Raunin Al'aura a cikin mazan da shekarunsu suka ja matsala ce da ta zama ruwan dare mai gama duniya, don haka ana ba da shawarar mutum yayi amfani da lafiyayyen abinci mai kyau kafin ta kaiga ya fara rasa ƙarfin jima'in sa.
Akwai tsirrai da dama da ake amfani dasu don karfafa karfin mazakuta da magance saurin inzali wandanda ke taimakawa maza wajen samun gamsuwa yayin jima'i.
Sune masu zuwa kamar haka:
■ Amfanin kankana domin magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
Kankana tana dauke da kaso mai yawa na amino acid wato L-citrulline.
Lokacin da mutum ya sha L-citrulline, jiki yana canza shi zuwa amino acid arginine.
Shi kuma arginine yana haɓaka matakin nitrogen oxide, wanda ke taimakawa wajen ƙarfafa karfin al'aura da kuma inganta matakin testosterone wanda ke kara lafiyar jima'i.
■ Amfanin Beetroot don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
Beetroot yana ɗaya daga cikin abinci mai muhimmanci dake taimakawa maza masu fama da raunin al'aura, kamar yadda Beetroot ke aiki iri daya da Viagra.
Viagra yana ƙara matakan nitrogen oxide, wanda ke faɗaɗa hanyoyin jini sannan kuma yana ƙara kwaranyar jini zuwa al'aurar dan Adam (Tashin gaban dan Adam na bukatar kwararar jinin sosai).
Beetroot yana ƙunshe da kaso mai yawa na nitrogen na dabi'a, kamar yadda nitrogen idan ya shiga cikin ciki ke sauyawa zuwa nitrogen oxide, shi kuma nitrogen oxide yana faɗaɗa hanyoyin jini da kwararar jini, kamar yadda Viagra ke aiki.
Akwai wasu karin kayan lambu da yawa waɗanda suma suna da yawan nitrogen acikin su kamar su karas, radishes, seleri, salak, da sauransu, amma Beetroot shi ke dauke da kaso mafi yawa na nitrogen.
■ Amfanin jirjir don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
An yi amfani da jirjir a shekarun da suka gabata don magance cututtukan zuciya da jijiyoyin jini, saboda yana dauke da kaso mai yawa na nitrogen.
Sannan kuma daga baya an gano cewa yana iya taimakawa wajen inganta karfin jima'i.
Yana kara yawan sha'awar jima'i, sannan kuma akwai yiwuwar za'a iya amfani da shi a matsayin abunda zai kara karfin jima'i, da magance saurin inzali da raunin mazakuta.
■ Maganin saurin inzali da kubewa
Ana daukar kubewa a matsayin abunda zai iya zama ya inganta karfin maza mai kyau don samun inganta ayyukan jima'i.
Sannan kuma hanya ce mai kyau don magance saurin inzali da kuma rashin karfin mazakuta.
Ana amfani da kubewa ta hanyar shan 5_10 grams na garin ya'yan kubewa tare da kofi ɗaya na madara
■ Magance saurin inzali da tafarnuwa.
Tafarnuwa na da amfani wajen magance matsalolin raunin al'aura, kuma galibi ana kiranta da "poor man's Penicillin" domin tana aiki a matsayin abu mai kashe kwayoyin cuta, da kara karfin garkuwar jiki.
Magance saurin inzali da tafarnuwa hanya ce mai arha ga masu karancin hali sannan kuma tana da saukin samuwa. Har ila yau tana rage matsalar rashin karfin mazakuta ba tare da haifar da illa kamar sauran magunguna da muke siya a kasuwa masu illa masu da hadari ba.
Hanyar magance saurin inzali da tafarnuwa ta hada da tauna tafarnuwa guda biyu zuwa uku a kullum, Wannan yana taimakawa sosai wajen samar da lafiyayyen maniyyi.
■ Amfanin citta don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
Ruwan da aka ciro daga jikin citta yana aiki a matsayin aphrodisiac wato abinci dake kara sha'awar sannan kuma yana da amfani wajen magance matsalar raunin al'aura.
Ana amfani da citta ta hanyar shan rabin teaspoon na ruwan citta tare da rabin dafaffen kwai da zuma
Ana shan wannan hadin sau daya a kowace rana da daddare har na tsawon wata guda, sannan kuma ana iya hada maganin saurin inzali na tafarnuwa tare da na citta domin samun sakamako mai kyau.
Wannan hadin yana aiki don kawar da matsalar raunin al'aura da magance saurin inzali.
■ Amfanin Albasa don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta
Albasa tana taimakawa wajen motsa sha'awar jima'i.
Domin amfanar albasa sai a samu farar albasa, a cire bawon, a yanka, sannan a soya a cikin man shanu
Ana iya shan wannan hadin a kullum tare da zuma cokali guda, amma wannan hadin ana shan shi a cikin da babu komai a cikin sa (empty stomach) na akalla awa biyu.
Wannan maganin yana taimakawa wajen magance matsalar saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
■ Amfanin Karas don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
Karas na da amfani wajen magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta.
Don amfana daga karas, sai a dafa yankakken karas gram 150, dafaffen kwai rabi, da zuma cokali daya
Ana shan wannan hadin sau ɗaya kowace rana na tsawon wata ɗaya ko biyu
yana kara karfin jima'i, don haka mutanen da suke fama da matsalolin jima'i za su iya amfana da wannan hadin.
♤ Amfanin dabino don magance matsalolin saurin inzali da kuma rashin karfin mazakuta.
Dabino abinci ne mai kunshe da fa'idodi da yawa kuma yana da amfani wajen dawo da karfin jima'i, kara karfin jiki, da kara kuzari.
Ana iya cin kimanin gram 100 na dabino a kowace rana don samun sakamako mai kyau.
Za'a iya karawa da zabib don magance saurin inzali da rashin karfin mazakuta
Masu ilimin tsirrai na dabi'a suna ba da shawarar ayi amfani da bakin zabib don samun waraka akan abubuwan da suka shafi jima'i.
Don samun mafita ga mutanen dake fama da matsaloli:
■ Raunin Al'aura da saurin inzali.
■ Matsalolin istimna'i.
■ Sabbin Angwaye.
■ Kimtsa mata sabbin Aure.
■ Matsalolin Rashin ni'ima da rashin gamsar da maigida.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments