikin musulunci, kamar sanin ilimin aure, hakkin miji da mata, nauyin ilimi da rayuwar matansa da ibadarsu da sauransu.
To mai za ka ce ga wanda ya yi aure bai iya ko da Ahlari ba?! Ga shi tinda ya yi wayo yake kokarinsa wajen karatun boko don neman duniya.
Don haka 'yan uwa na nu yi kokari wajen neman yadda za mu sauke nauyin da ke kanmu. Allah ya mana dace gaba daya amen.
MUHAMMAD ALBANI MISAU.
AURE:-
Aure dai sunna ne mai karfi daga cikin sunnonin Manzannin Allah (SWA), kamar yadda Ayoyi da dama suka nuna mana, Allah yana cewa: "HAKIKA MUN AIKO MANZANNI (da yawa) KAFIN KA ZO (ya Muhammad (SAW)) KUWA MUKA SANYA A GARE SU, MATAYE (da yawa) DA ZURIYA....." [Ra'adi 38]. A wata ayar kuma yace: "YANA DAGA AYOYINSA (Allah) YA HALITTA MU KU MATAYENKUDAGA GAREKU (Maza da Mata), DOMIN KU NATSU IZUWA GARE SU, KUMA YA SANYA KAUNA DA TAUSAYI A TSAKANINKU, LALLAI CIKIN WANNAN AKWAI AYOYIN (lura) GA MUTANE MASU TUNANI" [Rum 21].
A wata ayar kuma umurni ya bayar da cewa:
"KU AURI ABIN DA YA YI MU KU DADI DAGA MATA, BIBBIYU, UKU-UKU KO HUR-HUDU, TO AMMA IDAN IDAN KUN JI TSORON BA ZA KU YI ADALCI BA (a tsakanin mata fiye da biyu!) TO KU (auri) DAYA TAK,......" [Nisa'i 3].
Saboda muhimmancin yin aure ne ma ya sa Annabi (SAW) ya hana wasu Sahabbai su fidiye kansu, kamar yadda Sahabi Sa'ad bin Abi Waqqas (ra) ya yi bayani. [Bukhari 1467].
Kuma Annabi (SAW) ya nuna cewa aure sunnansa ne:
"DUK WANDA YA KYAMACI SUNNA TA, TO BA YA TARE DA NI" [Bukhari 5063, Muslim 1401].
Dun haka aure sunna ce ta Manzanni da Annabawan Allah, kuma duk wani mai daraja ta wannan hanyar yake kare mutuncinsa, kuma sai kasan iliminsa kafin ka yi.
FA'IDODIN YIN AURE:-
Duk wanda ya samu halin yin aure namiji ko mace, to za su wayi gari sun cimma wasu abubuwa da dama, ga kadan daga ciki:
(a:Sunyi biyayya ga umurnin Allah (SWA) kamar yadda ayoyi suka gabata.
(b:Sun bi sunnan Manzon Allah (SAW) sun yi koyi da shi, kuma za su samu natsuwa da kwanciyar hankali.
(c:Sun yi maganin sha'awarsu ta 'yan Adam, sun kuma kare mutuncinsu.
(d:Sun biya bukatarsu ta hanyar da ta dace, ba ta tsinanniyar hanya ba!
(e:Sun taimaka wajen magance yaduwar barnace-barnace da ayyukan ash-sha.
(f:Sun kara yawan al'ummar Manzon Allah (SAW), idan sun hayayyafa kamar yadda Annabi (SAW) yc
"(Lallai idan kun yi aure kun hayayyafa) ZAN YI TAKAMA GA SAURAN AL'UMMA" [Abu Dawud 2050, Nasa'i 6/75].
(g:Ga samun lada mai yawa a wurin Allah, domin ladan aure kamar na sadaka ne, don Annabi (SAW) yc "A CIKIN JIMA'IN DAYANKU MA AKWAI (ladan) SADAQA" [Muslim 1006, Abu Dawud 1286].
SIFFOFIN WANDA AKE SO A AURA.
Akwai siffofi da ake so, miji da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin su nemi junansu da aure, don samar da farin ciki da natsuwa a tsakaninsu, ga su nan kamar haka:-
(1) SIFFOFIN NAMIJIN DA ZA A AURA:-
a.Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, don mai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.
(b.Ya kasance ya dan haddace wadansu Ayoyin Alqur'ani, don sukan kara wa bawa Imani, wanda ya haddace ayoyin kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne a wurin Allah.
(c.Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, zagi, takuri da cin mutunci ba, a inda babu gaira babu dalili.
(d.Ya kasance yana da kuzarin biyan bukatan Iyalinsa da nemo mata abinci, suturi, wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum tun da Annabi (SAW) yc
"WANDA YAKE DA HALI DAGA CIKINKU YA YI AURE..." [Bukhaqi 5065, Muslim 1400].
(e.Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, da samun zamantakewa mai kyau.
(f.Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakanne ta hanyar 'yan uwansa ko zuriyars. Ko da yake haihuwa ta Allah ce, yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma yadda ya so, wani kuma sai ya sanya shi AQIM, kamar yadda yc
"YA KAN SANYA WANDA YA GA DAMA AQIM (wanda ba ya haihuwa)" [Shura 50].
(g.Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtan juna, don samun zaman lafiya. Anan nake jan hankalin 'yan uwa mata da kada su kuskura su auri mutumin banza, mai halin mutanen iska, don za su shiga mayuwacin halin da zai sa ba za su ji dadin rayuwarta ba har abada! Duba (Sahih Fiqhis Sunnah 3/103-107).
SIFFOFIN MACEN DA ZA A AURA
(a.Takasance ma'abuciyar addini. Annabi (SAW) yc
"...KA RABAUTA DA MAI ADDINI, ZA KA YI RIBA" [Bukhari 5090, Muslim 1466]
(b.Ta kasance tana da kyau, hali da mutunci, kamar yadda Annabi (SAW) ya fara lissafawa a Hadisin da muka ambata a sama.
(c.Ta zama mai tausayi da kauna, wanda ba za ta azabtar da miji ko wulakanta shi ba, don Annabi (SAW) yc
"WADANNAN SU NE MAFIYA ALHERIN MATA".
(d.Ta kasance tana da amana da biyayya, Annabi (SAW) ya yaba wa irin wadannan matan, amma mace fitsararriya ko shedaniya babu abinda za a samu daga gare ta sai fitina da tashin hankali.
(e.Ta kasance budurwa, wanda wani bai taba saninta ba, don akwai wanda ya yi aure a zamanin Annabi (SAW) sai ya tambaye shi, "BUDURWA CE KO BAZAWARA?" sai ango ya amsa da cewa: Ai bazawara ce! Sai Annabi (SAW) yc "AI DA BUDURWA CE (ka aura), KA YI WASA DA ITA, (itama)TA YI WASA DA KAI!" (Bukhari 5079, Muslim 715). Ba wai an hana auren Bazawara bane, matukar an samu fahimta, sai dai ba a san abin da ya koro ta daga gidan mijin farko ba, don haka a yi kokarin kiyaye martabar aure, idan anyi sakin nan ba alheri ba ne, idan babu dalili.
(f.Ta kasance mai haihuwa, saboda Hadisin da ya gabata a can baya na yawaitar al'ummar Annabi (SAW) da yin aure, ga wanda Allah (SWA) ya kaddara mu su haihuwa.
Wadannan siffofi su ake bukata ga ma'aurata su siffantu da su, don tabbatar da alherin aure da samar da natsuwa da kwanciyar hankali duniya da lahira. Allah ya azurta mu da mata na gari haka su ma matan ya ba su mazaje na gari.
YADDA AKE NEMAN AURE DA KULLA SHI.
Idan NAMIJI ya ji yana kaunar wata mace, kuma yana son ta da aure, to ya halatta ya kalle ta yadda ya dace, don tabbatar da abin da ya yi niyya, idan Allah (SAW) ya yarda.
Wannan gani da zai yi mata, musulunci ya halatta masa, tun da gani ne na neman tabbatar da alheri bana barna ba, bayan samun izinin waliyyanta, bayan ya ganta, sun zanta sun amince da juna, to haramun ne kuma wani ya yi kundumbala ya shigo, saboda fadin Annabi (SAW):
"KA DA WANI YA YI NEMAN AURE AKAN NEMAN DAN UWANSA, HAR SAI YA BARI (idan ba a samu amincewa ba), KO KUMA SAI MAI NEMAN YA BA SHI IZINI (Idan ya ga kamar ba zai kai labari ba)" [Nasa'i 6/73 don karin bayani duba littafin ALWAJIZ 281-282].
Amma idan manemin mutumin banza ne, malamai sun yi bayanin cewa ya halatta a wargaza shirinsa.
Idan namiji zai yi zance da mace, to a kiyaye wadannan sharudda:
(1.Kada ya kebanta da ita a wani wuri na daban, ya zama na suna tare da muharransa mata, ko kuma nata maza don kar su yi barna.
(2.Kada ya yi mata kallon jin dadi ka na sha'awa.
(3.Kada yayi hannu da ita, ko ya taba jikinta, don bata halatta masa ba, har sai an daura aure.
(4.Ya zama da kyakkyawar niyyar zai aure ta ne.
(5.Ya halatta ya yi zance da ita, ya tambaye ta, ta tambaye shi, abinda ya dace, don su fahimci juna, don kar a yi aure, daga baya a zo ana dan da na sani.
(6Kada ya fita da ita yawo, ko shakatawa, ko da an yi masa alkawari, yin haramunne, ko da kuwa babu abinda zai faru, fita da ita bai halatta masa ba, har sai an yi aure (Baiko fa ba aure ba ne tun da ana iya warware alkawarin saboda wani dalili, don haka sai a yi a hankali).
duba (FIQHUS SUNNAH LINNISA'I na Abu Malik da BAIKO BA AURE BA NE na Mal. Ahmad Murtala Kano).
Da za a kiyaye wadannan sharrudan, da za a samu natsuwa da jin dadi, rashin kiyaye su ne ya haifar mana da abubuwan takaici da 'ya'yan shegu marasa asali.
Idan abubuwa sun daidaita, sai batun daura aure tare da kiyaye wadannan sharrudan:
(a.Waliyyi:- Doe ne a samu yardarm waliyyi, don duk auren da aka daura ba tare da yardar waliyyi ba, to auren bai yi ba, idan akwai rikici ko matsala, sai shuguba ya shiga maganar ya warware ta, amma ta hanyar da ta dace.
Don duk matar da ta daura aure wa kanta, ba tare da waliyyinta ba, ta zama karuwa domin: "MAZINACIYA ITA CE TAKE AURAR DA KANTA".
Anan nake jan hankalin iyaye su daina yiwa 'ya'yansu auren dole, don hakan ba daidai ba ne, kuma hakan yana haifar da illoli masu yawan gaske, Annabi (SAW) yake cewa "A NEMI SHAWARINSU, A TAMBAYE SU, DON A SAMU DAIDAITO". Don haka iyaye sai a hankata, a bar yarinya ta auri wanda take so.
(b.Sadaki:- Dole ne a bayar sadaki a bisa abin da aka amince a kansa, mai sauki, wanda babu tsanani a ciki, don samun karin albarka a wurin Allah (SWA). Annanbi (SAW) yace:- "ALBARKAN AURE YANA DAGA KLARANCIN SADAKLI".
Allah (SWA) yana cewa "KU BA WA MATA SADAKINSU, KYAUTA CE (daga Allah, da dadin rai)" [Nisa'i 04].
Don haka sadakin na mata ne, kuma idan babu matsi sai a bayar da yawa babu laifi, don sadakin Annabi (SAW) yana da yawa. Amma batun dole kayan aure sai ya kai kaza ko sai anyi akwati adadi kaza, wannan baya cikin sharadin aure, da fatan iyaye da 'yan mata za su hankalta (An kusa a fara kai kayan aure a gari ya yi zafi ko akwati mai Giwa).
(c.Kulla aure: wasu kalmomi ne da ake amfani das u na nema da bayarwa, idan an yi wannan tsakanin waliyyin mace da miji ko wakilinsa, shi ke nan, aure ya kullu, sai a sanar da jama'a.
Amma zuwa wuraren barna na masha'a tare da maza da mata, haramun ne, ba musulunci ba ne yahudanci ne, kuma irin wannan baya albarka, kuma da wuri yake lalacewa, Allah ya sauwake.
Bayan an gama wannan, sai mata ma su hankali da natsuwa su dauki amarya su kai ta gidan mijinta, tare da yin nasihohi ko bayar da shawarwarin da suka dace, don tabbatar da zaman lafiya da samun arziki.
Don karin bayani a duba [FIQHUS SUNNAH na Sayyid Sabiq, da ADABUZ ZIFAF na Albani].
FADAKARWA
(a.Idan an daura aure, kafin matar ta tare a gidan mijinta, ko bayan ta tare, ana son a gabatar da walima. Walima sunnah ce mai karfi, a yi ta da abin da Allah (SAW) ya hore, ko da taimakon da za a samu, a tara mutane maza ne ko mata bisa tsarin Shari'a, a ci abinci, wannan shine walima. Mata na iya shirya walimarsu matukar babu sabon Allah a ciki,
duba littafin [AZZAWAJ na Dr. Muhd Ibrahim Alhafnawy 41].
Annabi (SAW) ya yi walima, kuma ya kwadaitar da Sahabbansa (RA), da su yi ta, har ma yace wa Anas bin Malik (RA) yayin da ya yi aure: "KA YI WALIMA KO DA (yankan) DAN AKUYA NE" [Bukhari 5169].
Kuma duk wanda aka kira shi dole ne ya amsa, sai dai idan yana da uzuri, sai ya sanar, kuma duk wanda ba kira shi ba, idan ya je, ya yi laifi.
(b.Taya ma'aurata murna da farin ciki sunna ce, tare da yi mu su addu'a, kamar yadda Annabi (SAW) yake yi
"Barakal lahu laka, wa baraka alaika, wa jama'a baina kuma fi khairin"
ma'ana: "ALLAH YA YI MA KA ALBARKA, YA KARA MAKA ALBARKA, YA HADA KU CIKIN ALKHAIRI"
[Abu Duwud, Tirmizy da Ibnu Majah. Hadisin Abu Huraira].
Ana iya bayar da gudumawa gwargwadon hali idan akwai, kamar yadda Hadisai da dama suka tabbatar da taimakekeniya a tsakanin Sahabbai (RA), amma mutum ya debo rikicin aure don gadarar gudumawa da roko ko maula ba daidai ba ne.
(c.Yayin da ango zai shigo bayan an kawo masa amarya dakinta, ana son ya yi sallama, wannan alama ce ko albishir ne na samun SALAMA (zaman lafiya) a tsakani Insha Allahu, domin bayan Ummu Salma (RA), ta tare gidan Annabi (SAW), da zai shigo, sai ya yi mata sallama. Yana da kyau, ya shiga da wani abin dadi ko zaki, sai ya fara kurba sannan ya ba ta, ita ma ta sha, saboda haka Annabi (SAW) ya yi, yayin da ya shigo dakin Nana Aisha (RA) [Hadisin Nana Asma'u (RA), Riwayar Ahmad 6/456] kuma muhimmin abu ne su tashi su yi alwala don su yi sallan nafila raka'a biyu tare, idan ba ta cikin jinin al'ada, yana gaba, Amarya na baya, bayan sun kammala kuma sai su yi addu'a, zai yi addu'ar Allah ya ba shi alherin matar, ya kuma nemi tsari daga sharrinta, kamar yadda Abdullahi bin Mas'ud, Abu Zarr da Huzaifah (RA), suka bayyana wa Abu Sa'id Maulan Abu Asid [Riwayar Ibnu Abi Shaibai].
Akwai wata addu'ar da take da muhimmanci ainun, sai ya riki gashin goshinta, ya yi Bismillah, sai ya ce
"ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA MIN KHAIRIHA, WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAIH, WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIH".
A kwai wata addu'ar da take da muhimmanci ainun, idan ya rike gashin goshinta, sai ya yi bismillah, sai ya ce "ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA MIN KHAIRIHA, WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAIH, WA A'UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIH"
ma'ana "Ya Allah lallai ni ina rokonka alherinta (wannan amaryar) da alkhairin da ka halicce ta a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta, da sharrin da ka halicce ta da shi"
(Abu Dawud 2160, Nasa'i 241-264 da Ibnu Majah 1981).
Daga nan kuma sai su ci gaba da tattaunawansu a matsayin sababbin ma'aurata.
Amma lallai ne, idan mutum zai sadu da iyalinsa, ya yi kokari ya rinka karanta wannan addu'ar: "BISMILLAHI, ALLAHUMMA JANNIBNISH-SHAIDANA, WA JANNIBISH-SHAIDANA MA RAZAQTANA".
Ma'ana: "Da sunan Allah, ya Ubangiji, ka nisantar da ni daga shaidan, kuma nisantar da shaidan daga abin da ka azurta mu da shi"
[Bukhari 5165, Muslim 1434].
Annabi (SAW) yace "IDAN HAR ALLAH YA KADDARA ARZIKIN SAMUN DA, TO SHAIDAN BA ZAI SHAFE SHI BA HAR ABADA".
Da ma'aurata za su rinka yin wannan addu'ar a ka da yaushe, da an ci nasara a rayuwar aure, 'ya'ya da zuriyya gaba daya.
(d.Haramun ne saduwa da mace a lokacin da take cikin al'adar haila ko haihuwa, har sai ta yi wanka, ida mutum ya yi hakan (lokacin da haila ko haihuwa) ya saba wa Allah (SWA), Sai ta yi tsarki, ta yi wanka sannan ya sadu da ita, Allah (SWA) yana cewa "MATAYENKU AI GONAKINKU NE, KU JE MU SU TA INA KUKE SO (Inda ya dace)" [Baqara 223].
Wato ta ko'ina mutum zai iya yi, amma banda ta dubura, don yin haka Liwadi ne, kuma haramun ne, hanya ta la'ana.
Kuma haramun ne bayyana asiran saduwa da iyali, Annabi (SAW) yace "DUK WANDA YA YI HAKA SHI NE MAFI ASHARARAN MUTANE RANAR ALQIYANAH" [Muslim 1437, Abu Dawud 4870].
Da za a kiyaye wadannan da za a samu albarkar aure, 'ya'ya da zuriyya, Insha Allahu.
HAKKOKIN MACE AKAN MIJINTA.
Wadannan hakkokin, kiyaye su shi ne kashin bayan tabbatuwar aure da ni'imarsa, rashin kiyaye su kuwa babbar matsala ce, ga su nan kamar haka:
(1.Samar mata da wurin zaman da ya dace don kare mata mutuncinta, kamar yadda Allah (SWA) yc
"KU ZAUNAR DA SU A INDA KUKE ZAUNE GWARGWADON SAMUNKU" [Dalaq 6].
l
(2.Dole ne ya sama mata abinci gwargwadon karfinsa, kamar yadda Allah (SWA) yc
"MAI WADATA YA CIYAR DAGA WADATARSA, WANDA KUMA AKA KUNTATA MASA ARZIKINSA, TO YA CIYAR DAGA ABIN DA ALLAH YA BA SHI" [Dalaq 7].
(3.Ya tufatar da ita a lokacin da ya dace, gwargwadon halinsa, Annabi (SAW) yc
"KA TUFATAR DA ITA, IDAN KA TUFATAR DA KANKA" [Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850].
(4.Biya mata bukatarta ta 'ya mace wannan dole ne, gwargwadon yadda llAllah (SWA) ya halicce su, haka zai taimaka wajen tsare mata mutuncinta, kuma hakki ne babba, kamar yadda Annabi (SAW) yake cewa
"LALLAI GA IYALINKA AKWAI HAKKINTA A KANTA" [Bukhari 1977, Muslim 1159].
Duk wanda yake tare da iyalinsa, har ya kaurace mata tsawon watanni 4 babu saduwa, sai ta yi karansa wajen magabata, ko ya sake ta, ko ya dawo ya gyara hali, wannan ai cutarwa ce babba.
(Wannan shi ake kira IYLA'I, kamar yadda ayoyin Bakara suka yi bayani, duba bayanin Malamai a cikin ALFIQHU ALAL MAZAHIBIL ARBA'AH na Abdurrahman Aljuzairy).
(5.Dole ya karantar da ita yadda za ta bauta wa Allah (SWA), ko dai ya yi da kansa ko ya roki wani, ko ya dauki nauyin hakan.
Rashin koyar da mata addini hatsari ne babba, don kusan duk tarbiyar gidan a hannunsu take, idan ba su san addini ba, yaransu za su tashi sun fi su lalacewa, sai dai wani ikon Allah.
Koyar da ita addini shine kare kai da iyalai daga shiga wuta, kamar yadda Allah ya yi umurni a inda yake cewa
"YA KU WADANDA SUKA YI IMANI, KU TSARE KANKU DA IYALANKU DAGA WUTAR DA MAKAMASHINTA MUTANE NE DA KUMA DUWATSU.." [Tahrim 6].
Amma koyar da ita wani ilimi ko sana'a wannan cigaba ne da samun saukin taimako a rayuwa.
(6.Ka da ya cutar da ita, da duka, zagi, musgunawa da kaskantarwa, don mace tana da daraja a wajen Allah (SWA), duk abin da ya faru sai a bi dokokin da Allah ya gindaya, kar a bi son zuciya. Hakuri da danne zuciya suna da muhimmanci a cikin al'amuran duniya, ba ma a na aure kawai ba, don haka abin da bai taka kara ba balle ya karya, bai kamata ya zama bala'i ba.
Idan mace ta yi laifi har ga Allah, akwai mataki guda 3 kamar haka:
A .WA'AZI: Za a yi mata wa'azi na bayanin muhimmancin biyayya da illar saba wa miji ko bala'in saki (Idan Allah ya ba mu lokaci za mu tattauna akan SAKI insha Allahu).
B .KAURACEWA: Idan wa'azi bai yi ba sai a kaurace mata a wajen kwanciya, a ki kulawa da ita a cikin dakinta, amma dole ne a bata abinci don Annabi (SAW) yc
"KADA KA KAURACE MATA SAI A CIKIN DAKI" [Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850 da Ahmad 4/447].
C .DUKA: Daga nan kuma sai dukan ladabtarwa, ba mai cutarwa ba, ban da dukan fiska, ban da zagi ko bakaken maganganu, ba kuma a gaban yara ko a waje ba. Idan abu ya faskara kuma sai a je wajen magabata don su warware matsalar. Wadannan matakai guda 3 Alqur'ani ne ya ambace su. Duba [Suratul Nisa'i 34].
Wannan shine tsari, daga nan kuma, ko a yi sulhu ko a rabu, Allah ya sauwake.
(7.Rashin bayyana sirrinta: Haramun ne ya bayyana sirrinta, kamar yadda ita ma aka haramta mata bayyana nasa. Annabi (SAW) ya yi gargadi akan bayyana sirrin juna, tun da an hadu dama dole ne kowa yasan asirin kowa.
(8.Lallai ne a ba ta izinin fita idan ya zama dole ko ya kama, don zuwa Asibiti, Makaranta, gidan Iyaye ko na 'yan uwa, da sharadin rashin aukuwar fitina, idan akwai matsala sai a dauki matakin gyara.
(9.Dole ne ya yi wa matarsa kyakkyawan zato, ban da tuhuma, zargi da dari-dari, idan har akwai shakku to sai ya dauki matakin gyara a zahirance ba a munafunce ba. Allah (SWA) yc
"YA KU WADANDA KUKA YI IMANI, KU NISANCI DA YAWA DAGA ZATO, LALLAI WANI SASHIN ZATO LAIFI NE, KA DA KU YI LEKEN ASIRI..." [Hujrat 12].
Shi ya sa ma Annabi (SAW) yc
"IDAN MUTUM YA YI TAFIYA KADA YA DAWO GIDA DA DADDARE KWATSAM, BA TARE DA YA SANAR DA IYALANSA BA" [Bukhari 5244].
Kuma idan mijin mace ba ya nan, idan ya kama a shiga wurinta, to duk wanda zai shiga ka da ya je shi kadai, ya neni wani muharraminta, ko wasu mata, don kauce wa mummunan zargi.
(10.Yin adalci dole ne ga matan da suke da yawa wajen mazauni, tufafi, abinci da abubuwan masarufi. Amma a bangaren sadaki, walima da kauna, ba lallai ne ya zama daidai wa daida ba, ana iya samun bambanci, Allah (SWA) yc
"BA ZA KU IYA YIN ADALCIN (So da Kauna) A TSAKANIN MATAYENKU BA, TO AMMA KA DA KU KUSKURA KU KARKATA (Zuwa ga Mowa) GABA-DAYAN KARKATA, KU KYALE (Wancar Boran) KAMAR WADDA AKA RATAYA (ba a kallonta sai za a yi amfani da ita)" [Nisa'i 129].
Kauna da So suna samun asali ne saboda; hankalin mace, kyawunta, kudinta, ko matsayin iyayenta, ds, don haka ayi dai a bi hankali ya ku mazaje kar a fada cikin halaka!
Don haka adalci dole ne a tsakanin mata da 'ya'ya, idan mutum ba zai iya yin adalcin ba, sai ya tsaya ga mace daya, kamar yadda Aya ta nuna, [Nisa'i 03].
Mace dayan ma dole ne a kiyaye mata hakkokinta, idan ba haka ba asha azaba.
(11.Yin ado da kwalliya wa mace hakki ne, don ka da hankalinta ya karkata zuwa ga mazajen waje. I
bnu Abbas (RA) yc "LALLAI NI INA SON IN YI ADO WA MATATA, KAMAR YADDA NAKE SON TA YI MINI, SABODA ALLAH (SWA) YANA CEWA: "SU MATAN SUNA DA IRIN ABIN DA YAKE KANSU (na hakkoki a gare ku) DA KYAUTATAWA" [Bakara 228].
(12.Yin wasanni, sake fuska, tattaunawa da hira hakki ne mai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma'aurata, kamar yadda aka samo cewa Annabi (SAW) yana wasa da matansa, yana hira da su, yana sake musu fuska. Yace
"MAFI ALKHAIRINKU SHI NE MAFI ALKHARI WA IYALANSA, NI KUMA (Annabi SAW) NA FI KU ALKHAIRI WA IYALINA" [Tirmizy 3892, Ibnu Hibban 1312].
(13.Dole ne a yi mu'amala mai kyau ga iyalai, hakan shi zai tabbatar da dorewar ci gaba, kwanciyar hankali da more rayuwar duniya da lahira. Idan suna da yawa zai taimaka wajen sassauta mumnunan kishi da kiyayya a tsakaninsu da rigingimun da babu gaira babu dalili.
Kiyaye wadannan hakkoki na mata shine zamantakewa mai kyau da samun arziki da albarka, Allah (SWA) yc
"KU ZAUNA DA SU DA KYAUTATAWA (mai kyau)" [Nisa'i 13].
HAKKOKIN MIJI AKAN MATASA
(1.Dole ne ta yi masa biyayya, ga abinda yake ba sabo ba ne, Annabi (SAW) yc "BABU BIYAYYA A CIKIN SABON ALLAH, ABIN SANI DA'A TANA CIKIN ABIN DA SHARI'A TA SANI NE" [Bukgari 7257, Muslim1840].
(2.Ta zauna a gida ban da yawace-yawace, ban da fita sai da yardarsa.
(3.Ta amsa masa idan ya nema ta, ba tare da matsala ba.
(4.Ka da ta bar wata ko wani ya shiga gidansa sai da yardansa, Annabi (SAW) yc "KADA WATA MATA TA BAYAR DA IZININ (shiga) GIDAN MIJINTA, ALHALI YANA NAN, SAI DA YARDARSA" [Muslim 1026] amma idan bai yarda ba, ko baya nan bai halatta ta bar wata ko wani ya shigo gidan ba.
(5.Ba za ta yi azumin nafila ba, idan yana nan, sai ya yarda, saboda Hadisin da ya hana haka.
(6.Ba za ta dauki wani abu daga dukiyan mijinta ta bayar ba, sai ya amince, Annabi (SAW) yc "KA DA MACE TA BAYAR DA WANI ABU DAGA GIDAN MIJINTA SAI YA YARDA" [Abu Dawud d.s].
(7.Za ta yi hidima wa mijinta, da kula da al'amuran yaransa, kamar abinci, wanki, share-share d.s, daidai gwargwado, tun da zaman aure zama ne na cude ni in cude ka.
Nana Fatimah (RA) diyar Annabi (SAW) tana aikin wahala ainun a gidan mijinta Aliyu bin Abi Dalib (RA) [Bukhari 5361, Muslim 2182].
Nana Asma'u (RA) diyar Abubakar (RA), ita ma tana hidima ainun, har kulawa sosai take yi da dokin mijinta [Bukhari 5224, Muslim 2182].
Idan miji ya samu dama sai ya sauwake wa matansa, ko ya rinka taya su, don Annabi (SAW) ya kasance yana taya matansa aikace-aikacen gida, idan an yi kiran sallah sai ya fita, ya tafi masallaci, kamar yadda Hadisin Nana Aishatu (RA) ya nuna. [Bukhari 676
(8.Wajibi ne ta kare mutuncinta, na mijinta da na 'ya'yansa da kuma dukiyarsa, banda almubazaranci, Allah (SAW) yc
"MATAYEN KWARAI, MA SU KARKANTAR DA KAI NE, MA SU KIYAYE (mutunci da dukiya ne) GA GAIBIN DA ALLAH YA KIYAYE" [Nisa'i 34] <Ya Allah ka ba mu mataye na kwaira>.
(9.Ta gode masa idan ya yi abin kirki, ka da ta muzunta masa, ko ta yi masa gori, kuma duk abin da ya samo ya kawo gwargwodon halinsa, ta karba hanu bibbiyu, don Annabi (SAW) yc
"ALLAH BA YA KALLON RAHAMA WA MATAR DA BA TA GODE WA MIJINTA, KUMA BA TA WADATUWA DAGA GARE SHI (da duk abin da ya yi) [Nasa'i 249]<Ya Allah ka tsare mu da irin wannan matan>.
(10.Yin ado wa miji da gyara jiki shi ma babban hakki ne, Annabi (SAW) cewa ya yi:
"FIYAYYEN MACE, ITA CE WADDA ZA TA FARANTA MA KA IDAN KA DUBE TA" [Nasa'i da Ahmad].
(11.Ka da ta cutar da shi ko ta bakanta masa rai, saboda idan ta yi haka, matansa na Aljanna wadanda suke jiransa za su tsine mata, su la'ance ta, su ce: "...YA SHIGO WAJENKI NE FA KAWAI! KWANAN NAN ZAI RABU DA KE YA DAWO WURINMU" [Tirmizy 1184, Ibnu Majah 2014].
<To fa mata! Kun ji matanmu na Aljannah abinda za su ce!>
(12.Ta yi wa iyayensa da 'yan uwansa mu'amala mai kyau, don haka zai sa ta samu karbuwa a wurinsu, su rinka yi mata addu'a ta fatar alheri.
Mu'amala mai kyau, ita ce: Sake musu fiska, maraba da su, ba su abinci, kyautata musu ds.
(13.Ka da ta kuskura ta nemi SAKI, sai idan abu ya gagara, kuma ta hanyar da ta dace, Annabi (SAW) yc
"DUK MATAR DA TA TAMBAYI MIJINTA SAKI BA TARE DA WANI LAIFI BA, TO HARAMUNNE TA JI KANSHIN ALJANNA" [Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209 ds].
Wadannan sune hakkokin da aka dora wa mace dangane da mijinta, idan ta kiyaye su, za ta zama ta kwarai, kuma daya daga cikin manyan matan Aljannah, kamar yadda Annabi (SAW) ya bayyana da cewa:
"IDAN MACE TA SALLACI (salloli) BIYAR DINTA (na farilla), TA YI AZUMIN WATAN TA (na Ramadan), TA KIYAYE FARJINTA (daga lalata), TA YI BIYAYYA GA MIJINTA, SAI A CE MATA "KI SHIGA ALJANNA TA KOFOFIN DA KIKA GA DAMA"" [Ibnu Hibban 4163].
Wannan Mata itace mace saliha, mai samar da annashuwa da albarkan duniya da lahira, don Annabi (SAW) yc
"DUNIYA JIN DADI NE DAN KADAN, AMMA FIYAYYEN JIN DADINTA ITA CE MACE SALIHA".
Allah ya ba ku ikon kiyayewa amen.
Da ma'aurata za su kiyaye wadannan hakkoki da tsakaninsu, wallahi da an samu zaman lafiya da natsuwa a duniyar aure gaba daya, kuma da lahirar ma tayi kyau.
ALHAMDU LILLAH!
KAMMALAWA
Wannan shine karkashen dan abin da Allah (SWA) ya ba ni ikon rubutawa dangane da abin da ya shafi sha'anin Aure.
Allah ya gafarta mun ni da ku gaba daya. Da fatan za ku sanya ni a du'a'inku na alkhairi.
MUHAMMAD ALBANI MISAU.
(mukhair1434@gmail.com) (mukhair@hootmail.com)
0 Comments