AMFANIN NONON RAƘUMI WAJEN MAGANCE CUTUTTUKA GUDA ARBA'IN DA TARA (49).
Karanta har ƙarshe, domin samun cikakken bayani akan yadda za ka haɗa maganin lalurar da ke damunka, da yaddar Allah.
1-Ciwon Ulcer/Gyambon ciki. 2- Ciwon Typoid. 3- Ciwon Tibi/Tarin Fuka. 4-Ciwon Asma. 5-Ciwon Basir. 6-Ciwon Hawan jini. 7-Karancin jini a jiki. 8-Ciwon suga. 9-Ciwon cancer. 10-Ciwon sanyi. 11-Fitar ruwa mai wari a gaban mace. 12-Rashin fitar jinin Haila. 13-Maganin kurajen Pimpus.14-Kaikayin fata. 15-Ciwon fitsari. 16-Fitsarin jini. 17-Ciwon shawara. 18-Domin samun kwarin kashi. 19-Raunin ji na kunne. 20-Maganin daskarewar jini a jikin mutum. 21-Ƙarancin ruwan maniyyi.
22Maganin saurin kawowa. 23-Karfin mazakuta. 24-Domin samun gamsuwar jima'i. 25-Shanyewar kashin yara. 26-Maganin mura. 27-Maganin Amai da Gudawa (Cholera). 28-Ciwon Mahaifa. 29-Ciwon Saifa. 30-Ciwon Hanta. 31-Ciwon dan yatsa/Karkare. 32-Maganin yawan ɓarin ciki. 33-Maganin Kasalar Jiki. 34- Maganin kumburin Ciki. 35-Maganin warin baki. 36-Maganin magwas/Kornafi. 37-Buguwar Kashi/Targade. 38-Ciwon Ga6o6i. 39-Rashin sha'awar abinci.40-Rashin ruwan jiki. 41-Domin walwalar yaro.42-Ciwon maraina. 43-Murɗawar ciki. 44-Hasken fata. 45-Maganin zubewar gashi. 46-Maganin Dasashin Hakorida Kumburinsa. 47-Macen da gabanta yake wari. 48-Macen da gabanta ya bude. 49-Daukewar sha'awa.
(1) CIWON ULCER/GYAMBON CIKI
Wanda yake fama da ciwon Gyambon ciki to sai
ya yi kokarin samun waɗannan mahadan kamar
haka:
a)Nonon Raƙumi
b)Ɗanyen Kwai
c)Man Habbatus sauda
d)Zuma
e)Bizru Kattan
f) Irƙususu
Da farko sai a samu Nono (madara) wacce ba a
hada ta da wani abu mai zaki ba, kamar kofi daya,
sai a tafasa danyen kwai a cikin nonon, a sha da safe
kafin a ci wani abu. To sai a dakata zuwa awa daya
da rabi sai kuma a hada man Habbatu kamar cokali
biyu tare da garin Bizru Kattan cokali daya a kofin,
sannan a zuba Irkususu cokali daya, sai a juya a sha.
Za a yi haka zuwa kwana bakwai to insha Allahu za
a warke.
(2)CIWON TAIFOT (TYPOID)
Mai fama da lalurar Taifot sai a samu:
a)Tafarnuwa
b) Nonon Raƙumi
c)Zuma
d)Man zaitun
e)Man tafarnuwa
Da farko sai a samu madarar nonon kofi đaya sai
a zuba tafarnuwa kamar ķwaya biyar tare da zuma
sai a sha tun kafin a kwanta, barci. Sannan sai a samu
man tafarmuwa tare da man zaitun. a shafe kashin
baya da shi. In kuma aka wayi gari sai a tafasa
tafarmuwa a shaki tururinta. To insha Allahu za a
warke da izinin Allah.
(3) CIWON TIBI KO TARIN FUKA
Dangane da mai tarin fuka zai rika amfani
nonon rakumi kofi đaya duk bayan cin abinci tare da
dauwama a kan haka. To insha Allahu zai samu
sauki da izinin Allah.
(4) CIWON ASMA
Mahaɗan su ne:
a)Nono Raƙumi kofi ɗaya
b) Irƙu Dahabu ƙaramin cokali
c) Citta cokali daya.
d) Za'atar Jabali rabin-rabin cokali
e) Sabgul Arabiy, cikin ƙaramin cikin cokali
To, sai a hada wadannan da muka kawo a cikin
kofi daya na nono sai a sha kofi daya da safe tun kafin a ci wani abu, idan kuma an sha, a samu awa daya sannan za a ci wani abu, haka ma da yamma za a sha kofi daya tun kafin a ci abincin dare. Sannan idan an sha sai an samu awa
sannan za a ci wani abu, Za a rinka maimaitawa. Da
fatan Allah ya sa a dace, ya ba da lafiya.
(5) CIWON BASIR
Wanda yake fama da ciwon basir to sai ya yi kokarin
samun fitsarin rakumi yana shafa shi a duburarsa wato yana matsa shi a duwawunsa. Zai yi haka sau uku a rana, kullum.
Sannan kuma ya rinƙa shan nonon rakumi safe
da yamma, har Allah ya ba shi sauki. Haka ma matsa
nonon rakumi a duwawu yana maganin basir mai
tsiro.
(6) CIWON HAWAN JINI
Mai fama da hawan jini sai ya yi amfani da wannan hanyar kamar haka:
shi ne, ya sa mu kofi
daya na Madarar Nonon Raƙumi ya sha da safe tun
kafin ya ci wani abu, sannan bayan ya ci abinci sai
ya yi amfani da wadannan mahadan kamar haka: -
a)Man Habbatus saudaa
b)Hulba
c)Na'ana'a
d)Kuzbara
e)Yansun
f)Baƙadunas
Da farko idan ya samu abin shan sa, to sai ya
diga man Habbatus sauda a ciki kamar digawa bakwai, to
sai ya zuba wadannan mahadan a ciki. Sai ya sha
kamar sau uku a rana bayan ya ci abinci tsawon sati
đaya. Sannan kuma zai iya shafe jikinsa da Habbatus saudaa da rana sai ya yi wanka koda sau daya a kowane sati.
To insha Allahu zai ga sauki da lafiya. Ko kuma zai
iya shafe jikinsa da man Habbatu tun kafin ya
kwanta barci ba tare da ya yi wankan rana ba.
7) ƘARANCIN JINI A JIKI
Dangane da karancin jini a jikin mutum, cutar
da ake cewa Nimoniya (anaemia).
To, sai a samu cikin kofi na Nonon Rakumi tare
da cikin babban cokali na garin Alkama sai a kada a
sha da safe, da yamma kuma sai a samu kofi a zuba
garin hulba tare da zuma, amma ba farar saka ba, sai
a sha zuwa sati biyu.
Ko kuma ma'abocin karancin jini ya dauwama
da shan wannan hadin:- wato ya samu dabino da
nonon Raƙumi sai ya hada, ya markaɗa idan ya cire kwallon, sai ya rika sha duk lokacin da ya ci abinci safe da yamma da dare.
To insha Allahu za a warke da
yardar Allah.
0 Comments