SIRRIKA 6 DA AMFANIN JIGIDA A KUGUN MACE.
1. A wasu yankunan ana hada jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen boye, wato aljanu.
2. Wani jigidan akan hada da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara.
3. Wasu jigidan akan hada su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin nakuda a lokaci haihuwa.
4. Akwai yakinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi ko katon ciki.
5. Jigida na taimakawa wa mace wajen kara girman kugu wato Hips a Turance, dakuma samun farin jini cikin mutane.
6. Jigida na daya daga cikin abubuwan dake jawo sha'awa da ra'ayin namiji zuwa ga mace.
Sai dai kuma duk da wadannan kyawawan dalilan wasu mutane da dama basu son jigida saboda a ra'ayinsu jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani tsafi.
Wata mata da ta shahara a hada jigida Felicia Musa ta ce tana matukar sha'awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana kara idan tana tafiya.
Ta ce jigida iri-iri ne akwai wanda wasu matan ke sakawa na farin jini ko na samun kariya amma yi hakan ba shine ke mai da mutum matsafi ba.
0 Comments