Abunda Zaki Idan Kanada Sha'awa Mijikin Kuma Baida Shi:
#Tsangayarmalamtonga
SHARE 🍉
Mata dayawa sukan shiga damuwa, wasu ma su bata rai, akwai wadanda hakan yakan zamo masu matsala a lokacinda suke da bukatan mazansu su kuwa mazan basu da bukatarsu.
Duk kuwa da ana samun matan da mazan ke da bukatansu su kuma a wannan lokacin basu da bukatan mazan nasu. Sai dai hakan yafi yawaita ne ga maza ganin sune mafi akasari suke shiga yanayin da sha'awar Jima'i yakan dauke musu.
Gajiya, bacin rai, fargaba, rashi da zullumi duk wadannan sukan iya kwantarwa mutum sha'awar sa na Jima'i, wanda akasarin wadannan yanayin sunfi shafar maza.
A duk lokacin da mijinki ya dawo ya nuna miki alamu ko kai tsaye bai da sha'awar Jima'i gashi ke kuma kina hannu, kada ranki ya baci ko ki yi fushi da shi. Ko ki soma zargi ko furta kalamai marasa daraja ga mijinki kamar yadda wasu matan suke yi. Ga wasu dabarun da zaki gwada domin janyo hankalin mijinki cikin sauki nan.
1: Sashi Yayi Wanka: Kasala na daya daga cikin abubuwan dake kwantarwa namiji sha'awar Jima'i. Don haka da zaran kin fahimci mijinki ya shigo jikinsa a mace, yi kokarin tanadar masa abunda zai yi wanka da shi.
Idan kuma daman kayan wanka na zamani kuke da shi a gidanku. Jawo hankalinsa ya zuba ruwa a jikinsa domin samun karfi a jikinsa.
2:Shirya Masa Kayan Shayi: Yana fitowa daga wanka abu na gaba da zai sa mijinki ya warware shine shayi mai dumi kamin ko bayan cin abinci ko kuma lokacinda yake cin abinci.
Kada ki sake ki hada masa shayi da madara muddin ba za a saka masa nascafe bane a cikin shayin. Domin shi madara zalla a shayi yana kara kashe jiki ne ga mutumin dake son yin bacci mai dadi. Don haka Lipton tea ko hadin nascafe shine abunda zaki hadawa mijinki.
Lipton tea ko cafe suna kara kuzari a jiki, kuma su gusar da gajiya ko kasala da mutum yake ji sannan su tsaiwaita masa lokacin da bacci zai dauke shi. Kinga anan kinyi hanyar da dole sai ya dauki lokaci kamin bacci ya dauke shi.
Idan kuwa shi ba mai shan shayi bane, to akwai lemun kwalba ko na gwangwani dake kara kuzari irinsu power horse dama na leda irin su passion kina iya zuba masa cikin ruwan da zai sha bayan cin abinci domin ya watsake.
3: Tausa: Cikin dabarunki na motsa sha'awar miji ya kwantar miki da naki sha'awar shine ki masa tausa.
Kina soma yi masa tausan ne tun a lokacinda yake zaune yana cin abinci ko shan shayi.
Wuyansa, kansa da kuma kafadunsa sune abun maida hankali wajen yi masa tausa a wannan lokacin. Daga nan idan doguwar kujerace daku kuma akwai sarari mike shi akai. Idan kuma babu halin hakan nan jawo shi cikin daki. Ki tabbatar a kwabe yake ki soma masa tausar a ruf da ciki.
Ki kasance mai kwantar masa da hankali idan da wata damuwa ce ya shigo, idan kuma da gajiya ce nan ma kina masa tausan kina masa kalamai masu ratsa zuciya cikin tattausar murya.
A lokacin da zaki juwoshi ya dawo ringingine tuni ya riga ya hada gora gabansa ya mike. Cikin sauki da kwanciyar hankali ba tare da bacin rai ko fushi ba ya zo hannu sai kuma yadda kika yi da shi daga wannan matakin.
Akwai matan da kai tsaye suke nunawa namiji suna bukatarsa ba tare da wasu dabaru na motsa shi ba, hakan zai yi wahala da fatar baka kadai ki motsawa namijin da bai da niya da kuma sha'awar Jima'i sha'awa.
Haka nan akwai wasu mazajen duk wannan matakin na 1 zuwa na 3 bai kamasu cikin sauki, idan mijinki hakan yake, to akwai mataki na 4 zuwa na 6 da babu namijin da ya isa ya tsallakesu muddin mace zata kafamasa wadannan tarkon ko wanene shi kuwa zai fada. A darasi na gaba zamu kawo su.
Da fatan mata zasu yi amfani da wannan dabaran a lokacinda suke da sha'awar Jima'i kuma suka fahimci mazansu su shigo da alamun basu da sha'awa a wannan daren.
Darasi na gaba, zamu kawo dabarun da maza zasu yiwa matansu da basu da sha'awar Jima'i a lokacinda su kuma suke cike da shi.
#Tsangayarmalamtonga
0 Comments