TAMBAYA DAGA MEMBER
Asslm Dan Allah doctor abani mafita kullum mijina yanaman gori akan banida ni,ima sbd duk lkcn daxamuyi Sunnah sai yashafa mai nafadamasa mtsln tashice SBD baya iya tsayawa muyi wasa kodana minti biyarne abun yanadamuna shekara biyu da aure ban tabajin dad in abunba kuma Dan wulakancima inyatashi shafaman man gyada yakesawa wlh duk lkcn dayaxo said inji nattsaneshi
AMSA
Hakika rashin yin wasannin motsa sha'awa zai iya zamowa babbar matsalar saduwa ga ma'aurata. Rashin yinsa yana haifar da bushewa kandas ga al'aurarku ke da mijinki gaba dayanku. Don haka akwai bukatar kiyi magana ta fahimta dashi, saboda ya canza yadda yake fuskantarki. Sa'annan idan shi baiyi miki wasannin ba, to, kina iya yimasa, domin samun maslaha.
Game da yin amfani da man gyada da yakeyi kuwa, a kwai yiwuwar ya haddasa muku kamuwa da cututtukan infection, musamman saboda ba'a yishi domin samarda santsi ba. Sa'annan zai iya zamowa ya canza yanayin al'aurar ki (vaginal pH balance), wanda shima zai samarda yanayi mai kyau ga hayayyafar kwayoyin cuta. Zai kuma iya haifar da kuraje, kaikayi, sulbewar fata, tareda jin zafin jima'i.
WalLahu A'lam.
0 Comments