AMFANIN DABINO A JIKIN ƊAN ADAM.



AMFANIN DABINO A JIKIN ƊAN ADAM. 

Dabino na ɗauke da sinadarai masu matuƙar muhimanci ga lafiya, saboda haka gake da gudummawa mai ƙarfi wajen kyuatata lafiya da kula da ita. 
  Daga cikin amfaninsa:

1. Dabino yana saurin narkar da abinci. 
2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure
 3. Yana taimakawa wajen kara jini
4. Yana taimakawa Ma'aurata maza da mata
5. Yana Maganin Basir Mai sa tsuguno a bayi. 
6. Yana karawa Ido lafiya
7. Yana Rage Nauyin kiba da teba.
8. Yana Maganin Gudawa
9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini
10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun
basira..
11. Yana kariya daga Sihiri
12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun sauqi wajen
haihuwa.
13. Yana kariya daga
 Sihiri.

 YADDA ZA A SARRAFA DABINO DOMIN YIN MAGANI. 

1-Ciwon nono ga matarda ta haihu. 

   Anacin dabino guda 7 asha man tafarnuwa karamin cokali sau 1
arana kwana uku. 

2- DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;
Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh milk) sannan a
saka Zuma a ciki a sha awa daya kafin a kwanta.

3- GA MATA MASU JUNA BIYU
Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan anyi kusan
haihuwa Wannan yana hanawa macce yawan zubar jini lokacin
haihuwa da iznin Allah.

4- GUDAWA
Ana daka garin dabino a saka a ruwan zafi a sha In shaa Allahu yana tsayar da gudawa.

5- SAMUN KUZARI
Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1
da safe da yamma.

6- SAMUN LAFIYAYYAR FATAw
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a shafa a fuska awa
daya sai a wanke fuskar da ruwan ɗimi wannan yana saurin gyara fuska.

7- Bincike ya nuna Yawaita cin dabino na hana kamuwa da ciwon
CANCER ko wacce iri.

MANZON ALLAH
(SAW) YA CE DABINON AJWA YANA MAGANIN
DUKKAN CUTATTUKA KUMA DUK RANAR DA
KACISHI BABU WATA CUTA DA ZA TA SAME KA AWANNAN RANAKO
KUMA SAMMU KO SIHIRI.

Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce
Annabi (saww) Yana
nufin kowanne dabino ba wai sai Ajwa ba (Wallahu A'alam)

Daga shafin Bashir Halilu. 

Post a Comment

0 Comments