MAGANIN RAGE QIBA DA TUMBI:
SHARE 🔔
TAMBAYA
Salam Dan Allah inaso adan fada min abubuwan dazan yi amfani dasu wajan ragi kiba da tumbi.wslm.
AMSA
Wa'alaikumussalam.
Ga wasu hanyoyin nan agwada da izin Allah, insha Allahu za'a samu biyan buqata.
.
MAGANIN RAGE QIBA⤵
Da farko dai ki zama mai yawan motsa jikinki wajen ( training ).
Na biyu sai ki samu wadannan sirrin kina yin shayi kina sha safe da yamma.
~shayi ba madara.
~ Lipton.
~ lemon tsami.
~ na’a-na’a.
Da farko ki tafasa shayi ba madara tare da Lipton da na’a-na’a da kayan kamshi, sai ki matsa lemon tsami a ciki ki sa sukari ki rikka sha safe da yamma tare da yawan motsa jinkinki a duk lokacin da kika sha. To insha Allah Zaki ga yadda jikinki zai komo bayan wata daya.
MAGANIN RAGE TUMBI⤵
1⃣ ki tanadi lemun zaki da citta A tafasasu minti hudu zuwa biyar a yi shayi ban da madara A zuba MA UL KHAL cokali daya ko biyu cikin kofin shayin a sha da ganyen shayi kamar Lipton da zuma ko suga Za a yi haka sau biyu a kullum Haka kuma za ki iya amfani da lemun tsami amadadin MA UL KHAL din Bayan haka mutum ya rika motsa jiki a kai a kai Idan kina ganin cewa ba ki da lokacin motsa jiki to sai ki rika gudanar da wasu aikace aikacen gida da kan ki.
2⃣ Bayan wannan za ki iya samun kwayar ya yan Zogale a markada a hada da ruwan zafi a rika sha da safe da dare yana maganin rage kiba ko tumbi.
3⃣ hulba garin na'a-na'a garin kanun fari zuma lemon tsami farin kwalli manna'a-na'a ki hadewadannan ganye guri 1 ki tafasa ki sami farin kwalli dunqulen zaki saka a ciki, idan ya kai kamar minti 5 sa ki cire, sannan ki saka zuma a cikin ruwan sha.
ki samu man na'a-na'a rinka shafawa, tumbi ki zai ragu insha Allah idan kuma anason rage kiba ne za 'a rinka zuba lemon tsami a ciki.
4⃣ Ganyen na’a na’a kamar guda 10 zuwa 12._
_Kokumba guda daya dan madaidaci.Lemon tsami guda daya.
Danyar cittamarkadadde cikin karamin cokali.
Ruwa lita biyu.
Yadda ake hadawa*⤵
Za’a Jika gaba daya kayan hadin a cikin ruwa da daddare ya kwana. Washe gari ayi ta shan sa a matsayin ruwa.
Ayi ta maimaita hakan har sai an samu yadda ake so.
Allah ta'ala yasa mudace.
0 Comments