Wasu Kalmomin Da Zaka Furtawa Mace Idan Ka Kamu Da Sonta:


Wasu Kalmomin Da Zaka Furtawa Mace Idan Ka Kamu Da Sonta:

SHARE 💕
#TsangayarMalam 

Rashin iya kalamai masu dadi na sa maza da dama rasa 'yan matan da suke nema da aure.

Duk wata mace nason jin mai sonta ya na sakar mata kalamai masu dadi kuma na kambamawa. 

Ga wasu kalaman da zaka furtawa macen daka kamu da sonta domin kara cusa mata kaunarka a zuciyarta.

 
1: Allah Ya miki kyau...... (Sai ka fadi wajen)
2: Duk shigar da kika yi yana burgeni. Kayan suna dacewa da jikinki.
3: Kasancewa dake na yaye mini bakin ciki da bacin rai. Kina faranta mini rai. Kina sani annashuwa.
4: Bamu jima da haduwa ba amma tamkar munyi shekaru da sanin juna saboda yadda kika fahimceni.
5: A Kullum burina bai wuce kasancewa dake ba. Ina son ganin ranar da zaki zama tawa halas malak.
6: Murmushinki yana bayyana mini sa'ar da nayi wajen zaban macen aure. Dariyarki na tambatar mini da dacen da nayi wajen haifan kyawawa 'ya'ya.
7: Kina da bambamci da sauran matan wannan zamani ta bangaren.............. (Ambaci bangaren).
8: Allah Ya amsa rokon dana masa na samun irin macen dana rokeShi kuwa.
9: Bana fatan ganin bacin ranki.
10: Ba zan iya rabuwa dake ba.
 
Wadannan Kalmomin na daban ne ga duk macen da zaka furta mata su. Haka nan kuma suna da matukar tasiri a soyayyar da kake yi da mace.

Da fatan maza musamman samari zasu rika amfani da kalaman da zasu kambama masoyansu da su.

Kada ka manta, ba wai kawai ka furtasu a baka kadai ba. Yi kokarin ganin ka aikatasu ta ga soyayyar da kake mata a zahiri bayan a furuci.

Post a Comment

0 Comments