Mafi yawancinmu har yanzu muna zubar da bawon lemu bayan mun gama cin ’ya’yan itacen, muna tunanin cewa ba za a iya cin shiba ko kuma zai iya cutar da lafiyarmu. Sai dai bawon lemu na kunshe da sinadirai da dama wadanda ke sa shi amfani ga lafiya da walwalar jiki.
AMFANIN BAWON LEMO.
Kasancewar bawon lemo yana dauke da vitamin C, fiber, da adadi mai yawa na polyphenol Compounds a cikin bawon lemu suna ba da babbar fa'ida ga lafiyar jiki da walwala.
Wasu daga cikin amfanin bawon lemu sun haɗa da:
■ Kula da lafiyar zuciya da rage matakin cholesterol na jini.
■ Rage hawan jini.
■ Daidaita motsin ya'yan hanji da samun kariya daga Cushewar ciki.
■ Samun kariya daga wasu nau'ikan ciwon daji.
■ Karfafa garkuwar jiki da bashi kariya daga cututtuka daban-daban.
■ Rage matakan kumburi a cikin jiki.
■ Kula da matakin sukarin jini.
■ Yana taimakawa wajen ragewa da daidaita kiba.
Shin za'a iya cin bawon lemu?
Yana yiwuwa a ci bawon lemu ta hanyar taunawa kai tsaye, amma ana bada shawarar a ci shi kadan a lokaci guda don guje wa kamuwa da ciwon ciki.
Anan ga wasu hanyoyin cin bawon lemu wanda zai iya rage ɗanɗanonsa mai ɗaci, wanda yawancin mutane basa son shi.
A yayyanka bawon lemu sannan a yi amfani da shi a matsayin abunda zai kara dandano a cikin shayi, ruwa, ko sauran abubuwan sha.
Yin abun sha (juice) na bawon lemu. Hakanan kuma ana iya ƙara shi a cikin nau'ikan abun sha daban-daban na dabi'a.
Daga ƙarshe, bawon lemu yana ɗauke da kaso mai yawa na wasu nutrients, mafi mahimmancin daga cikin su sune vitamin C, Calcium, potassium, da dietary fiber, bugu da kari yana dauke da wadataccen antioxidant Compounds.
Mutum na iya cin bawon lemu ta hanyar tauna su kamar yadda suke ko ƙara su a cikin abinci iri daban-daban.
Duk da haka, ya kamata mutum ya guji cin bawon lemu da yawa kuma a tabbatar da an wanke shi sosai kafin amfani dashi, saboda hakan yana rage haɗarinsa da kuma cutarwar sa.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments