Ba wai ana azumi ne kaɗai don a daina ci da sha (azumin baki) ba, ko don a horar da mu da yunwa, a'a; dukkan gaɓɓanmu, harshe, ido, kunne, hannu... suna azumi.
• Azumin harshe (magana) shi ne kamewa daga zantuka marasa ma'ana, ko na haramci; kamar ƙarya, ƙazafi, gulma da yasassan zance (mis. jayayya akan kwallo ko siyasa), sai dai zikiri da ambaton kyawawan kalmomi.
• Azumin ido (gani) shi ne kiyayewa daga kalle-kallen haramun a zahiri (kallen ƴan mata a titi) ko a cikin wayoyinmu, shiga shafukan baɗala sa fitsara a cikin wayoyi.
• Azumin kunne (ji) shi ne kiyaye sauraron haram, raye-raye da kaɗe-kaɗe, gulmace-gulmace, laɓewa da jin sautukan 'yan mata (wanda ba ajnabiyya ba), sauraron zantuka marasa ma'ana da sauransu.
• Azumin hannu (taɓawa) shi ne kiyaye taɓe-taɓe, ko sata, ko taɓa kayan wani ba tare da izininsa ba.
• Azumin ƙafa (tafiya) shi ne kiyaye takawa zuwa wajen alfasha (saɓon Allah); sai dai wurin aiyuka na halal, masallaci ko wuraren tunatarwa.
• Azumin hanci (sansani) kiyaye shaƙar kayan maye ta hanci.
• Azumin zuciya (tunani da ƙulle-ƙulle) shi ne ka riƙa tunatar da kanka alheri, ka guji ƙullatar kowa, ko ajiye sharri a ƙarƙashin zuciyarka.
Idan tunaninka azumi kamewa daga ƙin ci da sha ne kaɗai, Manzon Allah ce wa: "duk wanda bai bar maganar zur ba (alhalin yana azumi), ba ruwan Ubangiji da yunwa da kishirwarsa" (Bukhari, 1903).
Babu ma ma'ana, idan kana tunani wai an wajabta azumi don a yi wa wasu horo da yunwa. Azumi makaranta ne da ƙara samun kusanci da tsoron Allah, darussan kamewa daga alfasha, yawaita ibada, jinƙai da tausayi da aka koya, ana so a ci gaba yi har bayan Ramadhana.
✍️Aliyu M. Ahmad
22nd Sha'aban, 1444AH
14th March, 2023
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #GuzurinRamadhan
0 Comments