'BARKA DA SHIGA SABUWAR SHEKARA' HALAS NE KO BIDI'A?
- Kabir Abubakar Asgar
A ɗan ƙaramin leƙe-leƙena, ban ga wani malami cikin magabata na ƙwarai da ya yi magana akan hukuncin barka da shigowar sabuwar shekarar musulunci ba. Wataƙila saboda mas'alar ba ta faru ba a zamanin magabatan.
Malami mafi daɗewa da aka hakaito cewa ya yi fatwa akai shine Alƙali Najmuddeen Alƙamuliy (727) wanda aka ce ya ce ba komai, halas ne. Sai kuma wani malami mai suna Abul-Hasan Al-Maƙdisiy.
A cikin littafin (الحاوي للفتاوي) Na Al-Imamus Suyutiy ya hakaito wannan magana daga wasu malamai tare da bayyana cewa shi a ganin sa halas ne.
An tambayi Al-Allamah Ibnul Uthaimeen game da yi wa juna barka da shiga sabuwar shekarar musulunci, sai ya amsa da cewa: "Ni ina ganin ba laifi akan yi wa juna barka da shiga sabuwar shekara. Amma fa ba addini ba ne. Ba za mu ce wa mutane ku dinga yi ba. amma in sun yi ba za mu ce da laifi ba. Sannan kuma ya kamata su dinga haɗawa da addu'ar Allah ya sa albarka a cikin sabuwar shekarar. Wannan shine ra'ayina akan mas'alar. Al'ada ce kawai, ba addini ba ce".
A wata fatawar kuma mai kama da wannan Uthaimeen ya ƙara da cewa: "In wani ya ce maka barka da sabuwar shekara ba laifi ka mayar masa. Amma kai ka da ka fara. Ba shi cikin Sunnah mu ƙirƙiri wata sabuwar ɗabi'a ta yaɗa saƙonnin barka da shiga sabuwar shekara".
Shi kuwa Sheikh Salih Al-Fauzan da aka tambaye shi game da hukuncin barka da sabuwar shekara sai ya ce: "Ni ban san inda aka samo haka a cikin Shari'a ba. Sannan kuma shi lissafin kalandar hijira ba a nufaci amfani da shi don a ce wai farkon sa farkon shekara ba ne wanda za a dinga murna ana barka da kewayowarta. Shi lissafin kalandar hijira an yi shi ne don a tantance lissafi da kwanan wata. Umar ne ya kafa wannan tsari bayan shawara da Sahabbai don samar da tsarin tantance lissafin lokacin da aka aiko da wasiƙa da lissafin lokacin gudanar da sauran al'amuran gwamnati. A lokacin akwai lissafin kalandar miladiyya amma suka ƙi aiki da ita, suka fifita amfani da hijira wajen lissafin su. Amma ba wani a cikin su ko na bayan su da ya mai da wannan lokaci a matsayin lokacin biki ko murna ko yi wa juna barka. Saboda haka barka da shiga sabuwar shekara bidi'a ne".
Wannan magana ta Malam Fauzan tana da ƙarfi ƙwarai. Musamman in aka lura da cewa riƙo da wata rana a shekara ana yi wa juna barka da kewayowarta zai ba wannan rana damar ta shiga cikin lissafin ranakun idi ba tare da dalili ingantacce ba.
Baya ga cewa ita wannan al'adar ta samo asali daga al'ummomin da ba musulmi ba, wanda kuma addinin musulunci ya zo da hani game da koyi da su.
Sai kuma toshe kafar ɓarna, ba shakka in aka buɗe ƙofar halasta wannan al'ada to hakan na iya ba da damar zaƙewa; kafin a ankara musulmi za su shiga bikin murnar sabuwar shekara gadan-gadan, mai yiwuwa su fara aikawa da saƙonni da bayar da sanarwa a kafafen watsa labarai da ƙirƙirar tarurruka da bukukuwa da kuma riƙo da ɗaya ga watan Muharram a matsayin ranar hutu. Daga nan kuma sai su tsallaka zuwa sauran bukukuwan ranar kaza da ranar kaza.
A taƙaicen taƙaitawa, abin da ya fi zaman lafiya ga Musulmi shine ya guje wa wannan al'ada ta murna da biki da barka da sabuwar shekara.
A tuna faɗin Manzon Allah (SAW) a cikin Hadisin Ahmad da Tirmiziy da Nasa'iy daga sahabi Hassan Ɗan Aliyu ya ce: "Na kiyaye faɗin Manzon Allah (SAW) cewa ka bar abin da ke maka kokwanto zuwa ga wanda ba ka da kokwanto akan sa".
Allah shine mafi sani.
0 Comments