`YA`YAN ITATUWA DA AKA AMBATA A ALQUR'ANI


`YA`YAN ITATUWA DA AKA AMBATA A ALQUR'ANI


(1) RUMMAN
===========

Allah ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ
Ya ambace shi a Alqur'ani, Ya ce:
" ﻓﻴﻬﻤﺎ ﻓﺎﻛﻬﺔ ﻭﻧﺨﻞ ﻭﺭﻣﺎﻥ "
.
"Fiy himaa faakihatun wa nakhlun wa RUMMAN"
A cikin Suratur Rahman.

Ruman yana cikin tsirrai masu matukar amfani a duniya wadanda masana sukay bincike a kansa.
Tun shekaru dubunnai da suka wuce ake amfani da Ruman a matsayin Magani a kasashen Gabas ta tsakiya wajen maganin Olsa da Gudawa da dai sauransu.
.
Allah Ya ambaci Rumman a Alqur'ani, cikin Suratur Rahman, lokacin da Yake bayyana irin bishiyoyi na alfarma da Ya tanada a ckin Aljanna.
Kasancewar Rumman yana cikin bishiyoyin Aljanna ya isa ya nuna mana muhimmancinsa ga rayuwar danAdam kasancewar Aljanna gidan ni'ima ce.
.
.
Bincike ya tabbatar da cewa Rumman yana:
.
.
★Kara Lafiyar Zuciya.
Shan Ruman yana da muhimmanci sosai wajen kara lafiyar zuciya. Yana rage sinadarin 'atherosclerosis' wanda yana daga cikin sinadaran da ke haifar da cututtukan zuciya. Yana rage hadarin toshewar hanyoyin da ke kaiwa da fitar da jini daga zuciya zuwa kwakwalwa.
.
.
★Haka dai Rumman yana rage sinadarin LDL ko mu ce kitse mara amfani wanda ke cikin jini, sannan ya samar da sinadarin HDL wato kitse mai amfani.
.
.
★Daidaita Sikarin Jini.
Ruman yana da sinadarin 'fructos' don haka baya kara adadin sikarin da ke cikin jini kamar yadda wasu tsirran suke yi. Masana sun yi bayanin cewa ba wani hadarin karuwar sikari a cikin jinin masu cutar diabetes wadanda suka sha Rumman kullum har tsawon sati biyu.
.
.
★Maganin Hawan Jini.
Ruman sananne ne wajen rage matsalar hawan jini.
.
.
★Rage Hadarin Kamuwa da Cutar Kansa (cancer).
Shan lemon juice na Ruman kofi daya a kullum yana rage kwayoyin cutar kansa dake jikin mutum.
.
.
★Maganin Gudawa.
Shan Ruman tare da zuma cokali daya yana taimakawa wajen warware matsalolin da suka shafi Hanji. Kamar Gudawa, Atini, kumburin ciki da dai sauransu.
.
.
★Saukaka Fitar Fitsari
Ga masu matsalar.
.
.
★Mata Masu Ciki.
Ruman yana da sinadaran vitamins da minerals wadanda ke taimakawa mata masu ciki wajen hana yawan 6acin ciki, ciwon kafa da haihuwar yara wadanda nauyinsu bai kai ba.
.
.
★Gyara Fata.
Shan lemon Ruman yana gyara kowace irin matsalar fata. Yana maganin matsalar bushewar fata yana kuma samar da tattausar fata kuma lafiyayyiya mai kyau.
Shafa Ruman a fatar jiki yana maganin kuraje tare da ba ta kariya daga cutar Kansa.
.
.
★ Zubewar gashi.
Shan Ruman yana samar da wasu sinadarai a jikin mutum wadanda ke hana gashi karyewa da zubewa.
.
.
★Rashin Sha'awa.
Shan lemon Rumman yana maganin matsalar rashin sha'awa ga ma'aurata.
.
.
★Yana kuma Kara Kafin Maza.
.
.
★Rashin Haihuwa.
Amfani da Rumman na taimakawa wajen maganin matsalolin da kan iya kawowa mutum rashin haihuwa.
.
.
★Karfafa Garkuwar jiki.
Shan Rummanna taimakwa masu cutar Raunin Garkuwar Jiki kamar HIVaids wajen kara karfafa garkuwar jikinsu.
.
(2) DABINO.
==========
Dabino yana dauke da sinadarin da ke
karawa jiki karfi da kwari, yana mayar da
sukari da ke cikin jinin mutum wanda
yake raguwa sakamakon rashin cin abinci
ko abin sha, dabino yana dauke da
sinadarin ‘Iron,’ wanda yake taimakawa
wajen karin jini. Sannan yana karfafa jini
da hantar mutum. Ga wasu daga ciki:-

1. Yana samar da ruwan jiki
2. Yana taimakawa mata masu ciki
3. Yana karawa mai shayarwa ruwan
nono
4. Yana gyara fatan jiki
5. Yana maganin ciwon kirji
6. Yana maganin ciwon suga
7. Yana maganin ciwon ido
8. Yana maganin ciwon hakori
9. Yana gyara mafitsara
10. Yana maganin basir
11. Yana kara lafiyar jarirai
12. Yana rage kiba, wadda ba ta lafiya
ba ce ma’ana kumburin jiki na ciwo
13. Yana maganin, majina
14. Yana sa kashin jiki ya yi karfi
15. Yana maganin gyambon ciki (Ulcer)
16. Yana kara karfi da nauyi
17. Yana maganin ciwo ko yanka
18. Yana karawa koda lafiya
19. Yana maganin tari
20. Yana maganin tsutsar ciki
21. Yana maganin kullewa ko cushewar
ciki
22. Yana rage kitse
23. Yana maganin cutar daji (Cancer)
24. Yana maganin cutar Asma (Asthma)
25. Yana kara karfin kwakwalwa
26. Yana maganin ciwon baya, ciwon
gabbai, ciwon sanyi wanda yake kama
gadon baya.
27. Yana kara sha’awa da kuzari
28. Yana magance cututtuka dake
damun kirji
29. Yana karya sihiri.
30. Yana saurin narkarda abinci
31. Yana taimakawa wajen kara jini
32. Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata
33. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi.
34. Yana Maganin Gudawa
35. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun
basira..
36. Yana kariya daga Sihiri
37. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun
sauqi wajen haihuwa.
38. Yana kariya daga Sihiri.
ADDA ZA'AYI AMFANI DA DABINO WAJEN NEMAN LAFIYA.

>>CIWON NONO GA WACCE TA HAIHU;

Anacin dabino guda 7 asha man
tafarnuwa karamin cokali sau 1
arana kwana uku.

>>DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;
Ana daka dabino a zuba cikin
madara (freesh milk) sannan a
saka Zuma a ciki a sha awa daya
kafin a kwanta.

>>GA MATA MASU JUNA BIYU;
Ana cin dabino kwara bakwai
kullum da safe idan anyi kusan
haihuwa Wannan yana hanawa
macce yawan zubar jini lokacin
haihuwa da iznin Allah.

>>GUDAWA;
Ana daka garin dabino a saka a
ruwan zafi a sha In shaa Allahu
yana tsayar da gudawa.

>>SAMUN KUZARI;
Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1
da safe da yamma.

>>SAMUN LAFIYAYYAR FATA;
Ana hada garin dabino da zuma
da man zaitun a shafa a fuska awa
daya sai a wanke fuskar da ruwan
zafi wannan yana saurin gyara fuska. Bincike ya
nuna Yawaita cin
dabino na hana kamuwa da ciwon

(3) AMFANIN AYABA
******************
CIN AYABA YANA KARIYA DAGA KAMUWA DA
CIWON DAJIN KODA (KIDNEY CANCER), AYABA
TANA DAYA DAGA CIKIN ABUBUWAN DA SUKE
SA MUTUM YA ZAMA MAI SAURIN DAUKAN
KARATU DA DABARA AYABA NA TAIMAKAWA
WAJEN KARA KUZARI.
SHAFA AYABA A FATA NA KARAMA FATA KYAU
DA ZAMA SUMUL
AYABA TANA KARFAFA IDO KUMA TANA KARE
IDO DAGA CUTUKKA.
AYABA NA KARE MUTUM DAGA CUTAR ULCER
Mutane da yawa na son cin ayaba amma basu san
amfaninta ba, haka na sha ganin tambayoyi akan
wai ayaba nasa kiba?
Amma amsar shine ba dan itaciyar dake sa kiba idan
ka cishi kamar yarda aka fiddo shi daga lambu balle
har ma yasa kiba.
Ayaba na narkewa cikin mintina (45)sauran 'ya 'yan
itatuwa na narkewa cikin mintina (15) wannan shine
yasa kasa zaka ji wasu na cewa cikina ya cika na ci
ayaba amma bayan mintina 45 zasu ji kuma duk ya
narke.
Idan mutum zai mai da ayaba da
sauran 'ya 'yan itatuwa abin karin kumallon sa cikin
sati daya zaiga chanji wajen Lafiyar sa.
Ayaba na taimakawa Wajen Rage kiba, ayaba na
tattare da kayan gina jiki wanda ba sa saka kiba.

YADDA ZA'AYI AMFANI DA AYABA WAJEN
MAGANI.DOMIN RAGE KIBA;
Kullum Mutum yaci ayaba Ukku kafin ya karya
kumallo har tsawon Sati 3.

DOMIN MAGANI KURAJEN FUSKA;
Ana hada Ayaba da Zuma a shafa a fuska da dare
awa daya kafin a kwanta idan za'a kwanta a wanke
da Ruwan dimi sai a shafa man Zaitun.

DOMIN CUTAR ULCER;
Ya kamata mai cutar Ulcer ya riqa cin abinci da
Ayaba ko kuma cin ayaba bayan ya gama cin
abincin, yin haka na Warkar da ita kuma yana kariya
ga wayanda basu da ita.

DOMIN SAMUN LAFIYA GA JIKI;
Mutum ya mayar da ayaba abincin da zai fara ci
kafin yaci komai da safe.

(4) ZAITUN
=========

Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah
Madaukakin Sarki Ya ambace ta a cikin
Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An-
Nur.

Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan
adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana
da amfani kamar haka:

1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da
kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting
virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan
cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama,
kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.

2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga
kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant
subtances).

3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage
yawan sinadarin kolestirol (reducing high
cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake
da illa ga zuciya.

4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).

5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic
patients).

6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi
(anti-rheumatism & arthritis).

7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's
function esp. to older people whose hearts are
weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda
zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa.
Yana gyara zuciya da quruciya.

8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata
( protection from skin cancer).

9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).

10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu
kamar karatu ko rike karatun, musamman ga
manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:

~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da
rana, cokali daya a kowane lokacin.

~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba
cikin abinci bayan girki.

~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.

~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari,
zai kuma bada kariya daga cututtuka.

~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.

~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.

(5) `BAURE
=========

Shi dai ɓaure wani dan itace ne da yake da nasaba da durumi, sai dai ya dara durumi zaki nesa ba kusa ba. Binciken Legit.ng ya bankado sunadarai da ɓaure ya kunsa tare da cututtukan da yake kawar wa na jikin Dan Adam

Manyan sunadarai da wannan dan itace na ɓaure ya kunsa sun hadar da calcium, potassium da kuma fiber.

ga jerin cututtuka 15 da baure ke bayar da kariya a gare su tare da warkar da su.

1. Inganta karfin kashi

2. Kariya ga cututtukan mafitsara.

3. Kawar da cututtukan makogoro

4. Ganyen ɓaure yana kawar da cututtukan zuciya

5. Kariya ga ciwon daji (kansa)

6. Tsari ga ciwon sukari.

7. Cutar hawan jini

8. Inganta lafiyar iyalai wajen saduwa.

9. Tarin Asma da tarin fuka

10. Ciwon kunne

11. Zazzabi

12 Maruru

13. Inganta karfin gani na idanu

14. Kawar da cututtukan da ake dauka ta hanyar saduwa.

15 Narkar da daskararren maiko na jikin dan Adam.

(6) INIBI
=======

1- Yana daidaita yanayin nauyin jikin danAdam saboda sinadaran 'antioxidants' da yake dauke da su, wadanda ake kira da 'flavonoids'.

2- Yana gyara tsokar zuciya. Inibi yana dauke da sinadaran da ke taimakawa zirga-zirgar jini daga zuciya zuwa sauran jiki sannan yana rage hadarurrukan da kan faru a hanyoyin tafiyar jini.

3- Lafiyar Qwaqwalwa.
Inibi yana dauke da sinaran da ke kyautatawa tare da inganta lafiyar qwaqwalwa.

4- Fatar jiki.
Sinadaran 'phytonutrients' da ake samu acikin yayan itatuwa masu kala, kamar irinsu Inibi, yana taimakawa wajen kare fatar danAdam daga cututtuka.

5- Hawan jini.
Inibi yana rage hadarin kamuwa da hawan jini amma a shawarce ya kamata mai wannan matsala ya ci inibi wanda aka busar da shi ko wanda aka daskarar a firinji ko kuma Inibin da kay lemo da shi.

8- Cancer.
Yawan cin inibi ko kuma cin inibi da yawa, can rage hadarin kamuwa da cutar kansa.

Post a Comment

0 Comments