KADA KI AURI WANDA YAKE SONKI SABODA
•••KYANKI•••JIKINKI•••KYAN SURARKI•••
Saboda Dalilai kamar haka:
• Duk lokacin da yaga wacce tafiki kyau, to zai manta da naki kyan, ya fara kwaɗayin bin wata.
• Daga lokacin da fuskarki ta sami matsala, ko wani accident ALLAH yakiyaye, to amfaninki yaƙare agurinsa, domin dama kyan fuskarne yaja hankainsa, kuma agabanki zai rink waya da wasu.
• Daga lokacin da kyan naki ya gushe, tsufa ya fara kamaki, to shikenan, zakiga rashi kulawa da wulakanci, kuma a gabanki zai rinka waya da wasu.
• Daga ya kusanceki na ɗan wasu lokuta, to shikenan baki da wata daraja a idonsa, saboda yasan sirrin abinda yaja hankalinsa gareki, har ya aureki, kuma zai fara ƙoƙarin bin wata a waje daban.
• Daga lokacin daya sanki a 'ƴa mace, to shikenan, bakida sauran wata daraa, kuma babu wata soyayya da zaki kara gani, ƙoƙari zaiyi yakaiwa wata hari wacce take da wani abu wanda ke baki dashi.
• Daga lokacin da namiji ya aureki saboda sha'awa kawai, to lallai zakiga wulaƙanci bayan biyan bukatar tasa, anan take zakia canja miki, fuska.
• Daga lokacin da namiji yake buƙatar mace, yafi kowa iya sakin fuska da ladabi, amma yana samun abinda yakeso shikenan.
• Ina kira izuwa garemu maza, muji tsoron ALLAH, dukkanmu zamu haɗu da ALLAH,
• Kuma kowa yana samun sakamakon aurensa a gurin ALLAH ne abisa niyyar dakayi auren dominta.
• A duk lokacin da kaje gurin ƙanwar wasu ko 'ƴar wasu da niyya mara kyau, to kaima hakan zai faru da taka ƙanwar ko 'ƴarka.
• Idan ka ɓata 'ƴar wasu da kuɗi masu yawa, to kai kuma taka 'ƴar a kyauta za'a lalatata, kuma kana cikin ƙabarinka, sakamakon abinda take aikatawa yana samunka har izuwa filin alƙiyama.
• Idan kana tsoron haɗurwarka da ALLAH, kana fatan ka kwanta a ƙabarinka lafiya, kana fatan ka shiga aljannah cikin sauki, to kayi soyayya dan ALLAH.
Yaa ALLAH kasa muso junanmu danka, dan rahmarka dan girmanka, dan neman yardarka.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
0 Comments