Ka Kiyaye Abubuwan Nan Muddin Kana Burin Soyayyar Ka Ta Dore:


Ka Kiyaye Abubuwan Nan Muddin Kana Burin Soyayyar Ka Ta Dore:

SHARE 🤳
#TsangayarMalam 

Akwai mazan da suke yiwa soyayyar su rikon sakainar da aka kunsa kashi a ciki. Sai kuma bayan sun rasa soyayyar da ake musu sai kuma idanuwa su dawo su raina fata.
Muddin kana son soyayyar ka ya samu karbuwa wajen wacce kake so da aure to ka kiyaye wadannan abubuwan kamar haka:

 
1: Ka guji nunawa wacce kake so tamkar alfarma kake mata na soyayyar da kake yi da ita.

Akwai wasu mazan ganin mace na sonsu sai su rika nuna isa da gadara. Kiranta ma sai sun ga dama. Idan ta kira sai sun ga damar dauka.

Irin haka duk lokacin da budurwa ka ta gaji dare daya tana iya hakura da soyayyar taka ta fuskanci wani saurayin ta ajiye batunka har abada. Don haka idan kana soyayya da mace muddin da gaske kake nuna mata mahimmancin ta, da kuma ka darajata.

2: Idan kana son soyayyar da kake yiwa mace yayi inganci, kada ka zama mai riko. Kada ka zama mai yawan mita. 
Ka zama namiji mai yafiya, da kawo karshe lamari idan aka maka laifi ko sabamaka. 

3: Ka guji yiwa macen dake sonka karya.
Karya na sa namiji ya rasa soyayyar sa ko a yanzu ko nan gaba. Don haka duk abunda namiji zai yi akan soyaya kada ya sake ya shigo da karya cikin soyayyar sa.

4: Kada ka zama marowaci ko mai dunkulenlen hannu idan kana so soyayyar ka yayi tasiri a wajen budurwa ka. 
Rowa bayan zai iya jawo maka matsala a soyayyar ka. Zai iya kuma jawo maka kaskanci ga wacce kake so.

Ba sai ka rika bata kudi masu yawa ba. Sai dai yanada kyau ka zama saurayi wanda yasa ya kamata ba sai wacce kake so ta tambayeka ba.

5: Muddin kana son soyayyar da kake yiwa budurwarka yayi tasiri. Ka kasance kana da lokacinta. Rashin baiwa wacce kake so lokaci zai iya sa ka rasata. 

Yanada kyau duk wani namijin da yake soyayya ya daraja duk macen data bada soyayyar ta gareshi. 

Ya dace maza su sani, ba karamin sadakauwa mata suke yi ba wajen zaban namiji tilo cikin dubannin mazan da suka nuna sha'awar su gareta ba. Don haka mutunta wannan matsayin nata shi yafi.

Post a Comment

0 Comments