Amfanin'Ya'yan Kankana


Mutane da dama basu san amfanin dake qumshe da 'ya'yan kankana ba, Kankana abin sha ne, magani ce, 'Ya'yan da ke a cikinta maganine, akan Haka ne muka ga ya dace mu gabatar da binciken masana Kan amfanin 'Ya'yan Kankana ga lafiyar bil'adama.

Duk lokacin da ka sha kankana to ka daina yada qwallan, maimakon haka sai ka tarasu a waje daya ka wanke ka shanya a rana har su bushe, ko ka siyo wadanda ake siyarwa a herbal medicine store. Zaka dauki qwara 20 zuwa 30 sai ka nike su, har sai sun koma gari (powder), sai ka nemi ruwa misalin liter daya da rabi ka zuba garin ka tafasa sai ruwan ya tafasa, Shikenan hadin ya kammala.


Yadda ake sha:

Zaka sha sau daya a kullum amma zaka dakata a duk bayan kwana uku, Idan ka sha na kwana biyu to a ran na uku ba zaka sha ba, sai washe gari. A haka zaka rinka yi har zuwa wani lokaci ya danganci ciwon da ake son magancewa da kuma jimawar matsalar ko ciwon da ke jiki.

Magungunan da yake yi

🍉•Domin samun zuciya mai koshin lafiya da rage yawan wasu wasi.

🍉•Maganin yawan zancen zuci.

🍉•Karawa garkuwar jiki karfi da kuzari.

🍉•Samun maniyi mai rai da maganin karamcin haihuwa ga namiji.

🍉•Gyaran ciki da hanji da wankin dattin ciki.

🍉•Yana haskaka fatar jiki ta yi kyau da sheki

🍉•Yana taimakawa don saurin warkarda gyambo ko wani rauni a jiki.

🍉•kariya daga barazanar kamuwa da ciwon Sugar. Idan kana fuskantar wannan barazanar to ka jarraba wannan maganin.

🍉•Rage nauyin jiki da qiba.

🍉•Maganine ga masu fama da anemia.

🍉•Yana lausasa bayan gari mai tauri ko karfi dake fita kamar na dabbobi.

🍉•Rage kumburin hanji, kumburin ciki, kumburin jiki da sauransu.

🍉•Samun karfi da kuzarin kasusuwan jiki.

🍉•Yana samarda jini ga jiki 

🍉•Yana wankin Koda da sauran datti.

🍉•Maganin ciwon jijiyoyinjin jiki.

🍉•Yana kare jiki daga barazanar yiwuwar kamuwa da ciwon daji.

🍉•Yana wargaza tsakuwar koda.

Wannan kadan ne cikin irin alfanun 'Ya'yan Kankana ga lafiyar jiki.



SHARE THIS Facebook    


Post a Comment

0 Comments