Za'afaran wani sinadarin girki ne da aka samu daga furen saffron crocus (Crocus sativus L.) wanda ake neman sa sosai saboda saboda amfanin sa ta bangaren magani da amfaninsa wajen dafa abinci.
Saboda shaharar za'afaran da kuma dawainiyar da ake masa yayin shuka da girbar wannan sinadarin girki, yana da tsada sosai.
A halin yanzu ana ɗaukar za'afaran a matsayin sinadarin girki mafi tsada a duniya.
Ana jin daɗin za'afaran a sassa da yawa na duniya kuma shine tushen abinci a Indiya, Gabas ta Tsakiya, da Bahar Rum.
Shi wannan sinadarin girki yana da Kamshin da ɗanɗanon ƙasa, da kuma launi ja mai haske saboda yawan abubuwan da take tattare dashi na tsirrai, kamar su carotenoids crocin da crocetin.
Wadannan dama wasu abubuwan da aka samu a cikin za'afaran suna da kaddarorin inganta lafiya, kuma bincike ya nuna cewa amfani da za'afaran na iya amfanar lafiya ta hanyoyi da dama.
Yana ƙunshe da Anti-inflammatory da Antioxidant masu karfi.
Za'afaran yana da wadata a cikin abubuwa masu dauke da anti-inflammatory da antioxidant, wanda suka kunshi carotenoids kamar crocin, crocetin, da picrocrocin, da kuma terpenes kamar safranal, waɗanda sune manyan mahadi na bioactive da ake samu a cikin za'afaran.
Crocitin, crocin, picrocrocin, da safranal an gano su suna da tasirin antioxidant da anti-inflammatory.
Wani bincike ya nuna cewa shan za'afaran akai-akai da kuma shan supplement na za'afaran na iya taimakawa wajen rage kumburi da ƙananan abubuwan daka haifar da oxidative stress.
Oxidative stress yanayi ne da yake faruwa lokacin da aka samu rashin daidaituwa tsakanin masu samar da reactivate oxygen species (ROS) da antioxidant defenses a cikin jiki, wanda zai iya haifar da lalacewar kwayoyin halitta.
Wani binciken da ya hada da mutane 80 da ke dauke da ciwon type 2 diebetes an gano cewa mahalartan wadanda sukayi amfani da 100 milligrams na supplement na za'afaran a kowace rana na tsawon makonni 12 sun sami raguwa mai yawa a cikin matakan jini na malondialdehyde (MDA) da alamun oxidative stress.
Zai Iya Inganta Barci
Bincike ya nuna cewa abubuwa masu aiki da ake samu a cikin za'afaran suna da kaddarorin da ke haifar da barci kuma suna iya taka rawa mai amfani akan samun ingancin barci da daukar tsawon lokaci ana barci.
Wata bita ta baya-bayan nan wanda take kunshe da bincike biyar da mahalarta 379 sun gano cewa jiyya da ake da za'afaran ko kuma sinadaransa masu aiki, kamar su crocin, suna taimakawa wajen samun ingancin bacci da tsawon lokacin bacci.
Masu binciken sun ba da shawarar cewa za'afaran na iya taimakawa wajen inganta barci ta hanyar haɓaka matakin hormone din dake daidaita barci wato melatonin da kuma yin aiki akan wasu receptors a cikin kwakwalwa don haɓaka ingancin barci.
Duk da samun waɗannan sakamakon masu ban sha'awa, bincike yana da iyaka, kuma ana buƙatar ƙarin bincike game da tasirin saffron akan barci.
Zai Iya Amfanar da Lafiyar Kwakwalwa
Za'afaran magani ne na dabi'a don magance cututtukan tabin hankali, gami da damuwa.
Nazarin bincike 23 ya gano cewa, za'afaran yana da tasiri mai karfi akan alamun tashin bakin ciki da damuwa.
Har ila yau, masu nazarin sun lura cewa za'afaran yana da makamancin wannan tasiri akan alamun kunci kamar magungunan antidepressant.
Masu binciken suna tunanin wasu abubuwa a cikin za'afaran, irin su crocin da safranal, suna inganta alamun damuwa da bakin ciki ta hanyar hana sake dawowa da ƙwayoyin cuta masu haɓaka yanayi kamar dopamine, norepinephrine, da serotonin. Wannan zai ƙara matakan waɗannan sinadarai masu saka jin daɗi a cikin kwakwalwa
Zai Iya Amfanar Wasu daga cikin matsalolin Ido
Wani nazarin bincike ya nuna cewa za'afaran na iya amfanar mutanen da ke da matsalolin da suka shafi idanu, Age-related macular degeneration (AMD), cututtukan ido wanda a halin yanzu ke haifar da asarar gani a cikin tsofaffi.
Supplement na za'afaran an gano cewa yana Inganta gani ga mutanen da ke da AMD da kuma mutanen da ke da diebetes maculopathy, wata matsala mai alaka da ciwon sukari.
An kuma nuna cewa supplement na za'afaran yana rage pressure a ido ga masu fama da cutar glaucoma, yanayin da ke tattare da karuwar pressure a cikin ido, wanda ke lalata jijiyar gani kuma yana haifar da asarar gani.
Tunda mafi yawancin cututtukan ido suna samuwa ne ta hanyar girman kumburi, anti-inflammatory da antioxidant da aka samu a cikin za'afaran na iya taimakawa wajen rage kumburi a cikin ido.
Zai Iya Kara Lafiyar Zuciya
Saboda kasancewar sa yana da tasirin anti-inflammatory da antioxidant, ƙara shi a matsayin sinadarin girki a cikin abincin ku na iya taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya da jijiyoyin jini.
Ayyukan za'afaran sun nuna cewa yana da tasiri wajen rage hatsarin wasu cututtukan zuciya, irin su hawan jini, sukarin jini, da cholesterol.
Abubuwan gina jiki dake tattare a za'afaran
Za'afaran yawanci ana amfani da adadi kankani wanda ba shi bane muhimmin tushen yawancin vitamin da minerals.
Haka kuma, nau'in za'afaran na yau da kullun shine tushe mai inganci na ma'adinai na manganese kuma yana ɗauke da ƙaramin adadi na vitamin C.
Amfani da babban cokali 2 na za'afaran na kunshe da;
• Calories: 13
• Fat: 0.25 grams (g)
• Carbohydrates: 2.74 g
• Fiber: 0.16 g
• Protein: 0.48 g
• Vitamin C: 3.4 milligrams (mg)
• Manganese: 1.19 mg
Hadarin dake tattare da za'afaran
Yayin amfani dashi a cikin adadin al'ada, kamar lokacin amfani da za'afaran a matsayin sinadarin girki a dafa abinci, ana ɗaukar za'afaran gabaɗayan sa daidai ne.
Hakanan ana ɗaukar shan supplement na za'afaran shima daidai, amma idan aka ɗauki shi a cikin adadi mai yawa, za'afaran na iya haifar da ƙananan illoli kamar jiri, gajiya, bushewar baki, damuwa, tashin zuciya, da ciwon kai ga wasu mutanen.
Wani bincike ya ba da rahoton cewa amfani da supplement har zuwa 100 MG na za'afaran a kowace rana har zuwa makonni 26 yana da aminci kuma ba shida alaka da wani abu mai cutarwa.
Duk da haka, shan supplement na za'afaran na tsawon fiye da makonni 26 ko amfani da fiye da gram biyar na za'afaran a kowace rana zai iya haifar da mummunan sakamako, kamar zawo na jini da amai.
Babu isassun hujjoji don tallafawa amincin shan za'afaran mai yawa ga masu ciki.
Mutanen da ke da juna biyu ko masu shayarwa yakamata su guje wa shan za'afaran mai yawa.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments