Bayani game da ruwan rake.
1. Yana taimakawa wajen karfafa hanta kuma yana daya daga cikin maganin shawara.
Ruwan rake mai dauke da sinadarin ‘Antioxidants’ yana kuma taimakawa wajen kare hanta daga kamuwa da cuta.
2. Tunda ruwan rake yana maganin diuretic, yana taimakawa wajen kawar da guba daga jiki da cututtuka.
kuma shan shi akai-akai yana taimakawa wajen hana kamuwa da cutar yoyon fitsari da kuma kawar da zafin lokacin fitsari.
3. Yana hana ciwon ciki, sannan yana da kyau wajen maganin constipation.
4. Shan ruwan rake a kai a kai yana taimakawa Ƙarfafa garkuwar jiki.
5. Akwai ma'adanai da yawa da ake samu a cikin ruwan rake, kamar su calcium, magnesium, phosphorus, iron da potassium, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa ƙasusuwa.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
0 Comments