FA’IDOJIN KUSDUL HINDI :



FA’IDOJIN  KUSDUL HINDI :


*kusdul Hindi:*



Nau’in Itace ne da labarawa da mutanen Sin da sauran Kasashen yankunan ke amfani da shi acikin abinci tare da maganin cututtuka da dama.

Shi *Kistul Hindi* yana zuwa ne a kasashenmu na yammacin Africa a nau’i na gari, amma inda ake sarrafashi zaka same shi a nau’uka daban-daban.



Shiyasa zanyi bayani akan Garinsa saboda shi muka fi sani tareda sauqin samunsa.

Shi *GARIN KISTUL HINDI* Yana magance cututtuka dadama kamar:

*Ciwon mara yayin al’ada, daidai ta haila, magance dafi na wuka ko na maciji, kunama dss, maganin kumburi ko rauni, maganin aljani, sihiri, karfin maza, tsutsar ciki, magance matsalolin ciki.* dasauransu.

*YADDA AKE SARRAFASA:*

1. DOMIN MAGANCE MATSALAR HAILA, CIWON MARA, TSUTSAR CIKI, SIHIRI, DA MATSALAR ALJANI (ISKA) SAI ADEBI COKALI 5 NA GARIN KISTUL HINDI SAI GARIN HABBATUSSAUDA COKALI 3 SAI MAN ZAITUN COKALI 7 SAI GARIN ZAITUN COKALI 3 SANNAN AGAURAYESU AZUBA ZUMA KOFI DAYA KARAMI AKARA CAKUDEWA. ANEMI WURI MAI MATSAKAICIN YANAYI A AJE ARIKA SHAN COKALI 3 SAU 3 ARANA.
MAFI KARANCIN SHAN MAGANIN KWANA 3 ZUWA 7 GA MASU LARURAR AL’ADA KO MATSALAR ALJANI.



2. GA MASU SON KARIN KARFIN MAZA KUMA SU SAMU GARIN KUSDUL HINDI SU HADA DA NONON RAKUMI KO ZUMA SU MOTSE SU RIKA SHA IDAN ZASU KWANTA.

ANA KUMA ZUBA KIMANIN COKALI 1 ABAKI SAI ABI DA RUWA ASHANYE.

3. MATSALAR DAFI KUWA SHIMA ANA HADIYAR GARINNE DA RUWA KO AHADA DA ZUMA KO NONO NA SHANU ASHA.

HAKA KUMA GA MAI RAUNI KO YANKEWA ZAI IYA SHANSA KAMAR YADDA MUKA AMBATA HAKA KUMA ANA TAFASA RUWAN ZAFI DA GARIN AWANKE INDA DAFIN YAKE KO GASAWA KO KUMA ANEMI MAN ZAITUN AKWABA DA GARIN ASHAFE GURIN.

DA IZININ ALLAH ZA’ASAMU FA’IDAR MAGANCE WADANNAN CUTUTTUKA DA AMFANI DA GARIN KISTUL HINDI.

Allah yasa mu dace.

Post a Comment

0 Comments