Amfanin Shan Ruwa Kamin Jima'i Ga Ma'aurata:
SHARE 📚
#Tsangayarmalamtonga
Shan ruwa ana daf da soma Jima'i yana da matukar amfani ga ma'aurata inji masana.
Masanan sun jero wasu alfanun da duk wasu ma'aurata zasu iya samu muddin dai zasu sha ruwa kamin su soma Jima'i.
1: Shan ruwa kamin Jima'i yana karawa ma'aurata karfin jiki.
Maimakon jin kasala ko nauyin jiki, kuna shan ruwa zaku samu kuzarin hawa gado.
2: Haka nan kuma shan ruwa kamin soma Jima'i yana tunkudo sha'awa. Koda kuda daga cikin ma'auratan sha'awar sa ko nata bai motso ba, dandakan ruwa zai iya motso dashi.
3:Har ila yau shi shan ruwa daf da soma jima'i yakan taimakawa jini ya kara samun gudana a jikin ma'aurata yadda zai kara musu kuzari da lafiyar saduwa.
4: Shan ruwa kamin soma Jima'i yakan rage warin gumin jikin ma'aurata a lokacinda suke tsaya da saduwa idan zufa ya keto musu.
Maimakon zufan jikinku ya rika fitowa da wari, idan kun sharuwa hakan bazai yiwu ba. Ko kuma zai ragu.
5: Zai taimakawa ma'aurata yin fitsari bayan kammala Jima'i.
Yanada kyau bayan Jima'i duk wasu ma'aurata su samu damar wanke mararsu ta hanyar fitsari. Hakan na iya taimaka musu wajen cire duk wani cuta da zai iya tsayawa a gabansu ko mafitsararsu. Don haka idan suka sha ruwa kamin jima'i suna kammala Jima'i zasu tsaftace maransu.
Sai dai kada ya zamanto cewa ma'aurata sun shan ruwan dayawa yadda zai cika musu ciki ya kuma hanasu katabu. Ruwa dai za a sha dan daidai ba sai an cika ciki ba.
0 Comments