Yadda zaku magance stomach ulcers wato gyambon ciki da abin sha na kabeji.
Ana daukar ruwan kabeji daya daga cikin abubuwan sha masu ban mamaki da ake amfani da su don magance gyambon ciki, kuma hakan yana faruwa ne saboda dalilai masu yawa, ciki har da:
■ Kabeji yana da wadata a cikin glutamine, wato wani amino acid ne wanda zai iya taimakawa wajen ciyarwa da kuma gyara bangon da ke cikin sashin narkewar abinci wanda ulcer tayi sanadin lalacewar sa.
■ Kabeji yana taimakawa wajen haɓaka gudanar jini zuwa bangon ciki, wanda hakan na iya taimakawa wajen samun saurin warkarwar sa.
■ Kabeji tushe ne mai kyau na samar da vitamin C wanda ke da amfani wajen yakar kwayoyin cutar Helicobacter pylori Infections.
Ana iya shirya abun sha na Kabeji don a yi amfani da shi wajen magance gyambon ciki a gida ta hanyoyi kamar haka:
● Abu na farko shine a samo kabeji madaidaici a raba shi gida buyi ayi amfani da rabin.
● Sannan a yayyanka shi.
● Sannan a zuba wannan yankakken kabejin a cikin blender.
● Sai kuma a ƙara da ruwa madaidaici
● Sai ayi blending din shi na ɗan wani lokaci har sai ya markadu sosai.
● Ana shan wannan abin sha kafin cin kowanne abinci.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
Masu Fama da gyambon ciki, Allah Ka ba su lafiya suyi “Azumi” cikin ƙoshin lafiya.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments