AMFANIN NAMAN KYANKYASO WAJEN ƘARAWA MUTANE LAFIYA.


AMFANIN NAMAN KYANKYASO WAJEN ƘARAWA MUTANE LAFIYA. 

Masana sun gano amfanin cin naman Kyankyaso da kuma shan nonon Kyankyaso wanda mutane da dama ba su sani ba. 

 Masanan su ka ce, ruwan dake jikin Kyankyaso ya fi nonon saniya amfani domin yana dauke da sinadaran gina jiki da dama wanda suka hada da 'sugar' da kuma sinadarin ‘fats’ mai sa ƙiba da kuma ‘protain’ mai gina jiki da kara lafiya kamar yadda wani bincike na gidan talabijin na CNN ya nuna.

Banda ma amfanin ruwan na Kyankyaso, shi kansa Kyankyason na da matukar zaƙi sannan kuma ga amfani ga lafiyar jiki, domin dadin naman Kyankyaso kamar abin kwalamar nan na ‘Ice cream’ ne, in ji masu binciken. 

"Ruwan kyankyaso dai yana gina jiki matuka" Inji wani masani Leonard Chavas da yayi bincike a kai.

Ya ce "Nonon matar Kyankyaso har ta kai ma ya fi nonon saniya kara karfi da kara lafiya a jikin mutum kwarai da gaske. 

  A sauran kasashe dai kamar irinsu China ana kokarin ganin yadda za a rika gyara ruwan Kyankyaso domin a maida shi abin kalaci na yau da kullum. 

   Daga shafin Bashir Halilu. 

Post a Comment

0 Comments