TAMBAYA TA 2914
*******************
Assalama Alaikum. malam matar aure ce tana son mijinta ya sadu da ita, amma sai taga yana jin bacci sosai saita biyawa kanta bukata harta fitar da maniy.To bayan ta kwanta sai tayi mafarki shima ta farka taga maniy.To idan ta tashi wanka daya zata yi ko biyu?.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Janabah ce ta sameta ta hanyoyi biyu daban-daban amma dai hukuncinsu daya ne. Wanka ya wajaba akanta. Kuma wankan guda daya ya isar mata.
Sai dai gaskiya ta aikata babban kuskure ko laifi wajen biyawa kanta bukata din nan.
Buyawa kai bukata (istimna'i) haramun ne bisa nassin Alqur'ani mai girma. Allah Madaukakin Sarki yana fa'dar siffofin bayinsa muminai mutanen kirki, sai yace. :
"DA WADANDA KE KIYAYE FARJOJINSU, SAI DAI BISA MATAYENSU KO ABINDA DAMSHINSU YA MALLAKA (WATO KUYANGI).
DUK WANDA YA NEMI WANI ABU BAYAN WANNAN, TO (WADANNAN) SUNE MASU QETARE IYAKOKI".
Wato duk namiji ko macen da yake biya wa kansa bukata, ta hanyar da ba saduwa da matarsa ta aure ko mijinta na aure ba, to hakika ya Qetare iyakar da Allah ya ajiye masa.
Mafiya rinjayen Maluman Fiqhu sun tafi akan haramci wannan aikin, in banda Mazhabin Hanafiyyah su ka'dai sukayi sassauci akan wannan mas'alar suka ce makruhi ne.
Sannan kuma yin wannan abun yana iya janyo miki matsaloli ta fuskar lafiyarki. Kamar daskarewar maniyyi, ciwon mara mai tsanani, rikicewar tunani, ciwon makanta, rikicin jinin haila, da sauransu.
Ya zama wajibi kiji tsoron Allah ki dena biyawa kanki bukata. Idan sha'awa ce ta dameki, gara ki tashi mijinki koda barci yakeyi, kin san hanyoyin da zaki bi kija hankalinsa domin samun biyan bukatarki.
Sannan kiji tsoron Allah ki guji kallon finafinan batsa ko karanta labarun batsa domin suna iya zama dalilin watsewar tarbiyyarki.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (02/01/1443 11/08/2021)
0 Comments