Wasu Kurakuren Da 'Yan Mata Suke Yi Idan Saurayin Da Suke So Ya Gujesu:

Wasu Kurakuren Da 'Yan Mata Suke Yi Idan Saurayin Da Suke So Ya Gujesu:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga
 
Wasu matan sukan yi wasu kurakure a kokarisu na shawo kan samarinsu alokacin da suka gujesu haka nan kawai ba tare da wani laifi ba.

Muddin har namiji ya yanke shawran rabuwa dake, kada ki sake kiyi wadannan abuuwan domin dawo da soyayyarki:
 
1:Kuka: 
Kada ki sake kiyiwa saurayin daya gujeki ba tare da wani dalili ba kukan rabuwa dake. Koda zakiyi kukan saboda bacin rai kada ki bari wani yaji ko ya gani.

2: Bin Abokansa:
Kada ki sake kice zaka bi abokansa domin su masa magana ya dawo. Idan ma kina yawan gaisawa da abokanensa a wannan lokacin ki daina saboda kada ma wani cikinsu yace zai miki zancensa.

3: Bibiyansa A Shafukansa:
Kada ki sake ki rika bibiyansa a shafukansa na sada zumunta. Ki tabbatar da ki doɗe shi yadda bazaki riƙa ganin abubuwan da yake yi ba.

4: Ci Gaba Da Tunaninsa: 
Tabbas cireshi a rai a lokacin g isuda zai yi wuya. Amma hakan shine zai kare miki mutuncinki.
Ki tabbatar kin kauda duk wani abunda zai saki tunawa da shi a wayarki, a dakinki, a wajen aikinki ko a inda kike kasuwancinki.

5: Kin Baiwa Wasu Mazan Dama:
Wasu matan da zaran sun samu matsala da masoyinsu sai su yiwa maza kudin goro su daina kula maza da sunan duka haka suke, Wannan kuskure ne.

Kada kiyi saurin fadawa soyayya,kada kuma ki Hana wasu mazan damar sonki.
 
A duk lokacinda kika matsawa namijin da haka kawai yayi shawaran rabuwa dake dole ya dawo kuci gaba da soyayya da sunan kina sonshi. Zaki fiskanci matsalolin da suka fi na farko daga gareshi. Domin yanzu zai dauka idan babu shi bazaki iya rayuwa ba. Sannan mutuncinki zai zube a wajensa zai rika miki abunda ya gadama. A irin wannan lokacin ne zai bukaci yin zina dake saboda yasan bazaki ki ba.

Duk namijin da ya rabu dake kikayi banza da shi. Shine zai shiga damuwa musamman idan baki yi sake kin bashi gabanki ba. Koda kin bayar kada ki taba yada mutunciki.

Post a Comment

0 Comments