YADDA ANGO ZAI GYARA KANSA HAR ZUWA RANAR AURE.
TSARABA ANGO 🍉
Duba da Korafe-Korafen da suke Zuwar Mana Sakamakon Mutum yayi Aure. Sai a wayi Gari Su Tsinci Kansu Cikin Babbar Matsala a daren Angwanci Wanda shine dare Mafi Mahimmanci a Wajen Ango da Amarya, Amma wannan Daren yakan zama Dare mafi Muni ga Amarya da Ango, Ko a wayi Gari a wannan dare ya Zama mafi Shigar da Damuwa a zukatan Mutane biyu (Ango da Amarya) da suka dauki Watanni ko Shekaru suna Farantawa Junansu.
Tin daga Ranar da suka zama masoya guda biyu suna Kokarin Farantawa Junansu, tin daga wannan Ranar da suka Hadu a Matsayin Masoyan Juna. Sai a wayi Gari a Daren Angwanci sun Rasa Duk wannan Farin ciki da yake Lullube dasu a baya. Sakamakon Amarya ta sami Angonta ba yadda ta so ta same shi ba.
Ana Samun Wannan Matsalar, Sakamakon Rashin Samun Biyan Bukatar wannan Amaryar daga wajen Angonta.
Yana iya Faruwa Ango ya shiga dakin Amarya. Bayan Abokanansa sun Raka Shi.
Ana Samun Wannan Matsalar, Sakamakon Rashin Samun Biyan Bukatar wannan Amaryar daga wajen Angonta.
Yana iya Faruwa Ango ya shiga dakin Amarya.
Bayan Abokanansa sun Raka Shi. Idan sun tafi sun Barshi. Sai ya kasa yiwa Amarya komi, Zaiji Kamar Ma ba Namiji ba. Gabansa ya kasa ko Motsawa ko kuma ya wayi Gari Bashi da Wadataccen Ruwan Maniyyi Wanda hakan zai Iya kaishi ga Rashin Haihuwa ko kuma a wayi Gari ba zai Iya dadewa yana Iya Saduwa da Wannan Amaryar tasa ba. Minti biyar ko Goma ya Gama Ya Hakura. Wanda ba Mamaki Kuma Ita Daga Lokacin ne ma take Bukatar sa.
Amma Kuma Babu Labari Sai dai Barci Ita Kuwa zata kwana idonta Biyu a cikin Damuwa da Bacin Rai.
Akwai wanda ya zo ya same Ni kamar zai yi Min Kuka Yana Gaya Min Matsalar da ya Fuskanta a daren Angwanci. Wai Amarya ma Fushi take yimasa. Anan ne na Zaunar da shi, na Bashi Kyakykawar Magana. Na Nuna masa cewar Daman ana iya Samun irin wannan Matsalar Na Nuna masa cewar ba fa ta kansa aka fara ba Anan Na Bashi Abubuwan da suka dace Tin daga wannan Ranar bai sake dawowa ba, Bayan Mun Hadu wani Lokaci Ya Nuna Min Cewar ae ga matsala ce ta Kawo shi Tinda babu wannan matsalar kuma shine bai dawo ba
Saboda haka Shi Wanda aka sanya Masa Ranar Aure Yana da kyau Ya Tuntubi masani ilimin magani da zasu hadashi yayi tsaf,yasha magani kamar yadda amare sukeyi tun shaura wata 6 bikinsu ko wata 3, ka samu a hada maka Abubuwan da ake Bayarwa na Angwaye. Insha Allahu ba zaka Nemi Taimakon kowa ta wannan bangaren ba Sai dai Kawai ka Nemi Taimakon Allah.
Sai dai Kuma yana Faruwa wani ya Baka Maganin Bature Sabida Haka Kada ka Sake Wani ya Baka Magunguna irin na Bature. Sabida Illar da yake Haddasawa kamar Haka: Lalata Ido, Yawan ciwon Kai, Toshewar hanci, Kasala, Yoyon Fitsari,damuwa,fitsarin jini,Mantuwa da rudewa qaiqayin maqogwaro,bushewar baki,kuma duk wanda ya dade yana amfani dashi gabanda zai daina aiki. Sannan Amfanin sa a Jikin Mutum na Iya
Wannan Lokacin ne Kawai.
Shi Kuma Na Islamic Magani ne da yake Bin Jikin Mutum. Sabida Magani ne na itatuwa da kuma hade-haden Gargajiya Na Asali.
ABUBUWAN DA ANGO ZAI FARA KAFIN WATA 3:
1- ka samu habbatussauda, kustul Hindi, hulba, haltil, jinsen ka hadasu da dan yawa Ka niqasu sai ka dinga shansa kullum a shayi kamar teaspoon sau 3 a rana ko Kuma kadinga dafa cokali 2 a shayi kamar filas 1 kadinga Sha Kuma abin mahadin kada kasa suger sai dai mazar qwaila ko Zuma Mara hadi.
2- zaka Fara amfani da Maganin sanyi Mai kyau da maganin basur kana Sha lokaci lokaci.
CIKAMAR DA TAKE SA QARFIN JIMA'I:
Akwai wasu abinci da idan akayi anfani dasu suna sa kuzari ga da namiji misali Kamar su:
citta,barkono ayaba,salak,dabino,alaiyahu,albasa, wanan kamai dasu sukan abiinda kakeci idan kana Shirin aure da Bayan aurenka.
CIMAKAR DA TAKE QARA QARFIN MARAINA:
Gyada, Garin gero, yayan itaciya, man zaitun, gayyanyaki, wake, Kara's , dankalin hausa,yayan gurji da yayan kabewa da kwai na kazar gida dss.
CIMAKAR DA TAKE QARA RUWAN MANIYYI:
Ayava ,tumatur,yayan kabewa,gyada da gyadar yarabawa, tafarnuwa, ja fake anfani da wadanan kafin aure da Kuma Bayan aurenka.
CIMAKAR DA TAKE DA JIN DADIN JIMA'I:
Citta Mai kwaya, ayaba, gyada, Zuma, lemon Zaki, kubewa dabino busasshe, aya, yayan kabewa dss.
ABUBUWAN DA ANGO ZAI BARI KOMA YADAINA SHA:
Suger, lemon kwalba Dana roba, Shan taba, shangiya, Duk wani nau'in lemo da aka sawa suger ko kafi suger, Dan zaqi, sweetener Duk sai ka barsu idan kanason ka Zama cikakken namji.
ABUBUWAN DA SUKE SA RAUNIN AZAKARI:
Ciwon zuciya, hawan jini, yawan kitse a jiki, kunburin maraina, Rashin samun bacci, qanqancewar maraina, ciwon suger, Shan suger, tunani da yawa dss, wannan matsaloli dana lissafa toh idan kasan kana dasu ka Fara Neman magani kafin aurenka.
YA KAI ANGO SHAURA SATI 2 DAURIN AURE ZAKA FARA WANAN:
1-A samu cucumber a wanke ta sai asata a blender a markade har bawonta idan an markade sai a juye a kofi a sa zuma cokali tatacciya sai ka juye ka shenye ,zaki haka kullum har ranar daurin aure.
2-- za'ayi kunu salala na gyada ko gero idan ya dahu an sauke sai ka zuba garin habbatulrashad cokali 1 babba ka juye ka shanye shima za'ayi maka kullum har sati 2 zuwa ranar daurin aure.
3---za'a samu albasa manya guda 3 a tafasa sosai sai a sauke ayi blending sai azuba wanann ruwan da aka albasar a cakuda sai azuba Zuma adinga sha , shima Zaka Fara tun shaura sati daurin aure har zuwa ranar da za'a kaika.
4--- Asamu man habbatussauda, man hulba da man Ridi sai a hadesu adinga zuba cokali 1 amadara kanasha har zuwa ranar daurin aure.
Zai taimaka maka wajen samum qarfi ,kuxari ,hana saurin kawowa,yawan ruwan maniyyi,hana gajiya,karkashi da nishadi.
AQARSHE: ya Kamata lalai maza su tashi tsaye wajen gyara jikinsu kafin aure domin wannan matslaar tana da mutuqar hadari ga rayuwar aurenmu awanan zamanin domin Mata suna yin Sama da wata 6 suna gyara jikinsu da Shan magani kala kala na sanyi da samun nishadi shiyasa Idan baka gyara ba kana kallon matar zata fi qarfinka bazaka iya da ita ba sai dai kabarta cikin qunci da damuwa daga Haka Kuma tafa samin rauni da damuwa har ta Fara hango wani nimijin bakai ba.
Allah ta'ala yasa mudace
0 Comments