HANYOYI 10 NA RABUWA DA TOILET INFECTION:
Wannan sunan da MATA suka fi sanin shi da shi kenan, harma da wasu mazan, amma a fannin lafiya iya abin da aka gano to hanyar bincike to shine sunan ciwon.
(1)IBADA: MACE ta zamo me Ibadah sosai da ambaton Allah.
(2) TSAFTA: Idan za kiyi tsarki ko na Bawali ko na ga'iďi ki wanke Hannun ki da sabulu kafin kiyi, kula da tsaftar panties sosai da sosai, idan za'a fita a dinga sanya pant, da Dare a huta, sauya PAD Lokacin period kan Lokaci a dinga amfani da panties da suka dace, ki iya tsarki yanda ya dace da tsaftar wurin, ki ki nisanci madigo ko bin maza don har CANCER zaki iya samu.
(3) ABIN DA ZAI SHIGA QOFAR: Ba komai Hatta Hannun ki, balle ki cusa wani abu, duk wani wankewa da moisturising iya wajen qofar ake yinsa (Outside Viginal opening), ba ruwan ki da ciki, me AURE ta tsaya ga mijinta kaďai, kuma ta koya masa tsafta sosai da kula da lafiya, da gujewa duk abin da zai iya jawo ciwo idan bashi da sani ko Ilimin hakan.
(4) SHAN RUWA DA ABINCI: ki guji cin Abin da zai dinga Illata wurin, ko zama ba shan Ruwa yanda ya kamata wannan duk illa ne( idan da hali ki yawaita shan fruits).
(5) MOTSA JIKI DA RAGE SHAN MUGUN SANYI: suna taimakawa sosai domin suna sanya jini ya zaga ko ina na jiki, kuma hakan yana qarawa ko ina na jiki lafiya bama wurin kaďai ba.
(6) ZIYARTAR LIKITA ME INGANCI: kije kiga Gynecologist qwararre ya dora ki kan magani, kuma kisha tare da bin dukkan DOKA (Ga me Aure tasha da mijinta, me Abokiyar zama su sha dukkan su).
(7) ME AURE TA KIYAYE: Oral sex, fingering anything that is not mean for that opening should be avoided. LUBRICATING ga mata masu matsalar Dryness saboda wasu cutukan JIKI ko rashin Abinci me kyau ku lura da kyau da "Shin menene wannan abin da za ayi amfani da shi??? Tsaftar sa, me ya qunsa? da sauransu, make sure it's something that is safe, wanda bazai yi irritating ko disrupting din wurin ba.
(8) SITH BATH: sitbath wani abu ne me kyau ga mace da lafiyar ta, amma duk wanda za kiyi kiyi me inganci sosai da tsafta.
(9) MAGANIN MATA: wallahi kisan me kike sha kar ki jawowa kanki daukewar ni'ima da wargajewar sinadaran jiki balle ya kasa aiki yanda ya dace, Naji ance har yanzu wasu suna kwabe-kwabe su cusa, kuma suje ga miji hakanan....sannu DOSORUWA.
(10)KIYAYE DAMSHI: ki samu paper towel na tsane Jikin ki duk sanda kika gama Ďahara, ko towel wanda kika yarda da shi, kar ki yarda ki jinkirta Ďahara me kyau bayan kin tara da miji (Me aure), shawara ta qarshe idan kina da hali da iko ki dinga amfani da PROBIOTIC supplement, idan babu ki dinga yawan amfani da fruits ko kaďan ne iya wanda zaki iya, saboda yana daidaita tsakanin qwayoyin cuta na Gaban mace da Hanjinta na bayan Gida.
Don Allah ki gwada sauya LIFESTYLE dinki xuwa haka ke me fama da ciwon kisha mamaki bayan wasu watanni cikin ikon Allah.
Allah ya qare mu da Lafiya. Ameeen.
Zoohrah Oummu Deederht ✍
0 Comments