» YADDA ZA KI YI AMFANI DA FIYA DA MAN ZAITUN WAJEN GYARAN FUSKARKI
YADDA ZA KI YI AMFANI DA FIYA DA MAN ZAITUN WAJEN GYARAN FUSKARKI
Sau da dama mutane sun dauka amfanin fiya shi ne a ci, ba tare da sun fahimci ana amafani da ita wajen gyaran jiki da fuska ba. Dalilin da ya sanya a wannan makon muka taho miki da matakan da za ki bi wajen amfani da fiya da kuma man zaitun wajen gyaran fuskarki ke nan. Kafin mu kai ga bayanin yadda za ki yi amfani da fiya da kuma man zaitun wajen gyaran fuskarki, za mu bayyana miki amfanin fiya ga jikin dan Adam Amfani fiya ga jiki:
· Fiya tana dauke da sanadarin bitamin A da kuma Glutamine wadanda suke taimakawa wajen kawar da matattun kwayoyin halittar cikin fata.
· Ana amfani da fiya ga busasshiyar fata don kawo danshin fata. Tana dauke da sinadarai masu yawa wadanda suka hada da bitamin K da C da Copper da Iron da sauransu.
· Laushin fata: fata takan tsotse man da yake cikin fiya, wanda hakan yakan sanya man ya ratsa kofofin fata, inda fata kuma takan tatse sinadaran da suke dauke a cikin fiya, wannan sai ya sanya fata ta yi laushi da kuma dadin gani.
· Mayar da tsohuwa yarinya: Fiya tana dauke da sinadaran da suke kone kwayoyin cututtukan da suke kodar da fata, wanda hakan sai ya sanya fata ta rika sheki da kuma laushi, har a rika taken ta mayar da ke yarinya.
· Hasken rana yana dauke da sinadaran da suke kodar da fata ko kuma su sanya saurin tsufa, amma sakamakon sinadarin da fiya take dauke da shi, sai ya zamanto ta kare fata daga haske rana.
Idan kika hada fiya da kuma man zaitun zai sanya fatarki laushi da damshi da kuma sheki. Fiya da man zaitun na amfani ga busasshiyar fata, musamman ma wajen kare fata daga bushewa ko zazzagewa.
Kayan hadi:
1. Fiya
2. Man zaitun
3. Kukumba
Yadda aka hadawa:
Ki samu fiya babba daya, sai ki cire bayan fiyar, daga nan sai ki daka ta, bayan nan sai ki zuba man zaitun, sannan ki gauraya sosai, daga nan sai ki shafa a fuskarki.
Ki samu kukumba, sai ki daka ta, daga nan ki shafa a fuskarki. Za ki bari har tsawon minti 10. Daga nan sai ki wanke fuskarki da ruwa mai dumi, sannan ki yi amfani da tawul mai tsafta wajen goge fuskarki.
SHARE
0 Comments