Wasu Zakakan Kalmomi Daga Namiji Zuwa Ga Matarsa:


Wasu Zakakan Kalmomi Daga Namiji Zuwa Ga Matarsa:
 
#Tsangayarmalamtonga

 
A ci gaba da kawo muku wasu zakakan kalamai na furtawa matarka ko masoyiyarka ko tura musu sakonnin karta kwana, ga wasu nan da maza zasu iya amfani dasu zuwa ga matansu.

 
1: Ina jin dadin hira dake. Duk kalma guda naki yana dauke da sakon dake sanyaya rai.

2: Yau ce rana mafi daraja a gareni da kika zama matata ko kuma kika amince da soyaya na.

3: Cikenkiyar fassaran kalmar soyayya yana tare dake.

4: Babu wani Dan da zai fito daga cikinki da ba zai yabawa zabina dana masa na uwa tagari irinki ba.

5: Wasu lokutan ina satar kallonki na karemiki kallon da har ina mamakin yadda kika amince dani cikin maza sama da biliyan dake fadin duniyan nan.

6: Duk wannan nasaran da daukakan da muka samu a rayuwarmu na miji da mata, kece sila.

7: Daga ranar da kika amince ki aureni. Daga wannan ranar na nemi abubuwan danake yi marasa kyau na rasasu.

8: Na gode Allah daYa banike a matsayin silar shiryuwata.

9: Ba domin ke ba, da gidan ya zama kango duk da kyausa, girmansa da kayan alatun dake cikinsa.

10: Banida aboki da ya wuce ki uwar yayana.
 
Yi kokari a kullum ka farantawa matarka da wani kalma guda na soyayya.

Wadannan kalaman sunada matukar tasiri a wajen mata fiye da maza. Kada ka dauka tunda kai baka damu dasu ba, ita ma. Duk kalma guda na soyayya da zaka furtawa matarka ko masoyiyarka, yana kara mata lafiya da kaunarka.

Post a Comment

0 Comments