Bayani game da ruwan rake.
1. Yana taimakawa wajen karfafa hanta sannan kuma yana daya daga cikin maganin shawara.
Ruwan rake yana dauke da sinadarin ‘Antioxidants’ yana kuma taimakawa wajen kare hanta daga kamuwa da cuta.
2. Tunda ruwan rake yana dauke da diuretic, yana taimakawa wajen kawar da guba daga jiki da wasu cututtukan.
kuma shan shi akai-akai yana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar yoyon fitsari da kuma kawar da zafin lokacin fitsari.
3. Yana bada kariya daga samun ciwon ciki, sannan yana da kyau wajen magance constipation.
4. Shan ruwan rake a kai a kai yana taimakawa wajen Ƙarfafa garkuwar jiki.
5. Akwai ma'adanai da yawa da ake samu a cikin ruwan rake, kamar su calcium, magnesium, phosphorus, iron da potassium, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ƙasusuwa.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments