Shirin Abincin Sallah Na Musamman:




Shirin Abincin Sallah Na Musamman:

by Bilkisu Tijjani 


Abincin sallah mu hausawa muna abincin sallah kamar tuwo, masa ko sinasir, da dan soye soye haka, sai abinsha.

Uwargida yakamata ki tanadi abincin sallah kamar kala biyu zuwa uku akalla saboda ki burge maigida, wani maigida yana kawo abokansa su ci abincin sallah sannan kuma zaki yi zumunci dashi, wato zaki kaiwa makotanki, da iyayenki da iyayen mijinki.


Kila zaki samu baki wadanda za su zo muku barka da sallah kamar abokan mijinki da dai sauransu.


Misalin abincin da za ki yi na sallah:

Tuwon shinkafa miyar Taushe za ki iya hadawa da fried rice wato suyayyar shinkafa, sai ki hada da masa ko Sinasir, sannan kidan yi dan wani abun sha haka kamar zobo ko kunun zaki ko kuma lemon kayan marmari, sai namanki zaki iya yin soyayyar kaza sai a dora akan fried rice.

 
Yadda Uwargidan za ta tsara girkinki saboda ki gama da wuri kafin maigida ya dawo daga idi ko kuma kafin a fita idi har kisamu damar tafiya idi idan kina so.

Daren sallah za kiyi kokari ki tafasa namanki, sai kisa shi a firij kinsan soyashi ya rage, sannan miyar tuwanki zaki iya yinta tun ana gobe sallah da yamma sai ki sata a firij kisan kingama da miyar dimamanta ya rage idan kika tashi da safe, kina tashi sai ki dora tuwanki sannan ki dora suyar namanki idan kika gama soyawa sai ki dora dimaman miyarki idan tayi sai ki sa a cooler. Sai masar ko sinasir dama kinjika sjikafarki sai ki kaita nika Kafin ki kai sai ki dora shinkafar da zakisa a ciki bayan kindawo daga kai nika sa zafin nikan sai ki yanka albasa kisa yeas da suga da gishiri sannan ki dakko wannan shinkafar taki idan ta dahu sai ki zubata amma ki barta da dan ruwa ruwa ki zubata da zafi saboda tayi saurin tashi sai ki rufeta ki bata kamar awa daya haka sannan ta tashi sai ki fara gasata

Da asuba ki yi kokarin tashi da wuri kamar 4: haka zaki iya dora tukunyar tuwanki a murhu daya kafin ruwan ya tafasa sai ki jika shinkafar saboda tuwanki yayi kyau da fari, daya kuma ki dora ruwan shinkafar da zakiyi freid rice ki zuba shinkafar su tafaso tare kafin shinkafar ta tafasa kin yayyanka kayan su karas da albasa, tana tafasa sai ki wanke ta ki barta a kwando ki dora tukunyar da za kiyi a ciki kisa mata mai dai dai yadda kikaga zai isa kafin man yayi zafi sai ki masa idan man yayi zafi sai ki soya green fils da Karas da albasa, magi, gishiri kuri sannan ki zuba shinkafar ki juyasu ko ina sannan ki soya sama sama sai ki dakko ruwan naman da kika tafasa wanda zaki soya sai ki zuba mata ta karasa dahuwa yadda zata yi dadi sannan a gefe ruwan tuwanki yayi kin zuba shinkafar tuwon kinayi kina dubawa. Kafin su dahu sai ki hada salad din da za,aci freid rice din dashi shima idan kingama zaki iya sashi a firij saboda kar ya saki ruwa kafin azo ci. Zobo shima zaki iya hadashi tun ana gobe sallah kisa a firij. Idan tuwunki yayi sai ki kwasheshi. Sai pepper chicken shima ki jajjaga Tattasanki da dan taruhu ki soyasu ki hada shikenan kingama sai ki gyara kitchen dinki ki rufe shi.

Post a Comment

0 Comments