AMFANIN AYA A JIKIN ƊAN ADAM.
Daga cikin sinadaran da Aya ke kunshe da su akwai, sinadarin magnesium, calcium, iron, nau'ikan Vitamins daban-daban, protein da sauran su. Wadannan sanadarai da Aya ke da su, na da matukar muhimmanci wajen inganta lafiyarmu.
1. Aya Na Gina Jiki Cikin Gaggawa.
Ana amfani da Aya wajen inganta kiwon lafiya da gina jiki sakamakon yawan sinadarai ma su matukar amfani ga jiki da Aya ke kunshe da su, kamar sinadaran carbohydrate, magnesium, phosphorus, iron, fiber calcium, sodium, copper, iron da kuma zinc.
2. Maganin Matsalolin Ciki.
Aya na da matukar fa'ida wajen maganin matsaloli da kan shafi ciki. Ba don komai aya ke taka wannan muhimmiyar rawa kan matsalolin ciki ba, sai don sakamakon wasu sanadarai da ta ke dauke da su, dake inganta wa tare da magance matsalolin ciki musamman wadanda su ka shafi hanji. Sakamakon haka ta ke taimakawa wajen maganin cushewa da kumburin ciki.
3. Gyaran Jiki.
Gyaran jiki mu na nufin inganta lafiyar jiki da suka hada da gyaran fata, gudanuwar jini, kuzarin jiki da sauran su. Yawan sanadaran gina jiki da Aya ke da su ya sa ake amfani da ita wajen gyaran jiki, sakamakon haka ta ke gyara fata ta koma kamar ta yaro, ke nan ta zama "Mai da tsohuwa yarinya". Baya ga haka ta na karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzarin jiki.
4. Kara Qibar Jiki.
Aya na taimakawa wajen karawa mutum kiba cikin sauki. Domin samun wannan fa'ida sai a samu aya mai kyau, a daka ta, daga nan sai a zuba ta cikin ruwa ta kwana, idan gari ya waye, sai a tace a zuba sikari a shanye. Haka za a juri yi. Cikin yardar Allah ramar da mutum ke fama da ita za ta gushe ba da jimawa ba.
5. Inganta Rayuwar Aure.
Ba shakka bincike ya nuna yadda aya ke inganta rayuwar aure. Idan mu ka ce rayuwar aure, mai karatu zai gane inda mu ka dosa. Dalili anan shine ta na kara dankon soyayyar ma'aurata ta hanyar taimaka mu su wajen gamsar da junansu a lokacin jima'i. Ba don komai ba sai don amfanin ta wajen kara yawan ruwan maniyyi, sannan ta na karawa mata ni'ima da jin dadi yayin saduwar aure.
6. Kara Ruwan Nono Ga Mata.
Aya na da matukar amfani ga mata ma su shayarwa da ke fuskantar rashin ruwan mama. Saboda haka duk mace mai shayarwa dake fama da wannan matsala ta karancin ruwan nono sai ta dimanci amfani da aya.
7. Kara Karfin Garkuwar Jiki.
Aya na da sanadaran dake taimakawa wajen inganta garkuwarmu, kuma mai karatu ya san cewa, duk lokacin da garkuwarka ta zama mai karfi, to a lokacin ne za ta iya yaki da cututtuka da kan kai wa jikinka farmaki. Saboda haka ne ya sa aya ke iya yin fito na fito da kwayoyin cuta da za su iya illata jikin dan adam.
8. Aya ta na inganta lafiyar Ido sannan ta na kare mutum daga kamuwa da cututtukan ido.
9. Aya na samar da maganin tsutsar ciki.
10. Aya na taimakawa wajen daidaita kewayawar jini a jikin bil'adama.
11. Aya na taimakawa wajen narkar da abinci.
12. Ta na kare mutum daga hadarin kamuwa da ciwon mafitsara.
13. Aya na rage wa mutum hadarin kamuwa da ciwon zuciya.
14. Aya na rigakafin kamuwa daga cutar hanta.
15. Hakanan Aya na taimakawa wajen rage kitsen cikin jini marar amfani a jikinmu.
16. Aya na magance matsalolin fata kamar su kezbi, kora, makero, pinpus da sauran su.
17. Aya na taimakawa wajen samun kuzarin jiki.
Daga shafin Bashir Halilu.
0 Comments