TUSAR GABA


📑 TUSAR GABA 📝

SHARE ⌛

Tusar gaba wacce a turancin Likita ake kira da "Vaginal flatulence" ko "vaginal flatus" ko "queef" ko "vaginal gas" shine riƙe iska da fitar da ita daga farjinta kamar tusa amma iskar bata fita da wari. 
Yana zama illa babba yayinda tusar take fita da wari wanda hakan yana faruwane sakamakon tsagewa ko yankewar mahaɗa tsakanin farjin mace da gaɓoɓin da suke haɗe da farjinta, wani lokaci mace takanga fitar bayan gari daga farjinta musamman a lokacinda take fitsari. Wannar matsalar ana kiranta "Vaginal Fistula".

👉 Ki gaggauta ganin likita dazaran kin fara jin wari yayin tusar gaba ko ganin bayan gari yana fita agabanki ko fitan ruwa mai wari ko yawan samun infection ko jin zafi acikin farjinki ko tsakanin farjinki da ƙofar ɗuwawu.

LOKUTAN DA AKE SAMUN ISKAR GABA:

1- Yayin saduwa musamman idan mace batada matsi ko iska mai yawa a wurin kamar iskan fanka
2- Yayin motsa jiki
3- Yayin miƙa ko ɗaga abu mai nauyi
4- Yayin likita ya sanya wani abu a farjin mace (speculum) ko duba mararta
5- Yayin renon ciki
6- Haihuwa da yawa ko lokacinda mace takai shekarun daina jinin al'ada.

YANDA ZA'A MAGANCE MATSALAR:

1- Kisamu garin Tazargaɗe da garin Bagaruwa da garin lalle kihaɗa kidafa da ruwa mai yawa kitace kisa a baho idan yayi lif-lif saiki zauna ciki na mintuna 15. Zakiyi sau biyu arana.

2- Ki kwaɓa garin lalle kihaɗa da zuma kidinga yin matsi dashi idan zaki wanke sai kisamu syringe na allura kimatsi ruwan ɗumi (kisa gishi a ruwan) ki matsa cikin yana zubowa waje.

Post a Comment

0 Comments