MAGANIN CIWON HANTA FISABILILLAHI:



MAGANIN CIWON HANTA FISABILILLAHI:



Ciwon hanta na daya daga cikin manyan ciwuka da suke da wuyar magancewa a duniya amma da Yardar Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi za’a samu waraka.

*ALAMUN CIWON HANTA*

Akwai:

❛ Matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai.

❛ Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani.

❛ Yawan haraswa da kuma tashin zuciya ko da mutum ruwa ya sha.

❛ Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi ,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.

Ga duk Wanda ya ji wadannan alamu sai ya yi kokarin zuwa asibiti domin Gwaji.

A daina tsoron gwaji domin magance cutar na farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta.

Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan haraswa da tashin zuciya suna magani ba sujin sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin takan hadu da masu ulcer sosai.



MAGUNGUNAN DA ZA A YI AMFANI DA SU.

1. A samu garin habba cokali 10.

2. Garin Sidir cokali 5.

3. Garin Tin cokali 5.

4. Garin bawon kankana cokali 10.

5. Garin Citta cokali 1.

6. Garin tafarnuwa cokali 1.

7. Garin Hidal cokali 5.

8. Garin zogale cokali 3.

9. Garin Yansun cokali 6.

10. Garin Raihan cokali 6.

11. Garin Kusdul Hindi cokali 6.

YADDA ZA A HADA SU

Sai a hada su waje daya a samu Zuma lita biyu mai kyau sai a zuba ciki a juya ya hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.

Fadakakarwa

A guji amfani da nama musamman Jan nama da sauran abun da mai ciwon hanta baya bukata.

Kuma ga yadda abun yake:

1- Zuma tana kunshe da Sinadarai masu karfi wadanda suke da saurin Murkushe kowacce irin kwayoyin cuta acikin kankanin lokaci.

Kuma tana kunshe da wani Sinadari wanda yake taimakawa naman jikin hantar mutum ya sake tsirowa, ya maye gurbin wanda cutar Hepatitis din ta lalata.

2- HABBATUS SAUDA – tana kunshe da Sinadarai na maganin kusan dukkan cuttuttukan da zasu iya shiga jikin Dan Adam.

Sannan tana kunshe da wani Sinadari na Musamman wanda yake da tasiri wajen dawo da Qarfi da Kuzari adukkan gabobin jikin Dan Adam, tare da taimakawa wajen tsaftacewa Jinin jikin ‘Dan Adam.

3 – TAFARNUWA – ita ma ANTI BIOTIC ce wacce al’ummomin duniya sukayi dubunnan Shekaru suna amfani da ita amatsayin magani.

YADDA ZAKA YI.
****************
Ka samu Zuma kofi 2. Ka zuba Garin H/sauda cokali 10, garin Tafarnuwa cokali 2, garin Citta cokali 2.

Ka gaurayasu ka ajiye. Kullum da safe ka rika shan Cokali 3, idan ya rage 30 mins kafin kayi breakfast (wato karyawar safe).

Hakanan da yamma ma zaka rikayi. Zaka ci gaba dayi har sai lafiya ta samu.

Fatan mu shine har kullum Allah ya ba ku lafiya mai dorewa.


FOLLOW

Post a Comment

0 Comments