HUKUNCIN WANDA MATARSA TAYI MASA ISTIMNA'I :


HUKUNCIN WANDA MATARSA TAYI MASA ISTIMNA'I :

TAMBAYA TA 3114
********************
Assalamu alaikum malam, idan matar mutum ta biya masa bukatar sha'awarsa ta hanyar amfani da hannunta ko bakinta, shima istimina'i ne? Kuma shima akwai laifi agun Allah?? 

(DAGA L. M HASHIM).

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu. 

Addinin Musulunci ya yarda mutum yayi duk wani wasa da matarsa ko lokacin da take cikin tsarki, ko alokacin da bazai yiwu ya sadu da ita ba, sanadiyyar jinin haila ko biqi ko wata larurar. 

Kuma don mutum yayi inzali a irin wannan yanayin babu wani laifi akansa. Mutum dai bai sadu da ita ta dubura ba, ko acikin jinin haila. 

Game da sanya al'aura a baki kuwa, akwai sabani atsakanin Malamai. Yayin da wasu maluman suke ganin haramcin hakan, wasu kuma sun ce ya halatta. 

Wadanda suka ce bai halatta ba, sun kafa hujjah ne da cewar shi bakin dan Adam an halicceshi ne domin cin abinci ko shan abin sha, ko ambaton Allah. Amma ba'a yishi domin ya zama kafar saduwa atsakanin Ma'aurata ba. 

Kuma sun ce alokacin da ma'aurata ke tsotsar al'aurar junansu, lallai ne sai an samu fitar maziyyi wanda shi babu sabani atsakanin maluma bisa cewar najasa ne, hukuncinsa daya da fitsari. Kuma haramun ne musulmi ya hadiye najasa..

Hujjarsu ta uku kuma sun ce shi dai matse-matsin dan Adam ko kuma al'aurarsa waje ne da ya zamto matattarar kwayoyin chututtuka. Shi kuma bakin dan Adam yakan zamto kamar mashigar chutuka ayawancin lokuta idan aka aiwatar dashi ba bisa Qa'idah ba. Kuma sau da yawa ana samun fitar kuraje da sauran chutuka acikin bakuna ko harasan ma'auratan dake aikata wannan. Kuma yazo acikin mashahurin hadisi cewa "BABU CHUTA KUMA BABU CHUTARWA".

Wato kada ka chuci wani, kuma kada kada ka jefa kanka cikin abinda zaka chutu. 

Maluman dake ganin halascin tsotsar al'aura atsakanin Ma'aurata, sun kafa hujjah da cewa ai Allah da Annabinsa bai haramta yin haka acikin Alqur'ani ko hadisi ba, Kuma duk abinda ya zamto haramun ne an riga anyi bayaninsa acikin Alqur'ani da Sunnah kamar yadda muka bayyana abaya...

Kuma sun kafa hujjar cewa ya halatta Ma'aurata su aikata duk wani abinda zai Qara musu nishadi yayin saduwarsu mutukar dai Allah bai haramtashi ba. 

Don haka idan ma'aurata suka yi wasa da juna har yakai ga an samu inzali, wato fitar maniyyi, ba haramun bane. Abinda aka haramta shine mutum ya aikata hakan kansa da kansa. 

WALLAHU A'ALAM. 

Hatimu Abdullahi Ggn

Post a Comment

0 Comments