Samu Amsar Wadannan Tambayoyin 10 Daga Wajen Wacce Kake So Da Aure:


Samu Amsar Wadannan Tambayoyin 10 Daga Wajen Wacce Kake So Da Aure:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga
 
Akwai wasu bayanai da amsarsu wajen wacce kake so da aure suna iya karama karfi gwaiwa ko kuma sauya maka tunani. 
Cikin hikima, yiwa wacce kake son aurenta wadannan tambayoyin daya bayan daya, lokaci zuwa lokaci domin fahimtar matsayinka a gunta.

 
1: Tambayeta yadda take ganin wannan soyayar taku daga lokacin da kuka fara zuwa yanzu.
Amsar wannan tambayar zai fahimtar da kai irin yadda take tunanin zama da kai a matsayin mijinta ko kuma bata tunanin zaku kai wannan matsayin.

2: Tambayeta lokacin da take ganin ya kamata ka turo gidansu domin tambayar aurenta?
Akwai matan da soyayya kawai suke yi da kai amma basu da burin aurenka.Da zaran kayi musu zancen fitowa sai suyi ta baka uzuri da lokaci. 
Amsar wannan tambayar zai fiddaka daga duhu.

3: Farkon furta miki kalmar ina sonki mai yazo miki a zuciya?
Anan zaka fahimci yadda take kallonka, ko take ɗaukanka kamin ku soma soyayya.
Idan ma akwai abubuwa marasa daɗi da aka faɗamata game da kai duk zata sanar da kai.

4: Ko kin fhimci abunda yasa nake sonki da aure?
Kila kai tsaye ta iya baka amsar tambayar, ko kuma ta maida maka tambayar kai ka amsa mata. Kada kace mata komai har sai ka samu koda kalma guda ne daga wajenta.

5: Me yasa kika zabe ni cikin mazan da suke sonki da aure?
Nan ma amsar da zaka samu a wsnnan tambayar zai fahimtar da kai matsayinka a wajenta. Da sanin dalilinta na amince maka da yarda da kai ka zama mijinta.


6: Cikin halayena wannene kike so na daina, wannene kike so na gyara wannene kike so na ci gaba da shi?
Amsa ce da zata taimakeka wajen kara mamaye zuciyarta.

7:Kina burin auren mu mutu ka raba ko kina ganin akwai abunda zai iya rabamu ba mutuwa ba?

8: Idan bana tare dake meke saki kewana?

9: Kullum da akwa abunda kike son fadamini amma kuma dana zo gani gaki sai ki kasa fadamini menene wannan abun?
Wannan tambayace na bugun ciki. Idan har akwai wani abun a ranta zata saki jiki wajen sanar da kai a wannan lokacin.

10: Da fatan zaki iya zama dani a dukkannin yanayin rayuwa danake ciki?
Mace koda ba da gaske take sonka ba amsar da zata baka awannan tambayar shine e, za kayi amfani da wannan amsar ne domin kafa mata hujja nan gaba.
 
Sai dai ba duk mata bane suke da basiran amsa maka tambaya daidai da yadda zai gamsar kai ba, don haka kada rashin baka amsa daidai ya zama ka kullaceka.

Post a Comment

0 Comments