Mene ne zogale?
Daga bbchausa.com
Zogale ko Zogala (Moringa oleifera) Zogale na iya girma ya kai tsayin bishiya, amma a ainihin tsarin "daga tsirrai na duniya" (ICBN), yawancin zogale ba ya girma har ya kai girman bishiya.
Shi tushen zogale yana daya daga cikin tsirran masu albarka kasancewar bincike-binciken kimiyya sun tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama na inganta lafiyar dan Adam.
Zogale ya kunshi wasu sinadaran da ke warkar da cututtuka kamar ciwon suga, hawan jini, da yawancin cututtukan da wasu irin kwayoyin halittu wadanda idon mutum ba ya iya ganinsu.
Wasu jama'a na cewa cin zogale ko yin miyar shi ko shan sa kamar shayi gami da shan ruwan shi, na yin sanadiyyar samun waraka daga cututtukan da aka ambata a sama, dama wasu wadanda ba'a ambata ba.
Sun kuma yi imani Zogale na kara lafiyar jiki, kuma yana daga cikin nau'in abincin da masu shekaru 40 zuwa sama ya kamata su rika ci domin yana taimaka wa garkuwar jiki.
Moringa plants are packed with vitamins, amino acids, anti-oxidants and protein.
Ganyen zogale na dauke sinadarai masu gina jikin dan Adam
BBC ta mika wannan tambaya ta shi ko zogale ya fi kaza ga wani kwararren likitan.
Ya ce zogale na da amfani sosai a jikin dan Adam kamar yadda kayan lambu, saboda yana da wasu sinadarai da ake kira "micro-nutrients" da turancin Ingilishi.
Wadannan sinadaran na taimakawa wajen gina jiki da karin jini da abubuwa kamar inganta lafiyar fatar jikin dan Adam."
Likitan ya kuma ce akwai wasu abubuwan, "da ke rage aukuwar cututtuka kamar ciwon siga da hawan jini da kuma kansa, wada ake kira ciwon daji da Hausa."
Makomar mutanen da ba sa cin nama ko kifi
Likitan ya tabo al'amari mutanen da samsam ba sa cin nama ko kifi, wadanda suka koma cin kayan lambu da ganyayyaki kawai.
"Irin wadannan kayan lambun na taimakawa wajen gina jiki da kara masa karfi. A wasu lokutan, za ka ga cewa mutanen da ba sa cin nama ba sa yin kiba sosai domin kiba na haddasa ciwon siga da hawan jini da ciwon zuciya da sauransu."
A kan iya nika kwayoyin zogale kuma a barbada shi kan abinci
Rukunin mutanen da ya fi dacewa su ci zogale
Likita ya kuma kara da cewa dukkan mutane na bukatar kayan lambu:
"Babu wanda ba ya bukatar cin kayan lambu, har da ni da kuma kai ma. Kuma zogale na cikin kayan lambu mafi amfani".
Ya kawo misalin mutanen nahiyar Asiya kamar kasar Indiya, wurin da za a sami jama'a da ba sa cin nama, kuma ya ce babu lahanin da wannan halayar ke wa jikinsu.
Sai dai ya ce ba kowa ne ya kamata ya daina cin nama ba.
"Akwai wasu mutane kalilan da idan suka ci kayan lambu suke bata mu su jiki saboda wata matsalar rashin lafiya da suke fama da ita. Sai dai ba su da yawa cikin al'umma, domin ba su wuce mutum biyu cikin 100 ba."
Likitan ya kuma kawar da wani batu da wasu ke ikirari cewa cin nama kamar na kaza ba shi da amfani a jikin dan Adam.
"Ba a ce kar mutum ya ci nama ba, amma babu kyau mutum ya ci abincin da ya cika maiko, kuma naman kaza an san yana da maiko sosai. Saboda haka ne ya kamata a rika rage yawan nama kamar na kaza da danginsu masu maiko."
Ya ce yadda ake sarrafa naman ma na iya yin tasiri, domin idan aka dafa naman har dahuwar ta wuce kima, sai naman ya kasance babu abin da za a karu da shi, domin dukkan sinadaran da ke cikinsa sun kone.
Yadda ake sarrafa zogale
Likitan ____ ya ce zogale da sauran kayan lambu ba sa bukatar a dafa su sosai, domin wannan na sa su rabu da dukkan abubuwa masu amfani da ake fatan samu a cikinsu.
"Kyawun lamarin shi ne a tafasa su sama-sama, saboda dafa su sosai na iya zama asarar sinadaren da ke cikinsu."
Ya kuma ce babu wasu ranaku ko lokutan da suka fi dacewa a ci zogale ko ma kayan lambu.
Amma ya ce a yi hattara wajen cin naman kaza har ma da sauran nau'i na nama saboda dalilan da ya bayyana a baya.
Dukkan mutane na bukatar kayan lambu
Nutritionist...
To an kuma tambayi wata kwararriya kan amfanin abinci a jikin dan Adam, wadda ta fara da fayyace abin da yasa wasu ke cewa zogale ya fi nama.
Ta ce kowane nau'in abinci ko abin sha na dauke da wasu sinadarai masu tasiri kan amfani ko illa ga jikin dan Adam.
"Binciken masana ya nuna cewa zogalle na dauke da wadatattun sinadarai masu matukar muhimmanci da suka hada da sinadarai masu samar da kuzari da ake kira micro-nutrients da turancin Ingilishi."
Ta ce akwai kuma wasu sinadaran da ake samu a zogale da ke da muhimmanci wajen kare jikin dan Adam daga kamuwa da cututtuka. Su kuma ana kirasu da "phyto-chemicals ko kuma phyto-protectants".
Ta ce idan dan Adam ya "kawar da batun dandano da kuma abin da idanunsa ke iya kallo na tasirin kaza ga jikin dan Adam, za mu iya cewa cin zogale ya fi cin kaza."
Ita ma ta ce ya dace kowane mutum ya rika cin zogale akai-akai.
"A kowane mataki na rayuwa, daga karamin yaro har zuwa ga babban mutum, babu wata illa idan suka rika cin zogale, sai dai akwai wadanda aka so su fi mayar da hankali kan cin zogale da kayan lambu - kamar masu fama da ciwon suga, kasancewa shi zogale yana rage yawan sinadarin suga a cikin jini."
Sai dai ta ce ita ma kaza na da amfani sosai a jikin dan Adam ganin cewa tana dauke da wasu sinadarai kamar na "protein" da ke taimakawa wajen gina jiki.
Ta bayar da shawara ga masu cin zogale kan hanyar da ta fi dacewa a rika sarrafa shi kafin a ci.
"Ana iya yin kwadonsa, ko a yi dambu da shi ko kuma a saka shi cikin akamun kananan yara masu fama da yunwa. Wani binciken ya nuna cewa wasu kamfanoni masu yin alawa na amfani da zogale wajen inganta alawar."
Wanne ya fi tsakanin kaza da zogale?
Kan batun cikin zogale da kaza, wanne ya fi dacewa a rika ci kullum, sai ta ce babu laifi a ci wadannan nau'i'kan abincin a kullum, ta garagadi mutane kan adadin da ya dace ya rika ci.
"Misali ba daidai ba ne a ce mutum ya tasa zogale ya take cikinsa, ko ya tasa kaza guda, a ce kullum sai ya ce kaza guda, wannan zai iya haifar wa mutum matsala."
Amma ta ce kar mutum ya ci zogalen da yawansa na wuce gram 70, wanda shi ne yawan da zai amfani jikinsa.
0 Comments