AMFANIN NA'ANA'A GA MATA MUSAMMAN MASU CIKI DA SHAYARWA.


AMFANIN NA'ANA'A GA MATA MUSAMMAN MASU CIKI DA SHAYARWA. 

Ana ɗaukar Na'ana'a ɗaya daga cikin tsoffin ganye da ake amfani da su don magani.
An san shi a cikin al'adun mutanen da suka gabata kuma ana yin amfani da shi a matsayin abinda yake ƙara dandano da ƙanshi, kuma tsawon lokaci an yi amfani dashi don magance matsalolin kiwon lafiya da dama.

Mata suna amfani da na'ana'a a nau'i daban daban.
Yakan iya zama a sigar danyen ganyen sa, ko kuma a saka shi a shayi, ko kuma a matsayin man na’a na’a domin samun fa’idojinsa masu yawa, ko kuma a cikin nau’in capsules mai ɗauke da abin da aka ciro daga na'ana'a.

Zamuyi tsokaci ne a kan fa’idar na'ana'a ga mata, masu juna biyu, da masu shayarwa, sannan kuma mu ambaci wasu daga cikin illolinsa.

AMFANIN NA'ANA'A GA MATA.

Daga cikin fa'idoji masu yawa na na'ana'a ga mata sune:

■ RAGE ZAFI YAYIN SHAYARWA 

Yawancin iyaye mata suna fama da ciwon nono saboda shayarwa, musamman ma idan mahaifiyar tana shayarwa ne a karon farko, wanda kan iya sa tsarin shayarwa yazo da zafi.

Na'ana'a yana da damar rage waɗannan raɗaɗin ta hanyar amfani da man na'ana'a a shafa shi kai tsaye a kan fata. Mata suna yin amfani da na'ana'a ta hanyar nau'ika daban-daban, ciki har da danyen man na'ana'a, ko kuma ta hanyar surka man na'ana'a da ruwa.

Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2007 a jami'ar liitanci na kimiyya Tabriz da ke kasar Iran ya tabbatar da cewa ruwan na'ana'a yana samar da sakamako mai kyau wajen hana tsagewar kan mama (nipples) da rage bayyanar digo digon duhu a kansu.

A wani binciken da Iran ta gudanar a shekarar 2014 a jami'ar Shahid Beheshti ta kimiyyar likitanci ya nuna cewa iyayen da suka yin amfani da man na'ana'a bayan kowace shayarwa basa samun zafi a kan mama (nipples) da tsagewar sa.

■ INGANTA LAFIYAR FATA.

Anyi amfani da na'ana'a a shekarun da suka shude a matsayin magani don inganta lafiyar fata ga mata, saboda yana magance cututtukan fata da yawa kamar su kuraje da tabo.
 
Dalilin yin amfani da na'ana'a don inganta lafiyar fata shine saboda yana dauke da antibacterial da antifungal properties. 

Na'ana'a, a gefe guda, yana rage kumburi saboda tasirin sa na sanyaya fata. 

Ganyen na'ana'a yana ƙunshe da kaso mai yawa na salicylic acid da vitamin A.
A don haka yana sarrafa yawan fitar sebum (ruwan maiko na kan fata) sannan kuma yana hana kuraje.

Mata sun dogara da ganyen na'ana'a da mansa don samun menthol da kuma antioxidant na dabi'a da ake samu a cikinsa.

Na'ana'a tana aiki a matsayin abu mai hana fata bushewa, yana saka laushi ga fatar data bushe, sannan kuma yana kare fata daga ƙaiƙayi.

■ AMFANIN NA'ANA'A GA MATA MASU JUNA BIYU. 

Na'ana'a tana taka muhimmiyar rawa a lokacin daukar ciki, saboda yana da kyau ayi amfani da shi don magance wasu matsalolin kiwon lafiya da ke da alaƙa da daukar ciki, sabanin haɗarin da ake samu yayin amfani da wasu magunguna. 

Mafi girman fa'idar na'ana'a ga mata masu juna biyu ana iya samun ta ta hanyar shan shayin na'ana'a.

Sannan kuma wadannan sune muhimman fa'idodin sa ga masu juna biyu.
 

■ Rage kunar zuciya

■ Rage tashin zuciya da amai.

■ Rage ciwon kai mai alaƙa da ciki

■ Saukake matsalolin narkewar abinci yayin daukar ciki. 

Ba mutane da yawa bane sukayi bincike don su nemi bayani kan tasirin na'ana'a wajen rage tashin zuciya da amai a lokacin daukar ciki.
Dalili kuwa shi ne hadarin gwajin ga mata masu juna biyu, amma wani bincike da aka gudanar a shekarar 2013 a jami'ar kimiyyar likitanci ta Mashhad da ke kasar Iran ya nuna sakamako mai kyau da ake amfani da shi man na'ana'a wajen rage tashin zuciya da amai.

Ana ba da shawarar yin taka-tsan-tsan lokacin shan shayin na'ana'a yayin daukar ciki, duk da yawan amincinsa. 

Sannan kuma, shayin na'ana'a da aka yi a gida ba a kayyade yawan adadin na'ana'a ko sauran kayan da aka saka a ciki ba. 
Zai fi kyau a sha kofi daya ko biyu na shayi na'ana'a a rana.

Bai kamata a wuce wannan adadin ba a lokacin daukar ciki.

ILLOLIN SHAYIN NA'ANA'A GA MATA.

Na'ana'a na iya yin hulɗa tare da wasu ganyayyaki ko magunguna. 
Duk da fa'idodi masu yawa na na'ana'a, akwai wasu illolin sa da ake samu ga mata, kamar su:

■ Yana rage tasirin wasu magungunan yayin da kake hulda da na'ana'a lokacin shan su.

■ Yana haifar da kasala ga wasu

■ Yana haifar da ƙunar zuciya idan aka yi amfani da shi da yawa.

■ Yana haifar da damuwa ga fata idan aka yi amfani da adadi mai yawa.

Wasu daga cikin magungunan da idan kana amfani dasu, ya kamata ka gujewa amfani da na'ana'a sune Antacids da Magungunan ulcer. 

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

0 Comments