Illolin wasa da gaba, istim'nai wand ya kamata ku sani maza da mata.


Illolin wasa da gaba, istim'nai wand ya kamata ku sani maza da mata.


ILLOLIN AIKATA ISTIM'NAI WASA DA GABA(MASTURBATION ):


Shine masturbation istim'nai hanya ce da ake bi domin biyawa kai bukatar jima'i ba tare da anyi saduwa ba (intercourse) wacce mafi yawan samari da yan mata a wannan lokaci suka dauka hanya mafi sauki wajen gamsar da kansu ba tare da sun nemi mace ba.

Wanda a gefe guda yana da illoli da yake jawowa wanda ya dauki tsawon lokaci yana aikatawa,duk da masana sunce aikata shi yana da amfani ga lafiya da kuma jiki,amma yana cutarwa kuma cutarwar sa tafi amfanin sa.

Duk kuwa abinda illar sa yafi amfanin sa to ba shakka wannaj abu mai cutarwa ne kuma yana da kyau mutum ya kaurace masa,domin gudun fadawa halaka wacce zata kai kutum dana sani.


KADAN DAGA CIKIN ILLOLIN SA:


1. Yana jawo sanyin mara mai tsanani.
2. Yana jawo daukewar shaawa.
3. Yana jawo kankancewar gaba.
4. Yana jawo karancin maniy da tsinkewar sa.
5. Yana jawo rashin haihuwa.
6. Yana jawo raunin jiki.
7. Yana jawo yawan damuwa.
8. Yana jawo yawan mantuwa da dimuwa.
9. Yana jawo kurajen gaba.
10. Yana jawowa Namiji saurin kawowa.
11. Yana jawowa mace rashin gamsuwa da rashin jin dadin jima'i
12. Yana jawowa mace budewar gana da kwanciyar Nono
13. Yana jawo matsaloli na jinnu(Aljanu)

Da sauran su.

Wadan nan dai sune kadan saga cikin illolin aikata istim'nai.

KADAN DAGA AMFANIN SA A CEWAR MASANA.

1. Yana inganta barci.
2. Yana sakawa mutum nustuwa.
3. Yana hana mutum daukar Cututtukan jima'i.
4. Yana sa mutum ta dade yana jima'i bayan ya aikata shi kafin ya sadu da mace(masturbation before sex)
5. Yana kare hadarin kamuwa da cutar kansar furustuta (prostate cancer)

Kadan kenan daga amfanin sa wanda masana suka bayar.

Amma dai idan muka duba zamu ga illar sa yafi amfanin sa yawa,saboda haka ya kamata ku kiyaye.

Amma fa wadan nan abubuwa da kuka zayyana scientifically ko kuma a binciken masana na wannan zamani bai tabbatar istim'nai yana jawowa ba,suka ce mutane ne suke sawa a ransu cewa shine.

Amma muna nan daku lokaci zaizo da suka tabbatar da illar sa a kimiyance,fatan mu dai Allah yasa mu cika da Imani.

Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596

https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1

𝘀𝗶𝗿𝗿𝗶𝗻 𝗿𝗶𝗸𝗲 𝗺𝗶𝗷𝗶 

JOIN US TELEGRAM GROUP: 🏷️

Zamantakewar aure ga ma'aurata
https://t.me/sirrinrikemij

Post a Comment

0 Comments