AMFANIN BISHIYAR DOGON YARO KO TURARE (EUCALYPTUS).
Dogon yaro bishiya ce wacce ke da dimbin amfani ta fannin magani da yawa.
Ya fito ne daga yankin ostiraliya, amma yana girma a yankuna da dama na duniya.
Dogon yaro yana da wuyar narkewa idan an ci shi gaba ɗaya, amma ana iya amfani da ganyensa don yin shayi mai aminci, ko kuma man dake cikin sa mai mahimmanci, ana amfani dashi ta hanyar shaƙa ko kuma shafawa.
● AMFANIN DOGON YARO GA ZUCIYA.
Ganyen dogon yaro tushe ne mai kyau wajen samar da antioxidants, musamman flavonoids, waɗanda ke kare jiki daga oxidative stress da free radical damage.
Mafi yawancin flavonoids da ake samu acikin dogon yaro sun haɗa da:
■Catechins
■Isorhamnet.
■Luteolin.
■Kaempferol
■Phoretin
■Quercetin
Wadannan sinadaran suna taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya da kuma kare ta daga cututtuka.
● AMFANIN DOGON YARO GA MASU FAMA DA MURA
Ana iya amfani da ganyen dogon yaro don kawar da alamun mura da tari a cikin hanyoyi masu zuwa:
■ Rage majina
■Fadada bronchi da bronchioles wato bututun da suke dakon iska zuwa huhu.
■ Samun saukin tari
■Inganta alamun asma.
■ Samar da anti-inflammatory na dabi'a.
Babban bangaren da ke da alhakin waɗannan kaddarorin a cikin ganye shine eucalyptol, kuma wadannan sinadaran ana samun adadin su mai yawa a cikin man ganyen dogon yaro.
Don samun fa’idojin man dogon yaro ga masu mura, ana iya shakar sa ta hanci, ko kuma a shafa shi a ƙirji da makogwaro.
● AMFANIN DOGON YARO GA FATA.
Yin amfani da ganyen dogon yaro su na iya rage bushewar fata, domin yana dauke da sinadarin ceramide, wanda wani nau’in fatty acid ne a cikin fata, yana kuma taimaka masa wajen kare shi daga abubuwan da ke waje ta hanyar samar da Insulating barrier da kuma kara danshin ta.
Mutanen da ke da bushewar fata, dandruff, ko cututtukan fata kamar su psoriasis da kumburi yawanci suna da ƙarancin matakin ceramides.
Har ila yau, ganyen dogon yaro yana ƙunshe da wani sinadari da ake kira macrocarpal A, wanda shine sinadarin da ke taimakawa wajen samar da ceramide.
● AMFANIN DOGON YARO WAJEN RAGE RADADI (pain reliever).
Shakar man dogon yaro na iya rage radadi, saboda yana ƙunshe da kaso mai yawa na anti-inflammatory Compounds, irin su cineole da limonene, waɗanda zasu iya yin aiki a matsayin pain reliever.
Shakar man dogon yaro da aka gauraya a cikin man almond na iya taimakawa sosai wajen rage radadi.
● AMFANIN DOGON YARO WAJEN RAGE DAMUWA.
Dogon yaro na iya taimakawa wajen rage alamun damuwa da bakin ciki, kuma yana inganta kwanciyar hankali, saboda yana dauke da eucalyptol, shi wannan sinadarin yana dauke da anti-anxiety properties.
Man dogon yaro yana rage ayyukan sympathetic nervous system sannan kuma ya inganta aikin parasympathetic nervous system, wanda zai taimaka wajen karawa mutum nutsuwa.
● AMFANIN DOGON YARO GA MASU HAWAN JINI.
Man dogon yaro yana iya taimakawa wajen rage hawan jini wanda ya zama wajibi don rage yiwuwar kamuwa da cututtukan zuciya, saboda yana da tasirin kwantar da hankali, ta hanyar shakar sa.
● AMFANIN DOGON YARO GA HAKORA.
Dogon yaro na iya taimakawa wajen kiyaye lafiyar hakori da kawar da warin baki, kamar yadda ganyen dogon yaro ke dauke da sinadarin ethanol mai yawa da kuma wani sinadarin polyphenol, su kuma wadannan sinadarai suna da alaka da kananan kwayoyin cutar bacteria da ke haifar da rubewar hakori da ciwon dasashi, saboda suna hana taruwar plaque wato dattin dake taruwa saka makon makalewar sauran abinci a kan hakora.
Don haka, ana saka ganyen dogon yaro a wajen wanke baki don inganta amfanin sa.
● AMFANIN DOGON YARO GA MASU FAMA DA KUMBURI.
Dogon yaro yana iya taimakawa wajen magance raunuka da bada kariya daga kamuwa da cutar infection. Man dogon yaron da aka surka shi da wani man yana da anti-inflammatory properties sannan kuma yana taimakawa wajen saurin warkewa.
Haka zalika za'a iya amfani da man dogon yaro don magance ƙananan konuwa ko wasu raunin da za a iya jiyyar su a gida.
● AMFANIN DOGON YARO GA MASU CIWON SUGA.
Dogon yaro na iya taimakawa wajen magance ciwon sukari, saboda yana taka muhimmiyar rawa wajen rage sukarin jini.
Koda yake, dole ne ku tuntuɓi likita kafin amfani da man dogon yaro don rage sukarin jini saboda sukan iya samun rashin jikiwa da magungunan ciwon sukari.
● AMFANIN DOGON YARO GA KASHI.
Ana iya amfani da dogon yaro don kawar da kumburin gabobi da kuma ciwon da ake samu sakamakon yanayi irin su osteoarthritis da rheumatoid arthritis.
Hakanan kuma yana iya zama mai amfani ga mutanen da ke fama da ciwon baya, ko waɗanda suke ke warkewa daga ciwon gabobi.
ILLOLIN DOGON YARO.
Ko da yake akwai fa'idodi masu yawa na dogon yaro, dole ne mutum ya yi taka tsantsan da illolin da zai iya haifarwa,
wanda suka haɗa da:
■ Haifar da damuwa ga fata: Man dogon yaro na iya haifar da damuwa ga fata da kumburi idan aka shafa shi kai tsaye ba tare da an surka shi da wani man ba kamar man zaitun ko man kwakwa, ta yadda surkin zai kasance ya kai kashi 1% zuwa 5% na man dogon yaro bisa ga kashi 95% zuwa 99% na man da za'a surka dashi.
⚠️ Kafin yin amfani da man dogon yaro a fata, ya kamata ku gudanar da gwajin rashin lafiyar a kan ƙaramin yanki na fata kuma ku jira na tsawon sa'o'i 24.
⚠️ Yana da haɗari a sha man dogon yaro a baki kai tsaye saboda yana iya cutarwa.
Alamomin cutarwar man dogon yaro sun haɗa da jin jiri da kuma shakewar numfashi.
Sauran illolin sun haɗa da:
■Zawo.
■Tashin zuciya
■Yin amai.
■Lacewar ciki, Da sauransu.
⚠️ Mata masu juna biyu Ya kamata su guji amfani da dogon yaro a lokacin daukar ciki da shayarwa.
⚠️Hakanan ana ba da shawarar yin hankali yayin amfani da shi ga yara.
⚠️ Man dogon yaro na iya cin karo tare da wasu magunguna, irin su:
■ Magungunan Ciwon sukari.
■ Magungunan yawan cholesterol.
■Magungunan Acid reflux.
■Magungunan cututtukan ƙwaƙwalwa.
YADDA AKE AMFANI DA DOGON YARO.
Ana iya amfani da dogon yaro ta hanyoyi da dama, kamar;
■ Ta hanyar amfani da ganyen shayi da aka yi da garin ganyen dogon yaro.
■ Ana iya diga man dogon yaro s cikin air freshener ko a kaskon turaren wuta.
■ Ana iya saka ganyen dogon yaro a cikin bahon wanka don samun nutsuwa.
■ Ana iya kara man dogon yaro acikin wasu mayukan don shafawa akan fata.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments