AMFANIN KANUNFARI DON INGANTA LAFIYAR JIMA'I.
Mutane sun jima suna amfani da kanunfari na tsawon dubban shekaru a matsayin karin ɗanɗanon abinci da kuma tsaftace numfashi don ya zamo mai daɗi.
Haka kuma an dade ana amfani da shi don magance matsalolin ciwon hakori.
Bugu da kari baya ga amfanin sa ta fannin lafiyar jiki da darajarsa ta bangaren abinci, ana daukar kanunfari daya daga cikin tsiron da ke iya kara yawan fitar da sinadarin testosterone ga maza da mata, wanda ke kara karfin sha'awar jima'i da kuzarin jima'i ga duka jinsi biyun.
Kanunfari kuma yana da ikon inganta wasu daga cikin alamun matsalolin jima'i ga maza.
Amfanin kanunfari wajen inganta lafiyar jima'i.
Daga cikin tsirrai masu fa'idojin magani, an banbance kanunfari da wasu fa'idodi masu yawa na inganta lafiyar jima'i.
Ga fa'idodin masu zuwa kamar haka:
ƘARA KARFIN SHA'AWAR JIMA'I
An jima ana amfani da kanunfari na tsawon shekaru masu yawa don ƙara karfin sha'awar jima'i ga maza a yankin Asiya.
A shekarun da suka gabata, maza sun kasance suna tauna ƴaƴan kanunfari don haɓaka al'amuran da suka shafi jima'i. Wannan na faruwa ne sakamakon aikin dayake wajen inganta karuwar matakan testosterone, wanda ke da alhakin sha'awar jima'i a cikin maza da mata.
Don haka, kanunfari na taimakawa wajen haɓaka sha'awar jima'i da haɓaka ayyukan jima'i.
MAGANCE MATSALOLIN SAURIN INZALI.
Masana da dama sun yi tsokaci kan alfanun da kanunfari ke dashi ga maza masu fama da saurin inzali da wuri, wanda hakan na iya haifar musu da damuwa.
kuma ana kyautata zaton yana daya daga cikin muhimman alfanun da ake samu daga kanunfari shine aikin sa don inganta jima'i.
Zaku iya amfana da man kanunfari domin magance saurin inzali ta hanyar hada cokali daya na man kanunfari a kofi mai dauke da madara da kirfa (cinnamon) a sha kullum akalla na wata daya domin shawo kan matsalar saurin inzali.
Haka kuma zaku iya amfani dashi ta hanyar shafashi akan al'aura don magance saurin inzali.
Ana shafa man kanunfari a al'aurar na tsawon awa daya sannan a wanke shi kafin saduwa.
MAGANCE MATSALOLIN RASHIN KARFIN AL'AURA.
Kanunfari na taimakawa wajen haɓaka gudanuwar jini zuwa ga reproductive organ, sannan kuma tasirin su wajen haɓaka matakan testosterone yana taimakawa wajen magance matsalolin rashin karfin al'aura ga maza.
Yana karfafa matakan testosterone sannan kuma yana kara ƙarfin tashin gaba sannan kuma yana inganta al'amuran da suka shafi jima'i. Dangane da yadda ake amfani da man kanunfari game da rashin karfin al'aura.
Ana shafe al'aura da man kanunfari na tsawon awa daya kafin jima'i, sannan a wanke man kafin a yi jima'i don gujewa jin zafi a gaba yayin saduwa.
ƘARA YAWAN RUWAN MANIYYI.
Kanunfari yana ƙunshe da mafi yawancin vitamin da ake bukata don tsarin samar da maniyyi, kamar vitamin E, wanda yake taimakawa wajen ƙara yawan su.
Kanunfari kuma yana inganta harbawar maniyyi, wanda ke amfanar da mutanen da ke fama da matsalolin infertility.
Bayan vitamin da ake samu a cikin sa, kanunfari kuma yana ɗauke da minerals, protein, da kuma fats da ake bukata don samun lafiyayyen jiki, wanda ke taimakawa wajen inganta lafiyar jiki da dukkan sassan jikin, ciki har da reproductive organ.
YADDA AKE AMFANI DA KANUNFARI DON MAGANCE MATSALOLIN RAUNIN JIMA'I.
Saboda yawan fa'idojin da ake samu a cikin kanunfari don jima'i, mutane suna amfani da shi ta hanyoyi da dama don amfana daga shi, amma dole ne a yi amfani da shi daidai yadda ya kamata.
Ana iya amfani da kanunfari ta hanyoyi kamar haka:
■ Kuna iya amfani da garin kanunfari a shayin ku na safe ko kuma madara ana iya shan su kullum.
■ sannan kuma za a iya amfani da ’ya’yan kanunfari suma a shayi.
■ Garin kanunfari na iya rasa fa’idodinsa da kaddarorinsa cikin sauri, don haka a yi amfani da su cikin ɗan takaitaccen lokaci.
■ za a iya amfani da man kanunfari ta hanyar zuba cokali ɗaya na man kanunfari a cikin kofi guda na madara tare da garin kirfa (cinnamon).
■ Sannan kuma ana zuba man tafarnuwa kadan a madara a rika sha kullum na akalla tsawon wata daya don samun sakamako mai ban sha'awa.
■ Sannan kuma ana iya shafa man kanunfari a al'aura don magance saurin inzali da raunin mazakuta.
⚠️ Ya kamata ku guje wa amfani da man kanunfari idan ɗaya daga cikin ma'aurata yana samun tsananin zafi a yankin al'aura kafin ko bayan yin jima'i.
⚠️ Ya kamata ku kiyaye shafa man kanunfari kai tsaye zuwa yankin al'aura, kamar yadda yake wuri ne mai mahimmanci kuma za'a iya samun jin zafi cikin sauri.
Dole ne a fara amfani da wani man kafin shafa wannan.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments