CUTAR ULCER PART 1.
Cutace wanda ake samunta sanadin kwayoyin cututtukan Bacteria wanda ainashin sunan cutar shine (HELICOBACTER PYLORI) "H PYLORI" cutar tana zama acikin hanji har takai ga haifar da gyambo. Shine a hausa ake kiranta da suna gyambon ciki.
Ciwon ulcer yakasu kashi, kashi. Ga wasu kaďan daga ciki.
1-➡️Peptic Ulcer.✅️
ita ake kira da Gyambon hanji. Ita Kwayar cutar bacteria mai suna HELICOBACTER PYLORI (H. PYLORI) itace silar kowacce kalar ulcer.
Ana samun wannan BACTERIA acikin abinci wanda ayayinda mutun yace cin abinci idan akwai kwayar wannan cutar babu makawa zata zauna acikin stomach wato cikin tinbinsa da laďan kaďan sai tazamo ciwo, to shine ake kiranta da suna gyambon ciki.
Haka zalika yin amfani da magunguna na STEROIDAL ANTI-INFLAMMATORY (NSAIDs)
⬇️irin su.
1-Ibuprofen❌️
2-(Advil❌️
3-Motrin IB)❌️
4-Naproxen sodium (Aleve)❌️
Waýannan magunguna sukan haifar da ciwon ulcer amma ga wanda dama yanada ita cutar ulcern
Abinci mai yaji baya haifar da ciwon PEPTIC ULCER sai dai shi YAJI yakan haifar da Gastric Ulcer Amma banda Peptic ulcer shima duk hakan yana faruwa ne asanda mutun yake ďauke da cutar ulcer✅️
Akwai nau'o'ikan gyambon ciki guda bakwai✍️
1-Peptic And Gastric Ulcer.✅️
2-Esophageal.✅️
3-Arterial.✅️
4-Diabetic food.✅️
5-Venous jijiyoyi.✅️
6-Genital- Al-aura.✅️
7-Mouth.✅️
Ya Danganta da wurin da gyambon yake saboda alamun cutar yahaɗa da ciwo, tashin zuciya, ƙwannafi, ko ƙaiƙayi. Da dai sauransu amma ita kwayar cutar akan iya samunta aguri mai yawa ajikin mutun kamar yanda nayi bayani abaya wato (HELICOBACTER PYLORI) H-PYLORI❌️
2-➡️Ita kuma Gastric Ulcer: Ana samunta acikin nau'in abinci amma wasu suna samunta ta sanadin shan magunguna na CHEMIST kamar yanda nayi bayani abaya. Wasu kuma yakan kasance idan sun kamu da cutar ulcer kuma ulsar takasance PEPTIC ULCERCE to sai dalilin yawan amfani da waýannan abubuwa sai ya haifar musu da Gastric Ulcer.✅️
Alamun cutar ulcer! Tana ďauke da alamu kamar haka!⬇️
1- Jin zafin zuciya❌️
2-Yawan faďuwar gaba.❌️
3-Jin ciwon ciki.❌️
4-kyarnafi.❌️
5-Tsinkewar bahaya.❌️
Dadai sauransu. Wannan atakaice kenan.🙏
3-➡️Babu wani banbanci tsakanin Gastric ulcer da Peptic Ulcer dukkansu ulcerne saboda dukkansu Kwayar cutar Helicobater pylori shine yake hai far dasu ta sanadin ulcer.
Misali: Ulcer tana samuwa ta silar kwayar cutar HELICOBACTER PYLORI sannan su kuma GASTRIC ULCER da PEPTIC ULCER sun samune ta Rabe raben yanda cutar ulcer take. Wato yanda kwayar cutar take rarrabuwa.
4-➡️Wasu dayawa sukanji ciwon baya wanda har yakan kaisu suyi ta faman neman magani amma kuma wannan ciwon bayan ulcerne. Sau dayawa mutane suna rena cutar ulcer amma babu shakka cutar ulcer tana ďaya daga cikin manya manyan cututtuka masu lalata ainashin lafiyar ďan adam.
5-➡️Ana samun mutane dayawa da cutar ulcer amma tana matuqar rikitasu kuma ulcerce, dalili kuwa shine! Ana samun mutun da nau'in Gastric Ulcer da kuma nau'in Peptic ulcer wanda sanadin haka idan mutun bamai yawan bincike bane sai yakasa samun magani ko waraka akan wannan cutar✅️
Shawara.
6-➡️Mutun yayi koqarin sanin wacce nau'in ulcer ce ke damunsa saboda idan aka samu nau'inta dayawa ajikin mutun hakan sai yahana shi samun waraka. Kayi koqari likitanka yagane wacce ulcer ke damunka cikin nau'in ulcer ta yanda zaka kare kanka daga ita.
7-➡️Kar kabari sai cuta yagama illata jikinka tukun zakaje gun likita ko gurin masu maganin Islamic medicine. Kayi koqari kanemi magani asanda yadace. Ngd.
0 Comments