Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan adam :


 Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan adam :
 
Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper.

 ‘yayan kankana wadan da ake kira da ‘tarbooj ke beeja’ yaren hindi, ana amfani dasu kamar a kasar Asia, a matsayi kayan abinci, inda a Najeriya kuma ake amfani da ita a cikin miya, inda man ‘ya’yan kuma ana amfani dashi a don gyara fatar jiki.

 
 Ga wasu daga cikin amfanonin ‘ya’yan kankana a jikin dan adam: 

1. ‘Ya’yan kankana suna water da jikin dan adam da sinadaran magnesium wanda ke taimakawa zuciya wurin harba jinni da kuma magance ciwon diabetis. 

2 .‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji. 

3. ‘Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam. 

4. ‘Ya’yan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa ‘ya’yan kankana 1litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi. 

5. ‘Ya’yan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.
 

6. Kusan fiye da rabin ‘ya’yan kankana na dauke da mai a cikinsu wanda kusan 20% sina darin Fat ne a cikin ‘ya’yan kankana wanda ke sanya girman jiki. 

7. Jikin dan adam na bukatar amino acids wanda jikin dan adam baya iya bayar da irin wadannnan sinadarai sai dai daga abinci idan mutun yaci.

 ‘ya’yan kankana suna da irin wadannan sinadarai masu karawa dan adam lafiyar jiki da karfi. 

Post a Comment

0 Comments