WARIN GABAN MACE DA MAGANINSA
Yana da matukar muhimmanci a matsayinki na mace ki san irin warin da ke fitowa daga al'aurarki.
Ta wannan, za ki san yadda lafiyar gurin take.
Wasu matan suna daukar warin da ke fitowa daga al'aurarsu a matsayin wani abu da ba shi da mahimmanci a kula da shi kuma hakan na iya haifar da wasu cututtuka da yawa idan ba a kula ba. Hakanan zai iya sa mijinki ya nisance ki.
Akwai nau'ikan wari guda 5 da kowace mace za ta iya samu.
Su ne kamar haka;
1. FISHY ODOUR
2. ROTTEN ODOUR
3. METALLIC ODOUR
4. MUSKY ODOUR
5. YEASTY ODOUR
FISHY ODOUR
idan al'aurarki ta kasance tana wari kamar sabon kifi sannan kuma tana zuwa da farin ruwa ko launin toka.
Wannan matsalar bakteriya ce ke haifar da ita, kuma kwayoyin cutar da ke haifar da hakan galibi ana kiran su "VAGINOSIS".
ROTTEN ODOUR
Wannan wari ne mai tsananin gaske wanda zai iya haifar da cututtuka da yawa cikin kankanin lokaci. Kuma wannan matsalar na iya haifar da matsaloli masu yawa a gare ki har ta kai ga gaban mace zai fara rubewa.
Wannan nau'in shi ma ƙwayoyin cuta ne ke haifar da shi amma ya fi ƙwayoyin kifi (fishy bacteria).
METALLIC ODOUR
Lokacin da al'aurarki ta kasance tana wari kamar karfe mai tsatsa.. kuma wannan yakan faru ne bayan al'adar wata-wata ko kuma bayan an rushe sashin pH ta hanyar fitar da maniyyi.
A al'ada, yana ɗaukar kwanaki 3-7 don wannan warin ya tafi ta dabi'a, amma idan ya ci gaba, kuna buƙatar duba lafiyar ku musamman sashin pH na al'aurarki.
MUSKY ODOUR
lokacin da al'aurarki ta ba da wari mai yanayin musky, yana nufin kina sanye da matsattsun wando don haka ba a bai wa gabar wata dama ta shan iska ba.
Kuma yawan barin faruwar hakan, yana ba da damar ƙwayoyin cuta su zo kusa da ku ta ɓangaren al'aurarku.
YEASTY ODOUR
Warin Yeasty yana nufin kina da ciwon Yeast. Don haka da zarar ya ba da warin Yeasty, ki hanzarta zuwa a duba lafiyar ki.
MAGANI
Don magance wadannan matsalolin, sai a tafasa ganyen darbejiya (Neem) da kanunfari (ko kuma kanunfari kawai) na tsawon minti 15 zuwa 20, sannan a zuba gishiri kadan idan ya huce har ya kai matakin da za a iya shiga ciki. a shiga ciki na akalla minti 15 zuwa 20, sau biyu a mako.
Ko kuma
Sai ki tafasa ruwanki ki zuba masa gishiri, sannan ki zauna a ciki na kamar minti 15-20.
Kiyi haka musamman a lokacin haila kuma ki tabbatar kina yin hakan sau biyu a mako.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments