MAGANIN ZAZZAƁIN MALARIA.
Ga wasu daga ganyayyakin bishiyoyi da ake amfani da su domin magance Malaria.
1. Ganyen Gwanda.
Ganyen Gwanda sananne ne sosai wajen magance Malaria saboda yana da 'Anti Malarial Properties'.
A wanke ganyen Gwanda guda ɗaya, sai a tafasa, mai fama da zazzaɓin Malaria ya sha ruwan. A maimaita gwargwadon yadda mai lalurar ya samu sauƙi.
2. Ganyen Darbejiya.
Ganyen Darbejiya masana sun tabbatar yana ɗauke da isassun sinadarai da ke yaƙi da ƙwayar cutar Malaria.
Ana iya dafawa mai zazzaɓin Malaria ganyen darbejiya ya sha saidai banda mace mai ƙaramin ciki saboda shi 'abortificient' ne sannan banda masu ciwon hanta da sauran waɗanda jikinsu ba ya buƙatar abu mai ɗaci.
3. Lemon Grass.
Lemon grass na ɗauke da sinadaran ƙara lafiya da yaƙi da cututtuka, ciki har da Malaria. Ana haɗawa da Lemon grass acikin magungunan cututtuka kala-kala saboda irin amfaninta wajen taimakon lafiya.
4. Shuwaka.
Dafa shuwaka a yi amfani da ruwanta na magancewa da kuma zama rigakafin zazzaɓin Malaria. Saidai itama tana da ɗaci, mata masu ƙaramin ciki da kuma mutanen da jikinsu ba ya son abu mai ɗaci ba za su sha ba.
5- Ganyen goba.
Shi ma ana tafasa kamar ganye goma, a sha ruwan domin magance zazzaɓin Malaria.
Amma a sani, Malaria tana iya zama babbar cuta wacce ta ke taɓawa mutum ƙwaƙwalwa tana ma kaiwa a rasa mutum gaba ɗaya. Don haka idan aka jarraba shan maganin Malaria a gida ba a warke ba to a tafi asibiti, kada a bari ciwon yai tsanani sosai.
Idan kuna bukatar sanin amfanin wani magani ko abinci ko sanin yadda ake haɗa maganin wata cuta sai ku yi magana a comment, za mu kawo muku insha Allahu.
Daga shafin Bashir Halilu.
0 Comments